"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, June 30, 2012

GWAMNATIN JAR HULA. SAI KANO


HADEJIA A YAU! Tarihi shike maimaita kansa! Kamar yanda aka sani a da can mun san wasu dattijai wadanda kullum Adonsu shine: farar riga bakin takalmi da Jar hula. Bamu sani ba ashe adon nasu yana da fa'ida, ba wai suna yi bane dan kansu. A lokacin jamhuriya ta daya anyi jam'iyyun siyasa da dama a cikinsu har da NEPU. Kuma kowace jam'iyya tana da nata taken kuma tana da Tuta Irin tata. To ashe wannan adon da mukaga wasu daga cikin Dattijanmu sunayi ado ne mai ma'ana saboda suna cikin jam'iyyar NEPU. Kuma sun saka akidarta a ransu shi yasa suka maida adonsu irin na tutar jam'iyyarsu. Haka ma a jamhuriya ta biyu anyi jam'iyyu da dama a ciki harda P.R.P. Kuma su 'yan jam'iyyar NEPU sune suka kafa P.R.P. Dan haka sai suka sake saka alamarsu ta da can ta zama itace dai alamar P.R.P.
KWANKWASIYYA!
A shekarar 2011 Kano ta sake maimaita wannan tarihi karkashin Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso Inda ya dawo da wancan adon na 'Yan NEPU. Shima ya maida adonsa farar riga da Jar hula kuma hakan ya samu karbuwa ga jama'ar kano. Yanzu farin yadi da jar hula kasuwarsu tafi garawa ba wai kano kadai ba harda jigawa da Bauchi da Kaduna da Katsina. Sai dai da yawa masu saka Jar hula in ka tambayesu basu san Ma'anar Hakanba. Kawai dai sunga Kwankwaso yana sakawa.

Wednesday, June 27, 2012

KANO GARIN ALHERI.


HADEJIA A YAU! Kano ba gari ba Dajin Allah Inji masu iya magana! Tarihin kano abu ne wanda sai dai ace an baka kadan daga cikinsa, domin tarihinta bazai kammalu ba ga duk mai rubuta shi. An kafa kano tun a farkon karni na biyar bayan haihuwar Annabi Isah (AS) wato 500AD. Idan akayi la'akari da zuwan Bagauda da mutanensa. Tun daga wannan lokacin ake mulkin kano kawo yanzu mulkin fulani.
Kano ta shahara ta fannoni daban daban kama daga Ilmin Addini da na boko da kuma Uwa uba kasuwanci wanda ta zama babu kamarta a duk jihar Arewa. Al'adunsu da dabi'unsu abin koyi ne ga duk wanda yayi mu'amala dasu. Allah ya albarkaci kano da Ni'imomi daban daban wadanda basu misaltuwa. Kasuwa kuwa duk abinda ka sani ana sayarwa a duniya zaka samu a Kano, kuma duk abinda kake sayarwa zaka samu masu saye.
Kano ta zama wata cibiya ce wanda duk abinda ya sameta lalle ya samu duk jihar Arewa baki daya. A watannin baya ne kano ta samu kanta a wani hali wanda bata taba zatonsa ba. Wato na hare haren bom da kashe kashen jama'a wanda hakan ya kawo cikas a al'amuran yau da kullum. Amma duk da haka ba'a fasa saye ana sayarwa ba kamar yanda aka saba. Lalle duk abinda ya taba hanci to idanu zaiyi ruwa! Wato duk abinda ya taba kano to hakika ya taba Arewacin Nigeria.
Jama'ar kano da ma Arewacin Nigeria... Na rigingine fa ba-a fada masa ganin farin wata. Ina nufin mun san gurin wanda zamu kai kukan mu, shine sarkin da ya kafa kano ya albarkaceta da mutane Irin su WAZIRIN KANO, Da sauransu. Muna rokon Allah ya karemu daga duk abinda zai kawo barazana ga Kano da ma Arewacin Nigeria. Allah ka mana maganin abinda yafi karfinmu da abinda bamu zaton sa. Domin da ikonsa ne komai ya kasance da kuma abinda zai kasance. KANO KWARYAR KIRA MATATTARAR ALKAIRI. Daukar Nauyi freedom Radio kano.