Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, August 15, 2014

TARIHIN DAN-AMAR DIN HADEJIA M. USMAN GINSAU.

MARIGAYI DAN AMAR ( ALH. MALAM GINSAU) 1917 -1997……………………………..
Marigayi Dan Amar din Hadejia Alhaji Malam Usman Ginsau dan Chiroman Hadejia Ali, dan Sarkin Hadejia Haruna Maikaramba dan Sarki Muhammadu Maishahada ne. Yayi karatun makaranta a garin Hadejia.Yana daga cikin yan makaranta na farko da suko ka bude Clerical College da ke Congo a garin Zaria, kafin ta rikide ta koma ABU Zaria.

Malam ya koma England (UK) domin karin karatu a harkar Community Development. Marigayi Dan Amar ya zama Community Dev. Secretatry na Hadejia N.A. Bayan wannan aiki Marigayi ya kama aikin Gona gadan gadan har zuwa1980.

Ya zama Representative Na Hadejia NA a Old Kano State wanda ya bashi damar shiga Co -operative Society na Nigeria shi da Sarkin Ringim Alh. Sayayadi Mahmudu.Marigayi ya zama 2nd Vice President na Co-operative Society of Nigeria. Yayi Ritaya daga wannan aiki a 1980.

Daga nan Marigayi ya kafa Makarantar Islamiyya da ta Karatun Alkura’ani a Gidansa, shi da kansa yake karantar da mutane, wato manya da yara. Malam yayi ta yin wannan aiki har zuwa 1983 a lokacin da aka nada shi Dan Amar din Hadejia, Hakimin Kafin Hausa.Malam yana daya daga cikin dattijan da suka tsaya wa Kasar Hadejia da addu’a da kuma bada gudummawa wajen duk wani aiki na dattako a Kasar Hadejia. Malam ya rasu ya bar ‘ya ‘ya ashirin da shida.. Daga cikinsu Akwai Dan-Amar din Hadejia na yanzu Alh. Aliyu Usman Ginsau, Hakimin Kafin-hausa, da Baraden Hadejia, Alh. Haruna Usman Ginsau.

Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya kara sa albarka a zuriyar da ya bari. Ameen.Posted from WordPress for Android via Hadejia A yau.