Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, April 30, 2012

KUKAN KURCIYA

Dandalin Muazu Hadejia KUKAN KURCIYA..... Da kun ban gari da nayi tsokaci akan wannan hare haren boma bomai da ake kaiwa Arewacin Nigeria. Wata rana ina dan primary, malamin social studies yake bamu tarihin Hitler Adolph na Jamus sai naji yana cewa hitler in zaici gari da yaki da farko yana kai hari ga jami'an tsaro sannan sai ya kai hari cibiyar kasuwanci da gun ajiyar kudi. Bayan nan sai ya kai hari ga matasa 'yan makaranta! In yayi haka to ya karya tattalin Arzikin ku sai kuma yayi muku duk abinda yaga dama. Abin tambaya anan shine... Anya tarihi bai maimaita kansa ba? Musamman a kasata Nigeria? Yayinda shugaba yakeso ya tabbata a mulki zai iya amfani da salon Hitler yaci gaba da mulkinsa a tsunake. Yasan ba ta mulki kuke ba ku dai ku samu zaman Lafiya. Jama'a yakin ruwa fa ya tadda sakaina! Ya kamata muyi karatun ta nutsu game da Hare haren nan da ake kai mana da sunan wata kungiyar da babu ita. Ka dauka cewa duk abinda ya samu dan Borno ya sameka kai dan sokoto. http://Isabohadejia.blogspot.com/ Muyi kokari mu gyara kasarmu, muyi ta Addu'ah Allah ya kauda mana Miyagun Shugabanni. Kamar yanda Allah ya kawar da Hitler Adolph na Jamus. http:// jindolada.xtgem.com/