Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, September 27, 2012

MUTUWAR SARKIN HADEJIA BUHARI...

HADEJIA A YAU! Bayan Sarkin Hadejia Buhari ya Gama yake yake kamar yakin Takoko, gamon kafur da sauransu! Sai ya yanke shawarar ya fadada Kasar Hadejia daga Gabas. Kuma a lokacin babu wani Dansa da ya taso wanda zai bashi wata sarauta bubba. Dan haka ya Nada kaninsa Sarkiyo a matsayin Chiroman Hadejia a shekarar 1863. Da nufin ya zama Magajinsa, saboda Dansa Umaru shekarunsa Goma sha Takwas (18). Buhari yayi Tunanin ya Masa sarauta mai Girma a Kasar Hadejia, dan haka yayi kokarin ya masa sarautar Sarkin Auyo, bayanda ya Kashe Nalara sarkin Auyo ba'a nada kowa ba! Dan haka yaso ya nada Umaru a matsayin Sarkin Auyo. Wato ya kasance ya gajeshi bayan ya Mutu.

Da wannan kudiri da yake ransa, Buhari yayi kokarin ya cinye Gogaram (Bedde) da Yaki don ya Nada kaninsa Chiroma Sarkiyo a matsayin Sarkin garin. Kuma dukda yayi haka zuciyarsa daya, wasu daga cikin 'yan-uwansa sai suka yi kokarin su baza masa abinda ya tsara! Dan haka wani daga ciki 'yan-uwan Buhari sai ya fara yada jita-jita a tsakanin fadawan Buhari cewa yana so ne ya kaisu a kashe su don ya cimma wata manufarsa, su kuma fadawa sai suka ga Dangantakarsa da Buhari bazai fadi karya ba sai suka yarda da maganarsa.

Dan haka fadawa sai suka fara shawara a junansu ba tare da Sarki Buhari ko wani ya sani ba, don su yiwa Buhari tawaye a gun yakin, kuma duk suka amince da hakan. Bayan kwanaki sai Buhari ya sanar da fadawa cewa zasuje suci Gogaram da yaki, amma bai san an warware masa shirinsa ba. Aka saka rana Buhari ya jagoranci mayakan Hadejia don su ci Gogaram da yaki,

sarkin Hadejia Buhari ya shiga Gogaram ta kofar Garin yamma amma mayakan Buhari kamar su Sarkin Arewa Tatagana da Sarkin yaki Jaji da sauran fadawa sai suka tsaya suka ki su bi Buhari, ko da ganin Haka sai Buhari ya shiga garin suka fara dauki ba dadi da Mayakan Sarkin Gogaram DAN BABUJE. Har suka sokeshi da Mashi, kuma sai suka fice daga Garin suka koma Bedde ta yanzu. Koda mayakan Hadejia suka ga an raunata Buhari sai suka bisu da yaki, bayan sun dawo sai suka taho da Buhari zuwa Hadejia, inda suka yi Gadon Kara suka Dora shi. Akan hanyarsu ta dawowa Hadejia Buhari ya musu jawabi kuma suka fahimci cewa Munafurci ne akayi tsakaninsu da Buhari. Kuma yace musu lalle In ya mutu su kaishi Hadejia su binne shi, kuma Allah ya dauki ransa a Madaci kusa da Hadejia. Bayan fadawa sun fahimci 'yan-uwan Buhari ne suka munafurceshi, sai suka yanke shawarar cewa dukda Kankantar Dansa Umaru shi zasu Nada A matsayin Sarkin Hadejia. Kuma hakan akayi karkashin jagorancin Tatagana da Jaji. In kazo kayi Gaisuwar Mutuwar Buhari sai ka Juya kayi Mubaya'a a gun Sabon Sarki wato Umaru Dan Buhari. Hadejia A yau.