"" /> HADEJIA A YAU!: 11/01/2013 - 12/01/2013

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, November 24, 2013

TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA. KASHI NA BIYU (2).

Hadejia A yau!



Littafin Muhd. Aji Hadejia.

A kashi na farko kunji cewa Alh. Haruna Uji ya ci gaba da kidan Gurmi gadan gadan.

A lokacin Gwamnan Kano Abdu Bako, sai yaji labarin Haruna Uji, sai yasa aka nemoshi domin yayi masa waka akan wayar da kan Al'umma akan Noma. Saboda haka Gwamna Abdu Bako sai ya hadawa Haruna Uji kayan wasa, kamar Amsa Kuwwa (Loud speaker) da Abin Magana wato (Microphone) da Injin wuta, wato Generator.
Wannan shine lokaci na farko da Haruna Uji ya fara waka da kayan wasa na zamani, kuma ya kama yin waka gadan gadan a matsayin sana'a.

Wakar da yayi a lokacin Itace wakar Noma. Anyi wakar ne da nufin wayar da kan Talakawa su koma Aikin gona.

3.0. WAKOKIN HARUNA UJI NA FARKO.

Alh. Haruna Uji yayi wakoki masu tarin yawa, kuma a cikin Jerin wakokinsa ga wasu daga cikin wakokin da ya fara yi.

*Wakar Naira da kwabo sabon kudi.

*Wakar Gudaliya.

*Wakar Shamuwa.

*Wakar Noma.

*Wakar Bakar Rama.
Wadannan sune kusan Shahararrun wakokin da ya fara yi.

3.1. Ajin Haruna Uji a tsakanin Mawakan baka.

A cikin wani Littafi da Ibrahim Yaro Yahya da Abba Rufa'i suka tsara, Mamuda Aminu ya kawo rabe-raben Mawakan baka zuwa rukunai kamar haka:
*Mawakan Sarakuna
*Mawakan 'yan mata
*Mawakan Jama'a
*Mawakan Mafarauta. Da sauransu.

Ya kawo misalin Mawakan Jama'a shine wanda zai yiwa Sarakuna da 'yan kasuwa da 'yan mata da Masu kudi da talakawa waka. Misali Mamman shata da Haruna Uji da sauransu.

Hakan ta nuna cewa Haruna Uji ya kasance a cikin Mawakan Jama'a, domin ya tabo duk abinda aka zayyana a sama. Wato yakan yiwa kowa waka.

3.1.1 Dangantakar Haruna Uji da Mawakan Baka.

Alh. Haruna Uji yana da kyakkyawar dangantaka da sauran 'yan uwansa mawakan baka, yana girmamasu shima suna girmama shi, sannan ya hori wasu suma sun zama shahararrun mawaka a kasar Hausa. Yayiwa wasu waka kuma shima wasu sunyi masa. A cikin mawakan da suka masa waka har da Alh. Mamman shata, kuma shima Haruna Uji yayi wa Alh. Garba sufa wakar Ta'aziyya bayan ya mutu.

3.1.2 Jerin wasu daga wakokin Haruna Uji.

Bayan rukunin wakokinsa na farko, ga wasu daga cikin wakokin da yayi.

*Wakar Dankabo
*Wakar Alh. Sani Likori
*Wakar Direban Chiyaman
*Wakar (Air vice marshal) Ibrahim Alpha
*Wakar (kwamishinan 'yan sanda) Daudu Gwalalo
*Wakar Haruna karamba
*Wakar Adamu Hassan Abunabo
*Wakar Ahmed Aruwa
*Wakar Asabe Madara
*Wakar Amadu koloji makwallah
*Wakar Bako Inusa kano
*Wakar Balaraba
*Wakar Jimmai Aljummah
*Wakar Birgediya Abdullahi shalin.
*Wakar Dankamasho
*Wakar Fulanin Jebbi fulato
*Wakar Idiyo Mai kayan Babur
*Wakar Kainuwa.

SAURAN WAKOKIN KU DUBA LITTAFIN.

Ka duba kashi na uku (3)

Thursday, November 21, 2013

TARIHIN HARUNA UJI. DA WAKOKINSA. KASHI NA DAYA (1).

