Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, July 8, 2012

WAKAR SAUDATU ADO BAYERO1, Daren jiya ba na yau bane gun kwanan
yaro daban da bubba.2, Bismillah zana shirya waka sarki Allah
kaban basira inyi wakar saude 'yar nikatau.3, Ina dada godiya ga Allah sarkinda ya halicci saude.4, Ga saude sarauniyar kano mai saukin kayi da son mutane.5,Ga mai fara'a da son mutane Bata gaji tsiya da tsangwama ba.


6, A wajen kyauta fa ba kamar saude 'yar
sarkin kano na korau.7,Ga mai haske kamar Azurfa Dadin suna kamar Tagullah.


8,Taurari ko suna da haske basu kai hasken farin wata ba.6, Inda mata suna sarauta a kano mukan
muna da saude.7, A zaria sunyi Quen Amina muma a kano muna da saude.8, A gabas na dangana da Borno ba
kyakkyawa kamarki saude.9, A yamma najeni har Ilorin ni banga ba
wadda tayi saude.10, ta nan kudu har zuwa Adamawa banga ba wadda tayi saude.11, A arewa saida na wuce Nijar banga ba
wadda tayi saude.12, Kai duk matan dake cikin facebook babu wadda tayi saude.14, Hotonki ana comment akanshi na kirga Comment dubu a yanzu.15, Ga allurar cikin duhu sai mai zurfin
hankali ka tsinta.16, Ga saude bakin zare a matoya sai mai
hankali ka tsinta.17, Ni burina a duniya inga kina mulkin
kano sa'ade.18, Allah ba yanda bai iya ba a zazzau shi ya bai Amina.19, Ansa giwa cikin zubo taci guda bakin
rabonta kelau.
20, Allah in yai nufi ga iko nai babu abinda
zai hana shi.