content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!: Aug 12, 2016

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, August 12, 2016

SARKIN HAƊEJIA ABUBAKAR MAJE HARUNA (1984-2002).



Bayan rasuwar Sarkin Haɗejiya Alhaji Haruna sai aka naɗa Ɗansa Alhaji Abubakar Maje Haruna a matsayin Sarkin Haɗejiya na goma sha biyar (15), A jerin sarakunan Fulani, an naɗashi ranar Juma'a 31st/august/1984. Sai akayi Sarki mai farin jini da hakuri da son mutane, a wajen kyauta kuwa ya kasance mai Alheri tun yana ƙaraminsa. Sarkin Haɗejiya Abubakar kafin zamansa sarki yayi Ayyuka da dama, sannan ya kasance Ɗan kasuwa.

A zamaninsa an samu sauye sauye da dama a ƙasar Haɗejiya, musamman Ɓangaren Ilmin Addini dana zamani Kasuwanci da siyasa. Sarkin Haɗejiya Abubakar Maje ya halarci makarantu da dama inda ya fara halartar makarantar Elementary dake Unguwar Dallah a shekarar 1945, sannan ya tafi makarantar Middle School dake Unguwar fantai a shekarar 1949 zuwa 1952. Haɗejia A yau.

Sarkin Haɗejiya Abubakar ya tafi makarantar T.T.C. Maru dake a Lardin Sokoto a wancan lokacin, ya fara a cikin shekarar 1953 zuwa 1956. Sarkin Haɗejia Abubakar ya koma makarantar horar da ma’aikata dake Potiskum ta jihar Borno, wadda yanzu take a jihar Yobe. Kuma ya fara aikin gwamnati a matsayin Malamin Hakimi a Gundumar Bulangu, sannan ya riƙe muƙamin Magatakarda a majalissar Sarki. Saboda iya mu’amala da son jama’a sai yazama duk inda ka ganshi bazaka ganshi shi kaɗai ba sai da jama’a, hakan ya bashi nasarar gogewa wajen tafiyar da shugabancin jama’a. Haɗejia A yau.

A zamaninsa an samu ci gaba da yawa a ƙasar Haɗejia ta kowane fanni na rayuwa, musamman zaman lafiya da Kwanciyar hankali, sannan an samu bunƙasar garin Haɗejia wajen gine ginen zamani da gina sabin Unguwanni. A zamaninsa aka rushe ƙofar Garin Yamma da ta Arewa aka Gina sabi domin dacewa da zamani sannan aka sake gina Sabi guda uku, an gina ɗaya a Kusa da Kadime ɗaya kuma an ginata a hanyar Gumel da kuma hanyar Nguru. A zamaninsa an gina sha tale-tale (Round about) guda biyu ɗaya a yamma da kofar garin yamma, ɗaya kuma a Titin Tashar mota tsohuwa, sannan anyi sababbin hanyoyin mota a ciki da wajen Haɗejia. A zamaninsa....... Hadejia A yau! A duba littafin Fulani da mulkinsu na Ismaila A Sabo.
posted from Bloggeroid