Alh. Haruna Uji Hadejia.

Hadejia A yau! An haifi Alh. Haruna Uji A Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.

Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta a Gandun sarki, daga nan suka tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.

Bayan nan suka bar Birniwa suka dawo Hadejia suka ci gaba da karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara musamman wadanda suka zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu. Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu karatu mai dama.
Hadejia A yau!

1.1, ASALIN INKIYAR HARUNA UJI..
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA, Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin Iya Kura, Mijin Iya Kura' A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka daina ake cewa Uji.

1.11, SIFFAR HARUNA UJI.
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga magana (Idanu) haka kuma, ma'abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka 'yar shara, musamman lokacin zafi.

Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara'a da kyauta, domin abin hannunsa bai rufe masa ido ba. Yana da raha sannan kuma bashi da wata nakasa a fili.

2.0, SANA'OIN HARUNA UJI..

2.1, Farauta da Noma.
Bayan Haruna Uji ya bar makarantar Allo, ya fara zuwa Daji da nufin farauta. Wadda itace sana'arsa ta farko, wanda ya fara, kuma ta sanyashi jarunta inda ya zama bashi da tsoro. Kuma a nan ne ya samu tambaya wato lakani na tsare kai.

Bayan farauta Haruna Uji Manomi ne, ya fara aikin gona ne da taya mahaifinsa, domin neman tabariki, wannan tasa yasan harkar noma wanda har yake noma gonar kansa.

2.2, Sana'ar Tukin Mota (Direba)
Alh. Haruna Uji yayi Sana'ar Tukin mota, wanda ya fara da Yaron mota a gun Mai gidansa wanda ake kira da suna Jibrin Dan Amingo. Jibrin Dan Amingo dan Asalin Danbatta ne ta Jihar Kano. Haruna Uji ya shafe shekaru da dama yana sana'ar yaron mota. Tukin mota ne sana'arsa ta farko da ta fara fitar dashi wani gari da nufin zama. Suna aiki ne tsakanin Kano da Hadejia.

Kuma a wannan lokacin suna zaune ne a garin kano a Tudun wada. Amma duk abinda ya taso a gida dashi akeyi, musamman aikin gona da bukukuwa da sauransu.

2.3, Sana'ar Waka.
Haruna Uji bai gaji waka ba, domin Mahaifinsa Malami ne, kuma ko a wakarsa ta Gurmi ba Haramun ba yana cewa:-
"Ni Haruna dan Mallam nake, Waka ta ba ta gado bace"

Saboda haka tun farko Haruna Uji ya riki waka ne a matsayin nishadi, domin ba wanda ya koya masa waka a matsayin Sana'a.

Haruna Uji ya fara ganin Gurmi ne a gun wani ma'aikacin titi wanda sukayi aiki a hanyar Mallam madori zuwa Gumel, wanda ake kira Dan-mato, a gun Dan-mato Uji ya fara ganin Gurmi da kidansa, shi Dan-mato yana kada Gurmi ne a yayinda suka samu hutun aiki. Yana kadawa yana waka, lokacin Uji yana Matashi, duk lokacinda sukaje kallon aiki sai su tsaya suna ganin kidan Gurmin Dan-mato, wannan tasa kidan Gurmi ya shiga ran Haruna Uji, idan ya dawo gida sai yakan nemi gwangwani da tsirkiya ya hada Gurmi yana kadawa. Har Dan-mato suka hada aikin hanya bai koyawa Uji Gurmi ba, sai dai Uji yana zuwa yana ganin yanda yake kadawa. Wannan tasa Uji ya dinga kwaikoyon Dan-mato tun bai iya ba har ya koya.

Wannan yasa idan yana gurmi yara sukan tsaya suna ji da kallonsa, Wannan shine Asalin koyon Gurmin Haruna Uji. Daga nan sai ya fara tunanin ya samu sanda, da lilo da butar Duma da fatar Damo da Zobe domin ya hada bubban Gurmi.

Farkon lokacinda ya fara Gurmi idan an bashi abu baya karba, don yanayi ne saboda Nishadi. Kuma sau da yawa idan ya fito hira ko ana wani biki na samari da 'yan mata, yakan kada Gurminsa yana waka, samari da 'yan mata suna kallo.

