Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, August 11, 2013

JAWABIN ALH. BAIDI GAJO YELLEMAN A BUBBAN TARO DA AKAYI DON HADIN KAN Al'UMMAR MASARAUTAR HADEJIA. (KASHI NA DAYA 1)

Free Web Proxy
Jamaa Salamu Alaikum. Na tsaya gabanku ne a game da izinin da aka mani akan in yi bayani gameda “Cusawa matasa kishin masarautar Hadejia”. Shi dai kishi wani kauna ne da mutun yake dashi na wani abu, ko Kasa, Addini, Mutum da sauransu. Misali Kishin da mutum yakewa kasarsa, Mace da take game da mijinta, mutum yake game da addinsa. Wannan tsanannin kishin zai iya sa mutum yayi dukkan abinda zai iya domin yaga cewa ya amfani abinda yake kishin kuma yakare
martabarsa. Kakan yi amfani da kishi don ka cimma kyakkyawar manufa mai amfani.


Wani babban alamarine da zai sa kayi duk abinda zaka iyayi iyakar karfinka domin shi wanda kake kishin ko abinda kake kishin.


Kasar Hadejia al’ummace da Allah Yayiwa dimbin albarka ta fannoni daban daban na rayuwa Kamar dimbin masu Ilimin addini dana zamani, Manyan Sarakuna, Attajirai, Manyan yan siyasa, Manyan Maaikata tun shekaru aru aru. Idan nace kasar Hadejia ina nufin Hadejia, Auyo, Birniwa, Guri, Kafin Hausa, Kaugama, Kiri kasamma da Malam Madori.


Bari muga yanda maganar kishi ta shigo a harkar jamaar Hadejia. Sanin kowane cewa yakamata ace Hadejia ta wuce inda take dinnan kasancewarta Mai sarautar daraja ta daya tun shekaru aru aru, kuma mutanenta ne suke mamaye aikin Gwamnati tun Kano State har yanzu a Jigawa State sannan kuma a gwamnatin tarayya. To amma har yanzu mun san akwai sauran abubuwa da yawa da muke bukata don mu cimma burinmu na samarda abubuwan more rayuwa ga jamaarmu. Su
wadannan abubuwan more rayuwa kuma suna samuwane ta hanyoyi daban daban. Jamaa zasu taru su hada karfe da karfi don su
samarda wadannan abubuwa.


Amma almuhimmi shine abinda zaa samowa jammaa daga hukuma, wato Gwamnati.
Hanyoyin samu wadannan abubuwa shine zai nuna tsananin kishin da zakayi na samosu daga hukumar da abin ya shafa. Babban
maaikacin Gwamnati zai iya samawa matasa aiki a gwamnati, zai iya kawo Maaikata (Project), ko Makaranta, Titi, Asibiti. Ko ruwansha a bangarensa. Dan Siyasa zai iya amfani da mukaminsa yakawo duk abubuwan da na lissafa a sama. Attajirai zasu iya kawo kamfanoni. To idan wadannan suka hada karfe da karfi, nan da nan zaka ga
abubuwa sun bunkasa ta kowane fanni kuma jammaa sun sami biyan bukata. Ina tunanin ko muna da irin wannan tsananin kishi da nake nufi anan. Idan kuma muna dashi, to ina tunani ko muna amfani dashi yanda yakamata don ciyarda alummarmu gaba.


In Ciyaman Local Government bashi da kishi, ina zaiyi aiki?


Idan Dan Majalisa bashi da kishi, ina zai yiwa jamaa kyakkyawan wakilci?


Idan babban maaikacin gwamnati bashi da kishi, ina zai kawo ayyuka (Projects) garinsu?
Da sauransu.


Anan ina so inyi wasu yan tambayoyi: MU HADU A KASHI NA BIYU (2) DON JIN TAMBAYOYIN.

JAWABIN ALH. BAIDI GAJO YELLEMAN A BUBBAN TARON HADIN KAN AL'UMMAR MASARAUTAR HADEJIA. (KASHI NA BIYU 2)

Free Web Proxy Hadejia A yau.


Anan ina so inyi wasu yan tambayoyi:


1. Kana da kishi ne sai ka jira Mai Martaba Sarki ya tura ma tawaga a gaya maka jamaar Hadejia suna bukatar abu?


2. Kana da kishi ne sai ka jira har jamaa sunyi zanga zanga kafin ka biya musu bukata?


3. Kana da kishi ne baka son zuwa garinku ko cikin jamarka?


4. Kana da kishi ne kake yiwa garinka shigar dare kuma a mota mai tinted glass don kada a ganka?


5. Kana da kishi ne zaka rike mukamin gwamnati har kayi ritaya baka kari jamaarka da komai ba? Da sauransu.


Shi kishi ne zai sa kayi abu ba sai an sa ka ba, kuma in kayi ba sai an gode makaba. Rashin wakilci mai kyau duk rashin kishi ne yake kawo shi. Saboda haka idan dai muka dore akan wadannan abubuwa biyar da na lissafa a sama, to gaskiya babu inda zamu.


A duniyarmu ta yau, da wuya wani ya dafa maka abinci ya sa ma a bakinka. Kai ne zaka yunkura ka nemowa kanka yancinka ko kuma abinda zai amfaneka. Sabida haka dole musa kishi a zukatanmu don mu samowa lardinmu abinda yakamata daga gwamnatin Jiha har gwamnatin tarayya.
Babban burinmu shine mu sami Jiha (Hadejia State). Domin idan ka sami jiha, to duk wasu abubuwa na ci gaba zasu zo da sauki.


To amma kafin mu sami jihar, yakamata muci gaba da amfani da dimbin arzikin da Allah Ya bamu na masu ilimi, Sarakuna, maaikata,
manyan yan siyasa da yan kasuwa domin cimma duk wani cigaba da muke bukata.


Alhamdulillahi muna da Manyan maikata kamar Directors Permanent Secretaries, Ministoci, Soja, Yan Sanda da sauransu. Idan muka hada karfe da karfi muka sa kishi a alaamuranmu babu inda bazamu kaiba. Tarihi ya nuna akwai inda mutum daya mai kishi ya kawowa jamaarsa cigaba.
Saboda haka kara jaddadawa iyayenmu da yayyenmu da kuma musamman matasa manyan gobe gameda duk abinda zasuyi su sa kishi da hadin kai a gaba. Mu zama tsintsiya madaurinki daya muna haduwa da juna muna tattaunawa muna tsaida shawarwari kuma muna daukan dukkan matakin da yakamata don muga cewa mun cimma burinmu.
Matasa kune kunnenmu, kuma kune idanunmu. Saboda haka duk abinda yakamata Jamaa su sani, ku yakamata ku jaddadashi domin a dauki mataki. Har abada yin shiru baya warware matsala sai dai ya kawo rashin jituwa marar amfani Allah Yasa wannan taro ya zama dalilin samarda hadin kai da cigaba ga alummar Hadejia da Jigawa baki daya.