Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, June 7, 2012

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA KASHI NA (2)


HADEJIA A YAU! A kashi na farko Na baku Labarin yadda Turawan mulkin mallaka suka yiwa Hadejia Leken Asiri, wadda hakan ta basu dama suka kama garin.

Yanzu zamu dora! Koda yake Sarkin Hadejia Muhammadu ya samu labarin Turawa sun ci Kano da Katagum duk sun koma karkashin mulkinsu yace da yabi Kafiri Gara yayi shahada,Turawa basu fasa ba shima bai fasa ba.

Ranar Talata 1906 Turawa suka shigo Hadejia Gadan gadan akayi ta gwabza fada, dukda dawakan Hadejia basu taba jin kukan Igwa ba da sunji wannan kukan sai su turje haka nan akayi ta fama da su. jama'ar Hadejia manya da yara kowa yayi shirin yaki haka nan akayi yaki har Zuwa Azahar,  kuma Turawa suna kara shigowa Hadejia, saboda makaman su ba irin namu bane. An kashe manyan fadawan Hadejia da hakimai:

kamar yadda na fada a baya Sarkin Hadejia Muhammadu saida aka ce masa Kada Hadejia ta kare saboda shi Tukuna ya rusuna har Turawa suka cim masa. Allahu akbar!

koda Hadejiawa suka samu labari an kashe sarki sai kowa ya Rusuna,  Turawa suka shigo Hadejia suka Fara shirin tafiyar da mulki irin nasu. Hadejiawa sukayi Jana'izar wadanda suka mutu, wadanda kuma sukaji rauni aka kaisu Gidajensu. Turawa suka Nada Sarkin Hadejia Haru mai karamba 1906. 

To akwai sarkin yaki cilin Yana daga cikin wadanda suka samu raunuka a yakin kuma shi Captai phillips ya sanshi dama can. to kullum sai yaje Gidan sarkin yaki Yana Masa Izgilanci yana ce masa ina yakin? Ashe Sarkin yaki yana jin ciwon hakan. Wata rana sai yacewa matarsa Idan zata Kawo masa Abinci tasa wuka a cikin Tuwon.

haka kuwa tayi. saida captain phillips yazo yana masa Izgili Sai yasa hannu kamar mai cin tuwo sai ya dauko wuka ya Burmawa captain phillips a tumbinsa ya kasheshi. Kabarinsa yana can a Gabas Da Bariki Hanyar Tandanu. Shi ake cewa Kabarin mai tumbi. Wadanda suka rasa rayukansu a yakin suna da dama Amma ga kadan daga Sunayensu. Muhammadu Sarkin Hadejia, Madacima shi suka fara kashewa, Galadima, Ma'aji salihu, Furya, Barwa da Tarno, Bori na Salihu, Kaura Amadu, Mabudi zakar, Jarma warkaci, Sabo jikan Tete, Dandalma, Abdulwahabu sarkin Baka, Sarkin Arewa, Alkali, Farau farau, Sarkin Dawaki Dan gazau, Da dai Sauransu! Allah yaji kansu da Rahma.

ZUWAN TURAWA KASAR HADEJIA 1906 (1)


HADEJIA A YAU! A shekarar 1906 Turawan mulkin mallaka suka ci Hadejia da yaki, Inda yayi sanadiyar mutuwar mutanen Hadejia da dama da kuma wasu daga cikin Turawan. kafin wannan Turawa sun shigo Hadejia ne bayan sun ci Katagum da yaki, koda yake ba yaki sukayi da Katagum ba, sun Meka musu wuya ne ba tare da jayayya ba.

kuma Turawan sun shigo Hadejia ne ta Iyakar kasar Hadejia da Katagum, Inda sukayi sansani a Mai Goriba kusa da Masama. To basu shigo Hadejia ba sai da suka turo Dan leken Asiri wadda ya shigo Hadejia a Matsayin Balarabe mai saida kayan Sarauta Irinsu Alkybba da sauransu. kuma an saukeshi a Gidan Zangoma Wato sarkin Baki.

kuma a haka yayi ta Kewaya Hadejia har ya gane duk sirrin Garin Haka kuma yana kaiwa Sarki kaya yana saye har yasan Sirrin fadar Hadejia.

Wannan dan leken Asirin da yayi shigar Balarabe shine Captain H. C. B. Phillips, Wadda ake ce masa (Mai Tumbi). Kuma kafin suzo Hadejia an basu labarin Garin da kuma Mayakan garin, dan haka shi Captain phillips ya dinga bin Gidajen Jarumai yana Musu alheri a Matsayinsa na dan kasuwa, hakan tasa ya shiga jikinsu sosai kuma suka Amince dashi.