A wancan lokacin yana Gurmi yana aikin Mota, wannan yasa ya fara Gurmi a garuruwa daban daban na Arewacin Nigeria.

Daga nan Uji ya bar tukin mota ya koma kidan Gurmi Kuma ya nemi mataimaka don sunayi su biyu.

Karashe a kashi na 2.
Littafin Muhd. Aji Hadejia

Tuesday, November 19, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI. (KASHI NA 2)



BY COMRADE GARBA MUHD HADEJIA


A lokacin da makiyaya su ka fara yin ta'adi a gonakin mazauna yankin ba a gayyaci kowace hukuma a cikin al'amuran ba, ganin cewar matsalar karama ce a wancan lokacin. Kuma su manoman basu san hakikanin irin fulanin da suke yin wannan ta'adin ba. Har su kan yi tunananin cewar wai shin fullo-Hadejia ne ko Zamfarawa?


Faruwar hakan ta ja hankalin shugabannin mazauna yankin (manoma) wadanda suka hada da Dagatai,Bulamai, Lawanai (Bade), Mai (Gizimawa) don tattauna matsalar da shugabannin Fulani irinsu Lamidai da Hardawa. Irin wannan tattaunawa ta yi ta faruwa har hukuma ta shigo cikin sabgar don rushe dukkan wani yunkuri na barkewar rikici. Saboda abin ya na faruwa duk shekara musamman ma da kaka. Duk da shigowar hukuma cikin lamarin, bai hana daukar fansa daga manoman ba, saboda kai su bango da makiyayan suka yi na cinye musu amfanin Gonakinsu.


A duk shekara a kan asarar rayuwa daga kowane bangare. Duk da kasancewar jami'an tsaro kala-kala; yan sanda, mobile police, wani lokaci har da sojoji don sasanta tsakanin manoma da makiyaya. Suma jami'an tsaron daga bangarensu sun rasa da yawa daga cikin mutanensu. Wasu an harbe su da kibiya, wasu an sassarasu da arda sun mutu wasu an lagarta su, saboda hukuma bata basu damar harbi ba.


A kwai shekarar da har jirgi mai saukar ungulu (Helcopter) aka kai yankin don shiga surkukin dajin da ke wannan yankin. Daga cikin matsalolin da jami'an tsaro su ke samu daga wannan yankin, shine rashin basu umarnin daukar mataki na kare kansu daga dukkanin wanda zai yi yunkurin harbinsu ko sararsu. Haka tasa suke janye jikinsu daga shiga cikin rigimar gadangadan. Daga bangaren gwamnatocin siyaya an samu da yawa da suka taka rawa don ganin an shawo kan matsalar amma idan shekara ta zagayo sai an yi.Haka kowace gwamnati take yi.


A lokuta da dama akan kafa kwamatoci na musamman wanda zaiyi bincike akan matsalar, amma daga karshe sai a kasa cimma komai. Su kan nemi zama da kungiyar manoma da makiyaya da shugabannin kowane bangare don kowa ya jawa mutanensa kunne amma daga karshe sai abin ya bi iska. A wasu lokutan korafe-korafe su kanyi yawa daga bangarorin biyu na zargar junansu da laifin tayarda rigimar. Makiyaya su kan ce laifin manoma ne da suke noma makiyayar dabbobi da burtalai, su kuma manoma su ce laifin makiyaya ne da baza su yi hakurin barinsu su tare amfanin gonarsu ba.

Haka dai ake ta maganganu a kai. Daga lokacin da gwamnati mai mulki a yanzu ta hau. Ta yi kokarin lallai kowane makiyayi ya tsaya a makiyayarsa. Sannan ta tabbatar da kowane burtali da makiyayar dabbobi ba a nomashi ba. Sai dai wani abin mamaki har yanzu abin bai chanja ba, domin wannan rigimar bata mutu ba. Ko shekarar da ta wuce ma an sami rikici a wasu garuruwa irin su Gagiya da Garin Mallam. wadanda su ke kudancin Guri. Ko a wannan lokaci da ka ke karanta wannan rubutun ma, an sami wadansu daga cikin makiyaya suna shiga gonakin manoma suna cinye musu Amfanin gona. Wannan matsalar ta kawo ci baya gagarumi a kudancin Guri. Domin manoma da yawa sun hakura da noman shinkafa, Alkama, Wake da kankana. Abin da ya rage kawai sai gero da dawa, wanda a yanzu a kansu ake yin wannan rigimar domin shi din ma yana neman fin karfinsu.

