Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Wednesday, September 18, 2013

CIWON KODA A KASAR HADEJIA! DAGA PHARM. HASHIM UBALE YUSUF.

Hadejia A yau! Daga pharmacy Hashim Ubale Yusufu


Bismillahir Rahmanir Rahim. Assalamu Alaikum.

CIWON KODA A KASAR HADEJIA: A bisa kididdiga, kimanin mutane miliyan talatin (30million) ne ke dauke da cutar Koda a tarayyar Nigeria. (National Association of Nephrology). Yawancin wadannan mutane na mutuwa kuwa katsam daga cutukan da suka shafi makwarar jini da zuciya, wanda ke da danganta da ciwon kodar. Wannan ya nuna cewa kimanin mutane ashirin bisa dari (20%) na ‘yan Nigeria na fama da wannan ciwo, wanda ana ganin alama daga yawan karuwar masu neman tace jini (dialysis). A wasu asibitocin zaka iske kimanin mutane 200 zuwa 300 ke zuwa neman tace jininsu a rana.Cututtuka da dama na iya jawo ciwon Koda. Manyan dalilan dake hassada wannan ciwo anan karkarar sun hada da ciwo tsutsa (infections), kishirwa da kuma shaye shayen magunguna kai tsaye, Hawan Jini, shan taba da makamantansu.
Ita koda tana taimakawa jikine wajen tace dattin da kan taru a jikin mutum, sannan kuma tana taimakawa wajen tsotse ruwa, da sukari da sauran sinadaran gina jiki dake yawo a jini domin kar su bi fitsari su fice. Kenan zamu iya gani cewa idan har Koda bazata iya yin wannan tatar ba, to kuwa akwai matsala. Babban abun dazai faru kuwa shine, dattin na iya tare kofofin da jini da fitsari zasu bi, daga nan sai a fara kumbura, da kuma samun zazzafan ciwo na fitar hankali a hanyar da fitsari yake bi.
Sau tari zaka tarar mutane na aikin dake sa su zubad da gumi mai yawa, amma babu ruwa a kusa dasu. A kauyuka da rugage, zaka samu rijiyoyi sun kafe, ko kuma zasu sha ruwa gurbatacce, saboda ba inda zasu samu ruwan mai kyau su sha. Wannan bala’i ne.
Sannan kuma, yanzu wani abu wanda yake kamar gasa shine shaye shayen magunguna babu dalili ko kuma babu neman shawarar masana.
Wannan ka iyasa shan gurbatattun magunguna ko na jabu wadanda zasu iya cutar da ita kodar ta daina aiki. Haka kuma shaye shayen maganin gargajiya na daya daga cikin abubuwan da ke jawon wannan ciwo.
Akwai gazawar kayan aiki a asibitocinmu na tace jini da musayar koda, wanda hakan na jawo matsalar kai marasa lafiyar kasashen waje don warkarwa. A inda kuwa babu halin haka, sai addua kenan.