"" /> HADEJIA A YAU!: Dec 30, 2013

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, December 30, 2013

TARIHIN KAFUWAR HADEJIA A TAKAICE..

HADEJIA-TARIHIN KAFUWARTA Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, a yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a gurin. Sai ya yanke shawarar zama a wannan gurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi suw, wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Harma ya dauko Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan gurin. Kuma mutane sai suke zuwa sayen fatu da nama a wajensa. Duk wanda yazo gurin sai yayi sha'awar zama a gun, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin Haden jia. Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia. Kuma bayan zamanin wannan mutumin Hadejia taci gaba da zama gari kuma tare da shugabanci wato mulkin Habawa. Hadejia A yau! Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti, Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin garin Hadejia. Kuma Hadejia sunyi sarakunan Habe guda talatin da biyu(32) amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2, MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Mulkin Habawa ne, kuma ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia. Hadejia A yau..