Babban dalilin da ya sa manoman su ka hakuri da noma wadansu daga cikin amfanin gonar shine. Yawan zubda jinin al'umma da ake yi sakamakon kare dukiyoyinsu. Saboda wasu lokutan har garuruwansu (manoman) ake binsu don a halaka su. Wata shekara akwai garin da aka kona kurmus; tare da abincinsu, da dabbobinsu da dattijai da kananan yara wadanda ba za su iya guduba. Daga karshe, ina kira ga duk wanda ke ziyartar wannan dandali mai albarka, kuma ya kasance mai iko, da ya isar da wannan sakon ga hukumomin da abin ya shafa su duba al'amarin wadannan bayin Allah don kawo masu karshen wannan matsalar.


Sannan 'Yan majalissu na tarayya da na jiha da su kalli wannan abin ta hanyar janyo hankalin gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen warware wannan matsalar. Abin da gwamnati ya kamata ta lura da shi, shine wannan matsala ce ta cikin gida tsakanin manoma da makiyaya. Kuma suma wadannan makiyaya (fulani) 'yan uwanmu ne musulmi, sannan mun zo daga bangare daya, kuma tare muke zaune, kasuwa da ya muke ci da su ga auratayya ta hada mu.

Saboda haka ba sai da bakin bindiga za a sasanta ba, a'a akan tabarma za a zauna tare da kwararru a fannin warware rikici wadanda suka karanta (conflicts Resolution) da malaman addini da sauran masu fada a ji a cikin al'umma don a tabbatar da adalci tsakanin manoma da makiyaya. HADEJIA A YAU.

Sunday, November 17, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI...(1)

Hadejia A yau!
Daga Garba Muhammad Hadejia....
CIWON CIKIN BAREWA A DAJI.

Zamantakewa wata aba ce wadda ta ke kasancewa tsakanin kowane jinsi, na mutane, aljannu, dabbobi da tsuntsaye da sauran halittu. kowane jinsi daga cikin halittu yana da irin kalubalensa na neman cika jakar ciki da sauran bukatu wadanda dole sai an cimma su za a samu dorewar rayuwa, sannan rayuwa ta bada zaman lafiya.

Idan ko ya kasance wani ko wasu daga cikin wannan jinsi zasu fifita bukatunsu fiye da na 'yan uwansu, to za a iya samun barkewar rashin jituwa, wanda shine zai yi sanadin barkewar rashin zaman lafiya a tsakanin wannan jinsin.

Dan Adam, wanda ya kasance mafi hikima a cikin sauran halittu,saboda wadansu ni'imomi da ubangiji ya yi musu. Shi kadai ne ya ke da tunanin ya noma abin da zai ci, don samun dorewar rayuwa, da nisanta daga galabaita da zai yi a yayin da ya nemi abinci ya rasa a muhallinsa. Daga cikin
abin da ya noma har da tunanin tanaji don gaba yayi amfani da shi.

Kasancewarsa mai hikima (Dan Adam) Allah ya bashi ikon sarrafa wasu daga cikin dabbobin gida, kamar su shanu, awakai, tumakai,rakuma da sauransu.

Daga cikinsu (Yan Adam) akwai wadanda suka zabi kasancewa da dabbobi a matsayin dukiya. Wanda hakan ya sa dole su ka kebe kasu daga cikin jama'a don su samu damar kula da dabbobinsu ta hanyar ciyar da su da shayar da su daga ciyayi da ganyayyaki. Hakan yasa wasu daga cikinsu ko noma ba sa samun damar yi, sai dai su sayi abinci daga manoma ko a kasuwa daga kudaden da suka samu a yayin da suka sayar da dabba ko nononta.

