Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, March 20, 2016

14. SARKIN HADEJIA HARUNA DAN ABDULKADIR… (1950-1984)


Bayan rasuwar sarkin Hadejia Usman a shekarar 1950, sai aka nada Chiroman Hadejia Mallam Haruna a matsayin sarkin Hadejia na goma sha hudu(14), kafin nadin nasa shine chiroman Hadejia Hakimin Kafin-hausa. An nada shi a ranar Talata 1/august/1950, kafin ya zama sarki shine chiroman Hadejia Hakimin Kasar Kafin-hausa. Yayi karatun Allo a wurin Limamin Hadejia Muhammadu, yana karatun ne aka daukoshi aka masa sarautar chiroman Hadejia Hakimin Gundumar Guri a shekarar 1921. Bayan yayi shekara biyu yana Hakimcin Guri sai aka kaishi makarantar Lardi dake shahuci kano a shekarar 1923, sannan aka nada wakilin Hakimi aka tura Gundumar ta Guri. A farkon watan April 1950 an canjashi zuwa Hakimin Kafin-hausa, daga nan bai jima ba sai Allah ya yiwa Sarkin Hadejia Usman rasuwa kuma aka zabeshi ya zama sarkin Hadejia na goma sha hudu (14). Hadejia A yau! By Ismaila A. Sabo.

Bayan zamansa sarki Alhaji Haruna Abdulkadir sai yaci gaba da ayyukan raya kasa inda ya fadada aikin ilmi yasa aka gina makarantun primary a manyan garuruwan kasar Hadejia inda adadinsu ya kai har guda Talatin da biyar (35), sannan aka daga darajar makarantar middle ta fantai ta zama sakandire kuma aka kara yawan ajujuwa da dakin kwanan malamai. A bangaren yaki da jahilci shima an gina ofis don kula da koyar da dattijai Ilmi, sannan aka bude makarantun islamiyya Birni da karkara kuma ake koyawa mata sana’ar hannu. A zamaninsa Sarkin Hadejia Haruna ya gina dakin Nazari da adana littatafai (Library) a garin Hadejia inda aka ginata a yamma da Ramin Nasarawa dake unguwar Ilallah, kuma aka zuba littatafai da Jaridu na kasar nan dama kasashen ketare don jama’a su samu damar yin nazari. A gefe daya kuma aka saka Radio da Garmaho da Majigi don nishadantar da jama’a da jin halinda kasa take ciki.
A zamaninsa sarkin Hadejia Haruna ya gina............ www.facebook.com/Ismaila.asabo http://bit.ly/K2WOg4

posted from Bloggeroid