Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, March 16, 2013

SAKO ZUWA GA MASU AMFANI DA FACEBOOK.Hadejia A yau!Shafukan INTERNET da Wayar Hannu ta GSM....Bincike ya nuna cewa shafin internet na FACEBOOK da wayar hannu ta GSM suna daga cikin ababen dake kara rura wutar fadan addini a Nigeria.

Hakan yana faruwa sakamakon irin yadda mutane ke amfani da su wajen isar da sako atsakaninsu. Mutanen mu suna da son bayar da labari,Inma ingantacce ko mara inganci don neman addu'ar 'yan uwansu ko don nuna bajintar su ko kuma don wata manufa ta su ta daban.

Wannan yasa dayawa sukan fadi abinda basu da tabbas akansa, ko kuma suyi kari cikin labarin na su.

Ya kai dan'uwana mai son bayarda labari! Kaji tsoron Allah, kada kafadi, ko kada karubuta sai abin da kaji ko kagani kokuma kake da tabbas akansa. kasani za ka amsa tamyar Allah akan abinda kake fadi kokuma kake rubutawa a duniya (facebook), wacce amsa ka tanada?

Ba wani abin birgewa bane afara jin labarin dake tayar da hankali agurinka. Addinin muslunci ya hore mu da yin magana ba tare da ILIMI ba. Mu kiyaye ko Allah (S.W.A) ya kiyaye mu.

Ya Allah! Kakiyaye mu, kabamu zaman lafiya, Amin.

Haka kuma a Facebook zakaga GROUP ko PAGE wadanda basu da Aiki sai watsa Labarin karya. Misali sai a saka Hoton Yarinyar da bata jiba bata Gani ba wai Ace tace tana neman Miji. Wanda kuma Addinin Musulunci bai yarda da hakan ba.

Kuma 'yan mata kuji tsoron Allah duk abinda ya sameku kuke Janyowa kanku. Domin kune kuke yawan sauya Hoto dan ku Birge mutane!

A garin hakan kuma sai a samu wasu bata gari suyi downloading din hoton su dinga Talla daku.

Ko kuma Namiji ya Bude 2go da sunan mace yasa hoton wadda bata jiba bata gani ba. Wai dan ya yaudari 'yan Iska 'yan'uwansa. Allah ya kiyaye mu.

To Jama'a sai mu kula da fadar jita jita, domin karya haramun ce. Allah ya kare mu amin....