Wani lokacin sukan yi bulaguro daga wani yanki zuwa wani yanki don samarwa dabbobinsu abinci, musamman a lokacin rani ko damana su kan tashi daga yankin da bai da ni'ima zuwa yankin da ya ke da ni'ima.

Haka ta sa ake ganinsu a mutanen da ba su da takamaiman gari, kasa ko nashiya.


Kudancin Guri ya kasance mafi ni'ima idan aka hada shi da sauran yankuna na masarautar Hadejia. Domin albarkatu na daji, fadamu, gurin kiwo, kifi, tsuntsaye, da sauran albarkatun noma. Haka shine ya sa makiyaya suke da yawa a kudancin Guri.

Idan aka ce kudancin Guri ana nufin Gundumar Kadira ko muce (Kadira Distric) sun hada da manyan garu-ruwa irinsu Kadira, Abunabo, Musari, Gaduwa da Galdimari, Garin Mallam, Gagiya,Garmaguwa daSauransu.

Wannan yanki ya hada yaruka (kabilu) masu yawa sabanin sauran yankuna na Masarautar Hadejia. A wannan yanki za ka samu Mangawa, Gizimawa, Badawa, Fulani, Larawa, sai kuma Hausawa Auyakawa wadanda ba su da yawa.
Daga shekarar 1980 ne aka fara samun shigowar makiyaya (Fulani) a wannan yankin.

Fulanin da suka fara zuwa sun kasu kashi hudu, akwai:
Aborawa, Zamfarawa, Udawa, Fullo-Hadejia da Wuddurawa.

Wadanda su ka fara zuwa sune Aborawa. A wancan lokacin sukan zo a lokacin da ruwa ya gama cin dajin ciyawa ta fito sannan su yi kiwo. A wannan lokacin ya kasance a kwai wani ruwa da ake kiransa da suna Ruwan Dukuku; shi wannan ruwa idan ya zo ya kan mamaye dajin gaba daya, ya zamanto babu makiyaya. Hakan yake sa dole makiyayan su yi hijira zuwa kasar Yobe (Bade) don yin kiwo kafin ruwan ya janye su dawo.

Haka aka yi ta tafiya har Udawa su ka fara zuwa don yin kiwonsu a wannan daji kamar yadda Aborawa su ke yi. Su ko mazauna yankin su kanyi nomansu iri-iri, tare da sana'a ta kamun kifi.
Daga cikin Aborawa da Udawa aka samu Fulani mazauna wanda ake kira da Fullo-Hadejia. Sun kafa garuruwa irinsu; Safami, Maidashi, Matarar kano, Dolewa,Askandu da sauransu. Su kan zauna tare da dabbobinsu a rigagensu kuma su kan yi noma a guraren. A yayin da ruwan dukuku ya daina cin Dajin.

Daga nan sai zuwan zamfarawa.
Zamfarawa sun shigo kudancin Guri ne sakamakon fitintinu da ke yawan afkuwa a yankunansu na Zamfara.
Sakamakon haka ne ya sa su ka yi Hijira daga can suka zo kudancin Guri. Sun kasance ba mazauna guri kawai ba, sukan yawata zuwa sauran yankuna na Guri har sukan zuwa makwabta irinsu madaci, marma da sauran guraren da ake noman shinkafa don yin kiwo.

Haka zamantakewa ta ci gaba da kasancewa tsakanin wadannan al'ummah har zuwan Wuddurawa wadanda sukazo daga kasar Katagum da sauran yankunan jihar Bauchi. Domin kudancin Guri ya yi iyaka da Bauchi.

Zumunci tsakanin mazauna yankin da makiyaya (Fulani) ya ci gaba da kulluwa, sakamakon cudanya ta cinikayya da sauran al'amura na yau da kullum ya sa har auratayya ta fara kulluwa a tsakaninsu. Wannan ya sa duk auran da za a yi a Rigar fulani sai ka ga daya daga cikin mazauna yankin ya halarta haka suma fulanin.

Ku biyomu a kashi na biyu (2).
Hadejia A yau.

Wednesday, November 13, 2013

KASIDAR MALAMAN MAKARANTA.

