content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, November 19, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI. (KASHI NA 2)



BY COMRADE GARBA MUHD HADEJIA


A lokacin da makiyaya su ka fara yin ta'adi a gonakin mazauna yankin ba a gayyaci kowace hukuma a cikin al'amuran ba, ganin cewar matsalar karama ce a wancan lokacin. Kuma su manoman basu san hakikanin irin fulanin da suke yin wannan ta'adin ba. Har su kan yi tunananin cewar wai shin fullo-Hadejia ne ko Zamfarawa?


Faruwar hakan ta ja hankalin shugabannin mazauna yankin (manoma) wadanda suka hada da Dagatai,Bulamai, Lawanai (Bade), Mai (Gizimawa) don tattauna matsalar da shugabannin Fulani irinsu Lamidai da Hardawa. Irin wannan tattaunawa ta yi ta faruwa har hukuma ta shigo cikin sabgar don rushe dukkan wani yunkuri na barkewar rikici. Saboda abin ya na faruwa duk shekara musamman ma da kaka. Duk da shigowar hukuma cikin lamarin, bai hana daukar fansa daga manoman ba, saboda kai su bango da makiyayan suka yi na cinye musu amfanin Gonakinsu.


A duk shekara a kan asarar rayuwa daga kowane bangare. Duk da kasancewar jami'an tsaro kala-kala; yan sanda, mobile police, wani lokaci har da sojoji don sasanta tsakanin manoma da makiyaya. Suma jami'an tsaron daga bangarensu sun rasa da yawa daga cikin mutanensu. Wasu an harbe su da kibiya, wasu an sassarasu da arda sun mutu wasu an lagarta su, saboda hukuma bata basu damar harbi ba.


A kwai shekarar da har jirgi mai saukar ungulu (Helcopter) aka kai yankin don shiga surkukin dajin da ke wannan yankin. Daga cikin matsalolin da jami'an tsaro su ke samu daga wannan yankin, shine rashin basu umarnin daukar mataki na kare kansu daga dukkanin wanda zai yi yunkurin harbinsu ko sararsu. Haka tasa suke janye jikinsu daga shiga cikin rigimar gadangadan. Daga bangaren gwamnatocin siyaya an samu da yawa da suka taka rawa don ganin an shawo kan matsalar amma idan shekara ta zagayo sai an yi.Haka kowace gwamnati take yi.


A lokuta da dama akan kafa kwamatoci na musamman wanda zaiyi bincike akan matsalar, amma daga karshe sai a kasa cimma komai. Su kan nemi zama da kungiyar manoma da makiyaya da shugabannin kowane bangare don kowa ya jawa mutanensa kunne amma daga karshe sai abin ya bi iska. A wasu lokutan korafe-korafe su kanyi yawa daga bangarorin biyu na zargar junansu da laifin tayarda rigimar. Makiyaya su kan ce laifin manoma ne da suke noma makiyayar dabbobi da burtalai, su kuma manoma su ce laifin makiyaya ne da baza su yi hakurin barinsu su tare amfanin gonarsu ba.

Haka dai ake ta maganganu a kai. Daga lokacin da gwamnati mai mulki a yanzu ta hau. Ta yi kokarin lallai kowane makiyayi ya tsaya a makiyayarsa. Sannan ta tabbatar da kowane burtali da makiyayar dabbobi ba a nomashi ba. Sai dai wani abin mamaki har yanzu abin bai chanja ba, domin wannan rigimar bata mutu ba. Ko shekarar da ta wuce ma an sami rikici a wasu garuruwa irin su Gagiya da Garin Mallam. wadanda su ke kudancin Guri. Ko a wannan lokaci da ka ke karanta wannan rubutun ma, an sami wadansu daga cikin makiyaya suna shiga gonakin manoma suna cinye musu Amfanin gona. Wannan matsalar ta kawo ci baya gagarumi a kudancin Guri. Domin manoma da yawa sun hakura da noman shinkafa, Alkama, Wake da kankana. Abin da ya rage kawai sai gero da dawa, wanda a yanzu a kansu ake yin wannan rigimar domin shi din ma yana neman fin karfinsu.

Babban dalilin da ya sa manoman su ka hakuri da noma wadansu daga cikin amfanin gonar shine. Yawan zubda jinin al'umma da ake yi sakamakon kare dukiyoyinsu. Saboda wasu lokutan har garuruwansu (manoman) ake binsu don a halaka su. Wata shekara akwai garin da aka kona kurmus; tare da abincinsu, da dabbobinsu da dattijai da kananan yara wadanda ba za su iya guduba. Daga karshe, ina kira ga duk wanda ke ziyartar wannan dandali mai albarka, kuma ya kasance mai iko, da ya isar da wannan sakon ga hukumomin da abin ya shafa su duba al'amarin wadannan bayin Allah don kawo masu karshen wannan matsalar.


