content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!: ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI...(1)

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, November 17, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI...(1)

Hadejia A yau!
Daga Garba Muhammad Hadejia....
CIWON CIKIN BAREWA A DAJI.

Zamantakewa wata aba ce wadda ta ke kasancewa tsakanin kowane jinsi, na mutane, aljannu, dabbobi da tsuntsaye da sauran halittu. kowane jinsi daga cikin halittu yana da irin kalubalensa na neman cika jakar ciki da sauran bukatu wadanda dole sai an cimma su za a samu dorewar rayuwa, sannan rayuwa ta bada zaman lafiya.

Idan ko ya kasance wani ko wasu daga cikin wannan jinsi zasu fifita bukatunsu fiye da na 'yan uwansu, to za a iya samun barkewar rashin jituwa, wanda shine zai yi sanadin barkewar rashin zaman lafiya a tsakanin wannan jinsin.

Dan Adam, wanda ya kasance mafi hikima a cikin sauran halittu,saboda wadansu ni'imomi da ubangiji ya yi musu. Shi kadai ne ya ke da tunanin ya noma abin da zai ci, don samun dorewar rayuwa, da nisanta daga galabaita da zai yi a yayin da ya nemi abinci ya rasa a muhallinsa. Daga cikin
abin da ya noma har da tunanin tanaji don gaba yayi amfani da shi.

Kasancewarsa mai hikima (Dan Adam) Allah ya bashi ikon sarrafa wasu daga cikin dabbobin gida, kamar su shanu, awakai, tumakai,rakuma da sauransu.

Daga cikinsu (Yan Adam) akwai wadanda suka zabi kasancewa da dabbobi a matsayin dukiya. Wanda hakan ya sa dole su ka kebe kasu daga cikin jama'a don su samu damar kula da dabbobinsu ta hanyar ciyar da su da shayar da su daga ciyayi da ganyayyaki. Hakan yasa wasu daga cikinsu ko noma ba sa samun damar yi, sai dai su sayi abinci daga manoma ko a kasuwa daga kudaden da suka samu a yayin da suka sayar da dabba ko nononta.

Wani lokacin sukan yi bulaguro daga wani yanki zuwa wani yanki don samarwa dabbobinsu abinci, musamman a lokacin rani ko damana su kan tashi daga yankin da bai da ni'ima zuwa yankin da ya ke da ni'ima.

Haka ta sa ake ganinsu a mutanen da ba su da takamaiman gari, kasa ko nashiya.


Kudancin Guri ya kasance mafi ni'ima idan aka hada shi da sauran yankuna na masarautar Hadejia. Domin albarkatu na daji, fadamu, gurin kiwo, kifi, tsuntsaye, da sauran albarkatun noma. Haka shine ya sa makiyaya suke da yawa a kudancin Guri.

Idan aka ce kudancin Guri ana nufin Gundumar Kadira ko muce (Kadira Distric) sun hada da manyan garu-ruwa irinsu Kadira, Abunabo, Musari, Gaduwa da Galdimari, Garin Mallam, Gagiya,Garmaguwa daSauransu.

Wannan yanki ya hada yaruka (kabilu) masu yawa sabanin sauran yankuna na Masarautar Hadejia. A wannan yanki za ka samu Mangawa, Gizimawa, Badawa, Fulani, Larawa, sai kuma Hausawa Auyakawa wadanda ba su da yawa.
Daga shekarar 1980 ne aka fara samun shigowar makiyaya (Fulani) a wannan yankin.

Fulanin da suka fara zuwa sun kasu kashi hudu, akwai:
Aborawa, Zamfarawa, Udawa, Fullo-Hadejia da Wuddurawa.

Wadanda su ka fara zuwa sune Aborawa. A wancan lokacin sukan zo a lokacin da ruwa ya gama cin dajin ciyawa ta fito sannan su yi kiwo. A wannan lokacin ya kasance a kwai wani ruwa da ake kiransa da suna Ruwan Dukuku; shi wannan ruwa idan ya zo ya kan mamaye dajin gaba daya, ya zamanto babu makiyaya. Hakan yake sa dole makiyayan su yi hijira zuwa kasar Yobe (Bade) don yin kiwo kafin ruwan ya janye su dawo.

Haka aka yi ta tafiya har Udawa su ka fara zuwa don yin kiwonsu a wannan daji kamar yadda Aborawa su ke yi. Su ko mazauna yankin su kanyi nomansu iri-iri, tare da sana'a ta kamun kifi.
Daga cikin Aborawa da Udawa aka samu Fulani mazauna wanda ake kira da Fullo-Hadejia. Sun kafa garuruwa irinsu; Safami, Maidashi, Matarar kano, Dolewa,Askandu da sauransu. Su kan zauna tare da dabbobinsu a rigagensu kuma su kan yi noma a guraren. A yayin da ruwan dukuku ya daina cin Dajin.

Daga nan sai zuwan zamfarawa.
Zamfarawa sun shigo kudancin Guri ne sakamakon fitintinu da ke yawan afkuwa a yankunansu na Zamfara.
Sakamakon haka ne ya sa su ka yi Hijira daga can suka zo kudancin Guri. Sun kasance ba mazauna guri kawai ba, sukan yawata zuwa sauran yankuna na Guri har sukan zuwa makwabta irinsu madaci, marma da sauran guraren da ake noman shinkafa don yin kiwo.

Haka zamantakewa ta ci gaba da kasancewa tsakanin wadannan al'ummah har zuwan Wuddurawa wadanda sukazo daga kasar Katagum da sauran yankunan jihar Bauchi. Domin kudancin Guri ya yi iyaka da Bauchi.

Zumunci tsakanin mazauna yankin da makiyaya (Fulani) ya ci gaba da kulluwa, sakamakon cudanya ta cinikayya da sauran al'amura na yau da kullum ya sa har auratayya ta fara kulluwa a tsakaninsu. Wannan ya sa duk auran da za a yi a Rigar fulani sai ka ga daya daga cikin mazauna yankin ya halarta haka suma fulanin.

Ku biyomu a kashi na biyu (2).
Hadejia A yau.

6 comments:

  1. Wannan bayani/tarihi yayi matukar ma'ana ina da kira ga haziqin marubucin da cigaba a wannan dandali domin fa'idantuwar sanin silar farkon rikicin da tunanin hanyoyin maganin sa

    ReplyDelete
  2. Hakika naji dadin wannan rubutu kasancewar daya daga cikin ma'abota bibiyar wannan shafi na Hadejia Ayau, Malam Allah ya karo muku basira kai da Wanda yayi wannan rubutu Amb. Garba Alhadejawy

    ReplyDelete
  3. Gaskiya wannan rubutu ya bani ilimi akan suwanene mazauna yankin guri,zanso mai rubutu yaci gaba da rubutun koza musan dalilin da yake sa yawan fitin tinu tsakanin manoma da makiyaya

    ReplyDelete

RUBUTA RA'AYINKA!