Hadejia A yau! 1, Madallah da Mallam Usaini Sulaiman Malamin makaranta.

2, Bismillah mu fara da sunan Allah wanda yayi halittu, shi yayi malamin makaranta.

3, Allah shi ya shirya halitta, yayi ruwa wuta rana da wata yayi malaman Makaranta.

4, Shine yayi Malam Usaini, masu prince ta Eco banki kan hanyar zuwa Makabarta.

5, Sabo na gode sarki Allah, wanda ya bani iko na sa 'yata a Prince farar Makaranta.

6, Nagodewa Mallam Usaini, shine Headmastan Prince makarantar nan dana saka 'yata.

7, Ba shi dai ba har malamansa, koda zasu fishi hazaka sun isa malaman makaranta.

8, Nagodewa duk Malamansu, Yarinya a sati biyar ta haddace duk Jihohin kasata.

9, Ga jinjina ga Malam Usaini, da sauran Malamanda suke a Prince kuma kuna zuciyata.

10, Yarinya ta ban mamaki, tun daga A zuwa Zed idan ta zauna zata kawosu 'yata.

11, Lissafi kamar kalkuleta, kai ko kalkuleta ma nasan da kadan fa zatafi 'yata.

12, Burin duk Uba tarbiyya, to Alhamdulillahi Allah shi yayi malaman Makaranta.

13, Iyaye nai kira a gareku, duk mai Da ya kaishi Prince domin yaga fa'idar Makaranta.

14, Ga koyon Handwritting Idan Munje home work suke baiwa 'yata.

Tuesday, November 12, 2013

ZUWAN AMINU ALA HADEJIA.KADDAMARDA LITTAFIN WAKOKIN HARUNA UJI...

Aminu Ala.
Free Web Proxy

1, Mun gode Aminu Ala, Barka da zuwa Hadejia, gun taron kaddamar da littafin Aji kima.

2, Bismillah zana fara waka da yabon gwanina, gwanin kowa a waka lalle Ala babu dama.

3, Nagodewa Ilahi, Nagode Aminu Ala nagode Aji kima.

4, Ranar Asabat a fantai, A filin kaddamar da tarihin Haruna Uji, da wakoki nai masu dama.

5, Haruna Uji Hadejia, ya bada gudunmawa fa, a wakoki da suke kai sako ai nadama.

6, Ko anyi raha a watse, ko a fadakarda kai zaman rayuwarka ina makoma.

7, Taro kuma yayi kyawu, jama'a duk sunji dadi, suna yin jinjina gun shi wannan wanda yayi littafin Aji kima.

8, Ado Ahmed Gidan dabino, dashi da Aminu Ala, Bashir Ahmed blogger, Marubuta baku dama.

9, Yasir Ramadan gwale bai samu zuwa ba saboda nisa, Amma sakonka na san ya iske Aji kima.

10, In zaka fadi fadi gaskiya, wani shafi ne na Yasir, kaje kaga zunzurutun fasaha babu dama.

11, Godiya gun kungiyoyin, facebook na jihar jigawa, shugabannin Dandalin siyasa mun dau sakonku kuma.

12, Gizagawan zumunci, suma ba'a barsu baya, Dandalin marubuta godiya wakilancinku kuma.

13, Dr. Dahiru godiyarmu, bata manta da shi ba, don shine yayi sharhin littafin Aji kima.

14, Ga sakon godiyarmu ga Dr. Abbas na Ringim, shima ya danyi sharhi, jama'armu Ina makoma.

15, Shugaban karamar hukumar Hadejiya Alhajindo, Umar Danjani p.A. Barka da zuwanka kaima.

Alh. Baffa Bura.... Allah yayi ma Mabudi.......
Hadejia A yau.

Sunday, November 10, 2013

SAKON BANGAJIYA DAGA KWAMITIN KADDAMAR DA LITTAFIN TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA.

Comrade Aji Kima Hadejia!
Free Web Proxy
HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Bayan gaisuwa irinta Addinin Musulunci, muna meka sakon godiya da ban gajiya ga wadanda suka halarci taron kaddamar da Littafin Tarihin Marigayi Haruna Uji da Wakokinsa. Wanda akayi a
Ranar Asabat 9th November 2013, a Dakin Taro na sakandare fantai.

