Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Wednesday, August 5, 2015

JAWABIN MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALH. ADAMU ABUBAKAR YAYINDA AKA TABBATAR DASHI CHANCELLOR A UNIVERSITY UYO.

Hadejia A yau!


JAWABIN MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALHAJI ADAMU ABUBAKAR MAJE C.O.N. A LOKACIN DA AKA TABBATAR MASA DA MATSAYIN CHANCELLOR NA UNIVERSITY OF UYO. A RANAR LARABA 3/AUG./2015.

Ya fara da yabo da godiya ga Allah (swa.), sannan ya gabatar da vice chancellor na University of Uyo da tawagarsa da sauran manyan baki. Yace nayi farin ciki da jin dadi game da zuwanku Hadejia domin tabbatar dani a matsayin Chancellor na wannan makaranta wadda kuke shugabanta. Yace Bazan manta ba wata rana nayi tafiya zuwa Amurka sai naji wani ya kirani a waya yana sanar dani cewa yagani a Jarida an bani Chancellor a University ta Uyo, nayi mamaki matuka da gaske saboda banyi tunanin haka a zuciyata ba. Sannan nayi godiya ga Allah (swa.) wanda da ikonsa da kudirarsa ne hakan ta kasance.

Ina farin cikin tabbatarwa Gwamnati da kuma Al’ummar Nigeria cewa zamuyi aiki da gaskiya ba tare da banbanci ba domin mun kasance kasa daya Al’umma daya. Wani abin Alfahari shine ita wannan Jami’a ta kasance a yankin da na fara karatuna na Secondary, saboda ina daya daga cikin wadanda sukayi federal government college, Ikot-Ekpene. Kuma na dawo gida zan tallafa ga abinda aka tallafa min.

Babu bukatar inja dogon zance saboda Bakinmu yau zasu koma kano domin su hau Jirgin da zai kaisu Abuja, lalle ina mai farin cikin da kuma godiya gareku domin zuwa da kukayi kasar Hadejia don ku gabatar min da wannan abin Alkairi wadda bazan taba mantawa ba a rayuwata. Kuma zanyi amfani da wannan dama in gabatar da godiyata ga wadanda suka samu damar Halartar wannan taro domin tayani murna. Kuma ina rokon Allah (swa.) ya maidaku gida lafiya tare da duk wadanda suka halarci wannan taro.
NAGODE……..

Mai Martaba Sarkin Hadejia shugaban Majalissar Sarakunan Jihar Jigawa…
Alhaji Adamu Abubakar Maje C.o.n.