Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, March 6, 2014

TAURARINMU HADEJIAWA (Part four 4)

DAGA MUHAMMAD IDRISHadejia A yau! 

FARFESA HARUNA WAKILI...............Farfesa Wakili haifaffen kofar fadar Hadejia ne, kuma kamar yadda sunansa ya nuna mahaifinsa shi ne Wakilin kudun Hadejia [Dandalma] wato mai kula da yankin kudancin garin Hadejia.

Farfesa Wakili shi ne Farfesa na biyu a masarautar Hadejia kuma yana daya daga cikin `yan majalissar dattijai na Jami`ar Bayero ta kano kuma babban Alaramma a tsangayar tarihi ta makarantar, harwayau shi ne Mufti akan harkar tarihi a Arewacin kasar nan dominkafafen watsa labarai da dama na ciki da wajen Nijeriya suna dogara da fatawowinsa wajen warware matsalolin tarihi da suka bujuro musu.Baya da harkokinsa na cikin Jami`a Farfesa Haruna Wakili ya rike Daraktan Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa na Jami`ar wato MUMBAIYA dake Gidan Malam Aminu Kano a Unguwar Gwammajar kano.

" Na zaune bai ga gari ba", wanda bai sanJami`a ba, ba zai san gudunmawar Wakiliba domin a shekaru ashirin da biyar da suka gabata duk dan masarautar Hadejia da ya je Bayero ofishin Wakili ne zangonsa, shi kansa ba zai iya kididdige daliban da ya yi wa hanyar karatu a jami`a ba.

"Mai kamar zuwa kan aika" Yana cikin wannan gwagwarmaya Allah [swt] ya yi masa kwamishinan Ilmi na Jihar Jigawa. wannan mukami nasa duk Bahadeje mai hankali ba zai taba mantawa da shi ba domin baya da ci gaba a gyaran makarantu da samar da aiyuka da matasa da ya yi to kuma a lokacinsa babbar bukatarmu da muka dade muna nema ta neman babbar makaranta ta kai ga biya wato muka samu Jami`ar Kafin Hausa kuma aka gina babbar makarantaraiyukan gona ta Hadejia ta bar lungu ta dawo kan hanya.

Farfesa Haruna Wakili cikakken Bahadeje ne ba ya son raini amma yana da kishin al`ummarsa yana son ci gabansu kuma saboda daga darajar wannan masarauta shi rubutunsa ma na digirinsa na biyu akan wannan Masarauta ya yi.a takaice dai rayuwarsa akan bautawa Ilmi take.Hadejawa suna addu`a Allah Ya ba gwanin yafe gwado.FARFESA HARUNA BIRNIWA............kamar yadda sunansa ya nuna Farfesa Haruna Birniwa haifaffen garin Birniwa ne kuma yana cikin haular masu mulkin garin.Birniwa shi ne farfesa na farko a cikin wannan masarauta kuma farfesa nabiyu a fadin Jihar Jigawa.


Gaba daya rayuwar Birniwa a kan bautawa Ilmi take domin ya kasance daya daga cikin dattawan malamai a Jami`ar Danfodiyo dake Sokoto na shekaru masu yawa kuma ya rike 'provost' a kwalejin Ilmi dake Gumel sannan ya rike kwamishinan Ilmi a wannan Jiha.

Farfesa Birniwa ya bayarda gudunmawa a fagen bayarda ilmi a Jihar nan matuka domin daruruwan mutane sun ci moriyarzamansa a sokoto domin shi 'admission' a wurinsa kamar mutum ya mari budurwa ne don haka za a ya ce wa shi ne ya budewa Hadejawa kofa a sokoto kuma bai bar sokoto ba sai da ya yi dashe.
Lokacin yana 'provost' ma masu rabo sun samu aiki a wurin.Birniwa ba harkar ilmin zamani kadai ya tsaya ba domin fakihi ne a fannin addini kuma fahintarsa da addini ta kara sa kyawawan halayensa sun kara kyautata domin mutum ne mai hakuri da gaskiya da rikon amana da saukin kai.wani abun sha`awa ga halayensa mai unguwarsa a Hadejia ya ce in dai yana gari duk yadda za a je neman ci gaba da shi ake yi. munaaddu`a Allah ya albarkaci bayansa.