"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, May 5, 2012

UMAR MUSA 'YAR-ADUA

Umaru Musa Yar'Adua
Shi dai marigayi Malam Umaru Babangida
Musa 'Yar'Adua, an haifeshi ne a ranar 16
ga watan Augustan 1951 a birnin Katsina
dake arewacin Najeriya. Mahaifinsa shine
tsohon ministan birnin Lagos na farko a
jamhuriya ta farko, kuma kafin ya rasu
shine Matawallen Katsina, sarautar da
kuma shi ma marigayi Umaru Musa
'Yar'Adua ya gada.
Marigayin ya fara makarantar Firamare ta
Rafukka a 1958 kafin a mayar da shi
makarantar Firamare ta kwana dake
Dutsen Ma a 1962. Ya kuma halarci
kwalejin gwamnati dake Keffi daga 1965
zuwa 1969. Sai kwalejin Barewa 1971,
inda ya samu takardar shedar karatu ta
HSC.
Tsohon shugaba 'Yar'Adua ya halarci
Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya daga
1972 zuwa 1978 inda ya samu takardar
shedar digiri akan kimiyyar haɗa sinadirai
ko Chemistry da Malanta, kafin ya koma
domin samun babban digiri duk dai akan
kimiyyar ta Chemistry. Marigayin yayi bautar
ƙasa a jihar Lagos inda ya koyar a wata
makaranta da ake kira Holy Trinity daga
1975-1976.
Bayan da ya kammala aikin yiwa ƙasa
hidima ya fara aikin Malanta gadan-gadan
a kwalejin share fagen shiga jami'a da ake
kira CAST dake Zariya a tsakanin 1976
zuwa 1979. A shekarar 1983 marigayi
Malam Umaru Musa 'Yar'adua ya bar aikin
Malanta ya fara aiki da Gonar Sambo Farms
a Funtua dake jihar Katsina inda ya zama
GM daga 1983-1989.
Daga shekarar 1984 bayan da Sojojin
sukayi juyin mulki malam Umaru Musa
'Yar'adua an kira shi domin zama wakili a
hukumar gudanarwar kanfanoni da
hukumomin gwamnati da dama da suka
haɗa da hukumar samar da kayan Noma
da kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar
katsina, Bankin Habib da Hamada Carpets
da Madara Limited da kuma kanfanin buga
Jaridu da Mujalla ta The Nation wanda ke
kaduna kuma wansa Marigayi Janar Shehu
Musa 'Yar'Adua ya mallaka.
A lokacin da marigayi Malam Umaru Musa
'Yar'Adua ya shiga siyasa ya yi hannun riga
da mahaifinsa wanda a wancan lokaci yake
mataimakin shugaban Jam'iyar NPN, inda
shi kuma ya zama wakili a jam'iyar PRP ta
Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A
lokacin da Janar Babangida ya kaɗa gangar
siyasa ya zama sakataren jam'iyar SDP a
jihar ta Katsina kuma ɗan takararta na
gwamna, amma kuma ɗan takarar
jami'iyar NRC na wancan lokaci Malam
Saidu Barda ya kada shi. To sai dai a 1999
Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya tsaya
takakarar muƙamin gwamnan jihar ta
Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin
jam'iyar PDP, haka kuma ya sake nasara a
zaɓen 2003.
A shekarar 2007 Umaru Musa 'Yar'Adua ya
zama ɗan takakar muƙamin shugaban
ƙasa na Jam'iyar PDP bayan ya samu
taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif
Olusegun Obasanjo ya zama shugaban
ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban
yayi fama da ita ta sanya bai samu sukunin
gudanar da harkokin mulki kamar yadda
yayi fata ba musanman ƙudirorinsa guda
bakwai daya tsara na ciyar da ƙasar gaba
kafin nan da ƙarni ta 2020.
Marigayi Malam Umaru Musa 'Yar'Adua ya
rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta
2010 da muke ciki a fadar gwamnati dake
Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida
daga Saudiya inda yake jinya.
Ya kuma rasu ya bar mahaifiyarsa da
'yan'uwa da matar aure guda Hajiya Turai
tare da 'ya'ya bakwai da ya haifa da ita da
suka haɗa da mata biyar da maza biyu.
Haka kuma yana da wasu 'ya'ya biyu maza
da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar
Radda.

Tuesday, May 1, 2012

DAGA JIMEH SALEH B. B. C. HAUSA..

