Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, June 18, 2012

TASHIN BOM A DAMATURU DAGA BBC HAUSA

Rahotanni daga Damaturu babban
birnin jihar Yobe dake Arewacin
Najeriya, sun ce mazauna unguwanni
da dama ne suka tsere daga gidajen
su, yayin da wasu karin suka
kauracewa unguwannin su domin
samun mafaka.
Wannan dai ya biyo bayan tashin
bama bamai da karar bindigogin da
aka rika ji ne ba kakkautawa a
yammacin yau.
Rundunar Hadin Gwiwar Samar da
tsaro a jihar Yoben ta tabbatar da
abkuwar lamarin, sai dai ba ta
bayyana adadin asarar rayuka da
jikkata da aka samu ba a sakamakon
wannan hari.
Harin na Yoben dai na zuwa ne
kwana daya bayan wasu hare haran
kunar bakin wake da aka kai kansu
coci-coci uku a garin Kaduna da
kuma Zaria.
Hare haran da kungiyar Ahlisunna
lidda'awati wal jihad da ake kira
Boko Haram suka yi ikirarin kaiwa.

HADEJIA A YAU! Sarkin Hadejia Sambo shine ya karbo Tutar Musulunci a gun Usman Dan fodiyo! Yayi mulkin Hadejia tun daga 1808 zuwa 1848. Allah ya masa Rasuwa a Mai-Rakumi. Kuma anan kabarinsa yake! A cikin 'ya'yansa akwai wadanda sukayi Sarautar Hadejia a lokacin yana Raye. Kamar Garko Gambo 1845t-1847, Abdulkadir Dan Sambo 1847-1848. Sannan Sambo yaci Gaba da Mulkin Hadejia kuma ya Rasu a wannan shekarar. Sai kuma Dansa Buhari Sai Ahmadu sannan Buhari Sai jikansa Umaru Dan Buhari. Sai kuma Dansa Haru Bubba. Allah ya Gafarta musu.

KABARIN SARKIN HADEJIA SAMBO


HADEJIA A YAU! Sarkin Hadejia Sambo shine ya karbo Tutar Musulunci a gun Usman Dan fodiyo! Yayi mulkin Hadejia tun daga 1808 zuwa 1848. Allah ya masa Rasuwa a Mai-Rakumi. Kuma anan kabarinsa yake! A cikin 'ya'yansa akwai wadanda sukayi Sarautar Hadejia a lokacin yana Raye. Kamar Garko Gambo 1845t-1847, Abdulkadir Dan Sambo 1847-1848. Sannan Sambo yaci Gaba da Mulkin Hadejia kuma ya Rasu a wannan shekarar. Sai kuma Dansa Buhari Sai Ahmadu sannan Buhari Sai jikansa Umaru Dan Buhari. Sai kuma Dansa Haru Bubba. Allah ya Gafarta musu.

MAI GORIBA


HADEJIA A YAU! Wannan Hoton Mai Goriba ne! Kusa da Maskangayu Inda Turawa suka fara kafa sansaninsu kafin su Shigo Hadejia. Bayan sunci Hadejia da yaki kuma sai suka gina Bariki Ta zama nan ne Gidajensu da Ofis dinsu Har zuwa lokacinda Nigeria ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.

KOFAR MANDARA


HADEJIA A YAU! Wannan kofar Talata ce ko kofar Mandara! Tana daya daga cikin kofofin Garin Hadejia. Ta wannan kofar ce Turawa suka shigo Hadejia a 1906. Kuma da can babu ita Turawa ne Suka fasa Ganuwar Hadejia Suka shigo Shine Dalilin da ake ce mata Kofar Talata saboda Ranar Talata Turawa suka fasa ta suka shigo Hadejia ta cikinta. Hadejia A yau.

KOWA YA GYARA YA SANI


HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa da fatan
Alkairi Ga 'yan wannan Masarauta, Muna
kara godiya ga Allahu subhanahu-wata'ala
da ya bamu ikon Rubuta wannan wasika.
Domin da Ikonsa ne Komai ya kasance da
kuma abinda zai kasance! Bayan haka Ina
kira ga shugabannin Hadejia da su taimaka
su Inganta mana Muhimman guraren
Tarihinmu na kasar Hadejia. Sakamakon
Lalacewa da suke kokarin yi. Kamar Tsohon
Gidan yari, Gulbin Atafi da Ramin zaki, bariki
wato Gidan Rasdan da na D.O., kabarin
Captain H.H. Phillips wato Mai Tumbi, Kofar
Kudu (chediyar kyalesu) da kuma kofar
Gabas. Wani mutum yazo daga BIDDA ta
jihar Niger yace min Yana so na kaishi
Kabarin Captain phillips, sai nayi shiru Ina
tunanin wanene captain phillips? Sai na tuna
lokacin muna yara In munje kanya muna
zuwa kabarin Mai tumbi. Kuma a jikin
kabarin an rubuta captain H.H.phillips! Sai
nace masa Muje ko da mukaje sai na fara
Gabatar masa da Bariki cewa a nan Turawa
suka fara zama. Sai yace dani A'a ai sun
Zauna a can Gaba kafin suzo nan. Nace Eh
hakane. Koda mukaje Kabarin Mai tumbi sai
muka ga Ginin duk ya rushe kabarin yana
nema ya bata. Sannan sai yayi kira ga
Hukumomi su rinka kawata Guraren Tarihi
Irin wadannan. To muma muna kira ga
wadanda abin ya shafa da su Gyara guraren
tarihi ba sai kabarin Mai tumbi kawai ba.
Sannan yace In kaishi Fantai Inda Gidajen
Sarakunan Habe suke. Ko da yake munje
Amma bamu samu Dagacin Mandara a gida
ba amma mun Dauki Hotunan Gidajen nasu
da kuma Tsangayar Gwani Gambo a cikin
'Yankoli. Sannan Muka Zarce zuwa Mai-
Rakumi mukayi Ziyara ga kabarin Sarkin
Hadejia Sambo. Bayan mun dawo Mukayi
sallama da Bako ya wuce Gogaram Ta Bade
Yace daga nan Zaije har Ngazargamu. Nace
Allah ya kiyaye hanya. Sannan sai na fara
tunani Ashe tarihi yana da muhimmanci? Sai
na tuna Ai malamin History yace:- History is
the systematic Account of past and present
Event. Zan baku Karashen Labarin anan
Gaba. Hadejia A yau.