content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, June 17, 2012

WASIKA DAGA AJI KIMA ZUWA GA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR HADEJIA

Free Web Proxy
Budaddiyar wasika ga mai girma shugaban karamar shukumar Hadejia da yan majalissarsa.
Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, ina mai farin
cikin rubutoma wannan takardar domin in nuna irin
goyan baya da nake bawa wannan jam'iya da wannan gwabnatin mai albarka, bayan haka ina jinjinama bisa irin kokarin da kake wajen ciyarwa da
wannan karamar hukuma gaba. Ina sake jinjinama da yadda kake gudanarwa da mulkinka cikin
kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Bayan haka ina so nayi amfani da wannan damar na tunatar da kai wasu muhimman abubuwa
wanda idan kayi su zasu taimakama wajen samin sahihiyar
hanyar ci gaba da kuma adana tarihi ko bayan
ranka, wannan abun kuwa sune kamar haka.
Kasancewar garin hadejia babban gari ne mai tsohon tarihi a jeri garuruwan Hausa to ya kamata
ace yau akwai abubuwan da zamu yi alfari da su wajen tarihi kamar yadda ya'u idan kaje Daura zaka tarar da abubuwan da suka faru shekaru dari uku ko hudu
da suka shude kamar yau akayi su.
Ma'ana muma a garin Hadejia muna da irin guraren
nan kamar kabarin mai tumbi, kofar mandara, ruwan Atafi, Rijiyar turawa, mabuga, majema, marina, bariki da sauransu.
Kuma ya kamata ana tunawa da mutanan da suka bawa wannan gari gudunmawa misali saka
sunayensu a titinah,dakin taro makarantu dasauransu. mutane irinsu Alh Haruna uji ya kamata a
na tunawa dasu, amma abin al'ajabi aka saka sunayen mutane a titinah aka manta da Haruna
uji, wanda ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen daukaka masarautar hadejia.
Saboda haka a madadin daliban Hadejia emirate ina
mika wannan sakon ga maigirnma shugaban karamar hukuma da fatan za'a duba. Nagode.
Comrade Aji kima hadejia secretary general Hadejia student Association.

Thursday, June 14, 2012

MANYAN BORNO SUN ROKI DA A KAWO KARSHEN RIKICIN BOKO HARAM

HADEJIA A YAU! Al'ummar Jihar Borno dake Arewacin Nigeria sun Roki 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunna lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram da su Amince a tattauna dasu da Gwamnati domin a kawo karshen Hare harenda yake janyo Rasa rayuka da gidaje. A wata fira da yayi da 'yan jarida a Maiduguri Dr. shettima Ali Munguno ya bayyana rikicin boko haram a matsayin rikici ne wanda ya janyo Asarar rayukan Al'umma da gidaje, kuma ya janyo Rashin aikin yi ga Al'umma. Ya bayyana cewa mutane basu kwanciyar hankalin da zasu tafiyar da rayuwarsu a tsinake, ko harkokinsu na yau da kullum.uma ya bayyana cewa Jama'a basu samun salloli Biyar a cikin Jam'i saboda fargabar abinda zai kasance,Saidai mutum yayi sallarsa a cikin gidansa saboda rashin samun nutsuwa. Dr.Ali Munguno ya kara da cewa yana rokonsu da su Amince a tattauna dasu domin a kawo karshen Asarar rayuka da ake. yace a matsayinsu na 'yan kasa suna da ikon rayuwa a jikin mutane ba tare da tsangwama ba. yace duka mu da su kasarmu ce, bamu da wata kasar da tafi wannan. kuma ya kara da cewa Gwamnatin tarayya tare da gwamnatin Jiha a hada hannu wajen tattaunawar domin a kawo karshen wannan Al'amari.