Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, November 28, 2015

SARKIN HADEJIA ABDULKADIR. 1909/1925.....

HADEJIA A yau!

(12) SARKIN HADEJIA ABDULKADIR DAN HARUNA…. (1909-1925)
Sarkin Hadejia Abdulkadir ya gaji sarautar Hadejia bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin Hadejia Haruna Maikaramba a cikin shekarar 1909, an nada shi Sarki yana da shekara goma sha shida (16). Sai akayi sarki mai farin jini da son Nishadi, a zamanin mulkinsa ya maido da sha’anin mulki wanda aka daina lokacin mahaifinsa. Sarkin hadejia Abdulkadir a zamaninsa Ilmin Boko ya shigo kasar Hadejia, inda aka gina Makarantar Elementary a Unguwar Dallah. Kuma a zamaninsa ne aka fara gina Asibiti a Hadejia, wadda take a unguwar Bayi, kafin a dauketa ta koma Tsohuwar Asibiti. A zamaninsa ne ya kirkiro hawan sallar Gani wanda akeyi a watan Mauludi, da kuma hawan Bariki. A cikin shekarar 1910 sarkin Hadejia Abdulkadir ya fara hawan sallar Gani kuma ya kirkiro wannan hawa ne a cikin watan da aka haifi fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (s.a.w.) inda ake hawa da yamma ake zagaya gari musamman Unguwannin da suke da Tsangayoyi a wancan lokacin, Yakan biya yayiwa Malaman su murnar zagayowar watan Rabi-ul Awwal. Haka kuma a zamaninsa ne ya kirkiro Hawan Bariki domin zuwa gidan D.O. don kai masa ziyara da kuma nuna Al’adunmu na gargajiya gareshi.

A zamanin Sarkin Hadejia Abdulkadir aka kirkiri ZAMAN JIMLA, wato yin Gundumomin Hakimai, saboda a baya ana yin ZAMAN DAKO ne inda ake tura fadawan Sarki suje su zauna a gari domin su kasance sune masu kula da karbar Haraji da kula da sha’anin Kaasa, kuma sune masu kare kasar Hadejia daga hare haren Abokan gaba, kamar yanda mukaji a baya an tura Jarma Mamman ya zauna a Dakayyawa don ya kula da iyakar Hadejia da Kano, haka kuma Mabudi Hausa ya zauna a Kafin-hausa don ya kula da iyakar Hadejia da Katagum da wani bangare na kasar Kano. To a zamanin Sarki Abdulkadir sai ya kirkiri sabin Hakimai ya turasu Gundumomi domin su kula da wannan yankin kuma su tayashi gabatar da sha’anin Mulki. Hakiman da Sarkin Hadejia Abdulkadir ya tura sun hada da………