Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, March 7, 2013

HUKUNCIN GADO DA MASU CIN GADO. KASHI NA DAYA (1)

HADEJIA A YAU! Assalamu Alaikum! Wannan babi zai yi bayani a kan masu gado a cikin maza, da masu gado a cikin mata. Sannan babin zai yi bayani akan irin bambancin darajojin magada. (1) MASU GADO A CIKIN MAZA Masu gado daga cikin maza, su goma (10) ne! Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su, su goma sha biyar ne, (15) kamar haka:- 1. Da (Na tsatso) 2. Dan da, (Jika har zuwa tattaba kunnansa) 3. Uba (Na ciki) 4. Kaka namiji (Na wajan uba, har zuwa Sama) 5. Dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba daya) 6. Dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa daban) 7. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya, uba daban) 8. Dan dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba daya) 9. Dan dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa Daban) 10. Kanin uba, shakiki (Na uwa daya, uba daya) 11. Kanin uba li'abi (Na uba daya, uwa daban) 12. Dan dan kanin uba, shakiki (Na uwa daya uba daya) 13. Dan dan kanen uba, li'abi (Na uba daya uwa daban) 14. Miji. 15. Ubangijin bawa. Hadejia A yau! MASU GADO A CIKIN MATA Masu gado a cikin mata su bakwai ne (7) Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su, su goma ne, (10) kamar haka:- 1. 'Ya ko Diya (Ta tsatso) 2. 'Yar da, (Na tsatso duk yadda ya yi nisa) 3. Uwa 4. Kaka mace (Ta wajan uba) 5. Kaka mace (Ta wajan uwa) 6. 'Yar'uwa shakikiya (Ta uwa daya, uba daya) 7. 'Yar'uwa, li'abiya (Ta uba daya, uwa daban) 8. 'Yar'uwa, li'ummiya (Ta uwa daya, uba daban) 9. Matar Aure 10. Uwargijiyar bawa ko baiwa. Hadejia A yau! MASU GADO DARAJARSU TANA DA BAMBANCI DA JUNA Masu gado suna da bambanci da junansu. Ma'ana gado ba abu ba ne wanda za a ce a raba shi daidai, a tsakanin magada. Dole ne a raba shi yadda Allah Madaukakin Sarki Ya raba shi cikin hikimarSa. A rabon gado wani ya fi wani rabo. Wani kuma ba ya da rabo in ga wani. Wani kuwa zai tashi daga wani rabo ya koma ga wani rabo, saboda samun wani tare da shi. Wani kuma zai kada wani; wani sauran dukiya yake kwashewa. Saboda haka za mu bi su dalla-dalla, domin mu yi bayaninsu, in sha Allahu. MASU FARALI Za mu fa ra da bayanin abin da ake nufi da masu farali. Masu farali su ne wadanda Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci rabonsu a cikin Alkur'ani Mai girma. wadannan su ne kamar haka: 1. 'Ya (Ta tsatso) 2. 'Yar da (Na tsatso) 3. Uwa 4. Uwar uwa 5. Uwar uba 6. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya) 7. 'Yar'uwa li'ummiya, (Ta uwa daya) 8. Miji. 9. Mata. MASU ASIBCI Za mu fara bayani a kan abin da ake nufi da asibi. Asibi shi ne wanda idan a ka zo wajan rabon gado, zai tsaya har a fitar wa masu farali, farilinsu, sannan abin da ya yi saura ya kwashe, za mu jera su kamar haka: 1. Da (Na tsatso) 2. Dan da (Na tsatso) 3. Dan'uwa shakiki, (Uwa daya uba daya) 4. Dan'uwa li'abi, (Na uba daya) 5. Dan dan dan'uwa shakiki (Uwa daya uba daya) 6. Dan dan dan'uwa li'abi, (Na wajan uba) 7. Kanin uba shakiki (Uwa daya uba daya) 8. Kanin uba li'abi, (Uba daya uwa daban) 9. Dan kanin uba shakiki, (Uwa daya uba daya) 10. Dan kanin uba li'abi, (Uba daya uwa daban) 11. Wanda ya 'yanta bawansa. 12. Wadda ta 'yanta bawanta. MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU KARBI FARALI Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani lokaci kuma su amshi farali, su ne kamar haka: 1. 'Yar'uwa shakikiya (Uwa daya uba daya) 2. 'Yar'uwa li'abiya (Uba daya uwa daban-daban) MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU KARBI FARALI WANI LOKACI SU HADA DUK Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani lokaci kuma su amshi farali, wani lokacin kuma duka gaba daya, da asibci da farali. Sune:- 1. Uba. 2. Kaka namiji. MASU GADON NISFI Kafin mu yi bayanin masu gadon nisfi, ya kamata mu san mene ne nisfi? Nisfi kalmace ta Larabci. Ma'anarta rabi (1/2). Idan an raba wani abu biyu, kowane daya daga cikinsu ya zama nisifi ke nan. Masu gadon nisfi (Rabi), su biyar ne kamar haka: 1. Miji. 2. 'Ya (Ta tsatso) 3. 'Yar da (Na tsatso) 4. 'Yar'uwa (Ta uwa daya, uba daya) 5. 'Yar'uwa (Ta uba daya, uwa daban) Wadannan su ne masu nisifi. Za mu bisu daya bayan daya; mu yi bayanin su dalla- dalla, ta hanyar da za a fahimta, in sha Allahu, domin ko wanensu yana da sharuda. Alhamdulillahi.