Muna Meka sakon bangajiya da fatan Alkairi zuwa ga Shugaban karamar hukumar Hadejia, Alh. Abba Haruna. Da mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin dalibai Alh Umaru Danjani.

Gaisuwa da fatan Alkairi ga
Shugaban kwalejin Ilimi ta jihar Jigawa Dr. Dahiru Abdulkadir. Da shugaban Makarantar koyon aikin Alkalanci ta Ringim Dr. Abbas A. Abbas.

Gaisuwa da fatan Alkairi ga
Babban mai kaddamarwa;

Pharm.Hashim Ubale Yusufu

Muna meka sakon godiya ga kungiyoyin facebook da kuma kungiyoyin Marubuta da Mawallafa na Jihohin kano da jigawa.

Sakon godiya da bangajiya zuwa ga Alh Aminu Ladan Ala
da Ado Ahmed Gidan Dibino.

Muna Meka sakon Jinjina da bangajiya zuwa ga Alh Baffa Bura FNICPR.

Muna meka sakon Godiya ga Iyalan Marigayi Haruna Uji da jama'ar Unguwar Gandun Sarki.
Gaisuwa da godiya ga Jami'an tsaro da 'yan jarida da ma'aikatan yada Labarai.
Allah ya huci gajiya.

Tuesday, November 5, 2013

TARIHIN MARIGAYI HARUNA UJI DA WAKOKINSA. MUHD. AJI HADEJIA...

Comrade Aji Kima Hadejia!
Free Web Proxy
HADEJIA A YAU!
Muna gayyatar yan uwa da Abokan Arziki zuwa wajen kaddamar da littafin da na
rubuta wanda na kira
"Tarihin Alh Haruna Uji da Wakokinsa"

Za'ayi Taron kamar haka:

Rana=Asabat 9th November 2013 Guri=Dakin Taro na sakandire fantai Hadejia Jigawa state Lokaci=10am

Baban Bako na musamman;

mai girma gwamnan jihar jigawa Alhaji Dr sule Lamido con.

Uban Taro;

Mai Martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje Con.

Shugabannin Taro;

1.Alhaji Suleman Baffa
2.Alh Muhammadu Daguro

Masu Masaukin baki:

1.Mai girma shugaban karamar hukumar Hadejia Alh Abba Haruna
2.mai girma dan majalissar jiha mai wakiltar Hadejia Alh Aminu Abus
3.Mai girma mai bawa gwamna shawara akan harkokin dalibai Alh Umaru Danjani.

Bako mai jawabi;

Mai girma kwamishinan Ilimi na jihar Jigawa Farfesa Haruna Wakili.

Mai bitar Littafi;

Shugaban kwalejin Ilimi ta jihar Jigawa Dr. Dahiru Abdulkadir.

Babban mai kaddamarwa;

Pharm.Hashim Ubale Yusufu

Mataimakan masu kaddamarwa

1.Mai Girma shugaban jam'iyar PDP ta jihar Jigawa Alh Salisu Mamuda.
2.Mai Girma kakakin majalissar dokokin jihar jigawa Alh Adamu Ahmed
sarawa.
3.Mai Girma mataimakin kakakin majalissar dokoki Abdu Alh Dauda Karkarna.
4.Masu Girma Ciyamomin Hadejia da Auyo da k/Hausa da Kaugama da m/madori da Guri da birniwa daKirikasamma.
5.Masu Girma yan majalissar Hadejia, Auyo. K/hausa, Kaugama, M/madori da Guri da Birniwa da Kirikasamma
6.Mai Girma kwamishinan matasa da raya al'adun gargajiya Alh Babandi Muhammad.
7.Alhaji Salisu Sambajo MFR

Masu Rera Waka;

1.Alh Aminu Ladan Ala
2.Fati Niger
3.Saddiq zazzabi
4.Surajo mai Asharalle
5.Dan Kwamarado

Masu Gabatar da Taro

1.Alh Baffa Bura FNICPR
2.Alh Umar Kiyari Jitau Madamuwa
3.Salmanu Adamu Rishi.

Allah ya bada ikon Zuwa.