Image Hosted by ImageTitan.comJama'a da dama sun kauracewa birnin Maiduguri sakamakon rikicin Wakilin BBC Jimeh Saleh ya kai ziyara zuwa mahaifarsa ta Maiduguri a Arewacin Najeriya a karon farko cikin shekara guda - inda ya tarar da garin a cikin wani mawuyacin hali sakamakon munanan hare-haren da kungiyar Boko haram ke kaiwa.


A daidai lokacin da rana ke shirin faduwa; duhu kuma na kara yi, wani ladani na rangada kiran salla. Karar muryarsa na tashi daga saman daya daga cikin tsaffin masallatai na birnin.


Jama'ar musulmai sun gudanar da sallah Magrib - inda suke hada wa da Isha'i saboda akwai dokar hana zirga-zirga daga karfe bakwai zuwa shida na safe. Halin da ake ciki a yanzu na rashin tabbas da tsaro - ya sha banban da birnin Maiduguri da na taso a ciki. A 'yan watannin da suka wuce, kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a sassan Najeriya da dama - ciki harda na bama-bamai a Maiduguri.


Na isa Maiduguri bayan na dawo daga London a karon farko cikin shekara daya, birnin na nan cikin kamar yadda na barshi - sai dai talauci ya karu - haka kuma jama'ar garin masu hazaka da hadada. Babu masu motocin haya, masu bara, da shaguna wadanda ke kaiwa dare suna harkokinsu.


A yanzu jama'a ba sa iya cin abinci sau ukku a rana. Masu hada-hadar gidaje na cewa a yanzu harkar babu riba, wasunsu ma asara suke tafkawa. "Rufe shago karfe 7 na yamma daidai yake ace mutum ya yi aikin rabin rana," a cewar wani masanin tattalin arziki a jami'ar Maiduguri, wanda kamar yawancin mutane, ya nemi a saya sunansa.


"Muna cikin matukar tsoro," kamar yadda wani mazaunin birnin ya shaida min, "kuma kai kadai ne dan jaridar da zan iya magana da shi, saboda kaima na sanka, amma don Allah kar ka bayyana sunana."


Mutane da yawa sun kauracewa Maiduguri watanni da dama da suka gabata saboda kashe-kashen da ake yi, inda suka bar gidajensu a kargame. Wasu daga cikin attajiran birnin sun yi kaura da harkokin kasuwancinsu zuwa wasu biranen. An kafa dokar tabaci a Maiduguri bayan da aka kai harin ranar kirsimetin 2011 a Abuja da Jos wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 40.


Tun daga wancan lokaci, sojoji dauke da muggan makamai suka kafa shingayen bincike a sassa daban-daban na birnin, tare da tsaurara matakan tsaro a majami'u da ofisoshin 'yan sanda da sauran wuraren da Boko Haram ke kaiwa hari. An tura sojojin ne domin su kare mazauna birnin - sai dai baki ya zo daya wurin yin Alla-wadai da dokar hana zirga-zirgar da aka sanya da kuma yadda suka mamaye titunan birnin.


Sun zargi sojojin da cin zarafin jama'a da sauran laifuka masu alaka da cin zarafin bil'adama. Da zarar an kai hari, sai sojoji su shiga unguwanni suna farautar mutane a cikin gidaje tare da nakadawa maza duka. Sojojin dai sun musanta wannan na faruwa - amma abu ne mai wuyar musantawa saboda yadda jama'a ke nanata shi a kodayaushe.


Babban layi ne wurin da aka fi yin hada-hadar kasuwanci a birnin ta hanyar sayar da kayayyakin sawa, da na latironi da sauran kayan al'amura na yau da kullum. Kwarori da 'yan Chadi da sauran jama'a na fadi tashin futuka a wannan wuri domin amfana daga arzikin da ke akwai - sai dai a yanzu komai ya tsaya a wurin. Daga cikin 'yan wadanda da suka yi sa'a su ne masu sayar da kekuna da kuma kani-kawa: Kasuwar kekuna ta bude tun bayan da aka hana hawa babur a bara sakamakon hare-haren da ake kaiwa a kan baburan.


Sai dai duk da haka wasu da dama na fatan abubuwa za su daidaita a birnin Maiduguri, mafi yawa kuma sun koma ga Allah domin yin addu'a ko an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali - wanda a baya shi ne taken mahaifata ta Maiduguri.