Sannan 'Yan majalissu na tarayya da na jiha da su kalli wannan abin ta hanyar janyo hankalin gwamnatin tarayya da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen warware wannan matsalar. Abin da gwamnati ya kamata ta lura da shi, shine wannan matsala ce ta cikin gida tsakanin manoma da makiyaya. Kuma suma wadannan makiyaya (fulani) 'yan uwanmu ne musulmi, sannan mun zo daga bangare daya, kuma tare muke zaune, kasuwa da ya muke ci da su ga auratayya ta hada mu.

Saboda haka ba sai da bakin bindiga za a sasanta ba, a'a akan tabarma za a zauna tare da kwararru a fannin warware rikici wadanda suka karanta (conflicts Resolution) da malaman addini da sauran masu fada a ji a cikin al'umma don a tabbatar da adalci tsakanin manoma da makiyaya. HADEJIA A YAU.

Sunday, November 17, 2013

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MANOMA DA MAKIYAYA A KUDANCIN GURI...(1)

Hadejia A yau!
Daga Garba Muhammad Hadejia....
CIWON CIKIN BAREWA A DAJI.

Zamantakewa wata aba ce wadda ta ke kasancewa tsakanin kowane jinsi, na mutane, aljannu, dabbobi da tsuntsaye da sauran halittu. kowane jinsi daga cikin halittu yana da irin kalubalensa na neman cika jakar ciki da sauran bukatu wadanda dole sai an cimma su za a samu dorewar rayuwa, sannan rayuwa ta bada zaman lafiya.

Idan ko ya kasance wani ko wasu daga cikin wannan jinsi zasu fifita bukatunsu fiye da na 'yan uwansu, to za a iya samun barkewar rashin jituwa, wanda shine zai yi sanadin barkewar rashin zaman lafiya a tsakanin wannan jinsin.

Dan Adam, wanda ya kasance mafi hikima a cikin sauran halittu,saboda wadansu ni'imomi da ubangiji ya yi musu. Shi kadai ne ya ke da tunanin ya noma abin da zai ci, don samun dorewar rayuwa, da nisanta daga galabaita da zai yi a yayin da ya nemi abinci ya rasa a muhallinsa. Daga cikin
abin da ya noma har da tunanin tanaji don gaba yayi amfani da shi.

Kasancewarsa mai hikima (Dan Adam) Allah ya bashi ikon sarrafa wasu daga cikin dabbobin gida, kamar su shanu, awakai, tumakai,rakuma da sauransu.

Daga cikinsu (Yan Adam) akwai wadanda suka zabi kasancewa da dabbobi a matsayin dukiya. Wanda hakan ya sa dole su ka kebe kasu daga cikin jama'a don su samu damar kula da dabbobinsu ta hanyar ciyar da su da shayar da su daga ciyayi da ganyayyaki. Hakan yasa wasu daga cikinsu ko noma ba sa samun damar yi, sai dai su sayi abinci daga manoma ko a kasuwa daga kudaden da suka samu a yayin da suka sayar da dabba ko nononta.

Wani lokacin sukan yi bulaguro daga wani yanki zuwa wani yanki don samarwa dabbobinsu abinci, musamman a lokacin rani ko damana su kan tashi daga yankin da bai da ni'ima zuwa yankin da ya ke da ni'ima.

Haka ta sa ake ganinsu a mutanen da ba su da takamaiman gari, kasa ko nashiya.


Kudancin Guri ya kasance mafi ni'ima idan aka hada shi da sauran yankuna na masarautar Hadejia. Domin albarkatu na daji, fadamu, gurin kiwo, kifi, tsuntsaye, da sauran albarkatun noma. Haka shine ya sa makiyaya suke da yawa a kudancin Guri.

Idan aka ce kudancin Guri ana nufin Gundumar Kadira ko muce (Kadira Distric) sun hada da manyan garu-ruwa irinsu Kadira, Abunabo, Musari, Gaduwa da Galdimari, Garin Mallam, Gagiya,Garmaguwa daSauransu.

Wannan yanki ya hada yaruka (kabilu) masu yawa sabanin sauran yankuna na Masarautar Hadejia. A wannan yanki za ka samu Mangawa, Gizimawa, Badawa, Fulani, Larawa, sai kuma Hausawa Auyakawa wadanda ba su da yawa.
Daga shekarar 1980 ne aka fara samun shigowar makiyaya (Fulani) a wannan yankin.

Fulanin da suka fara zuwa sun kasu kashi hudu, akwai:
Aborawa, Zamfarawa, Udawa, Fullo-Hadejia da Wuddurawa.

Wadanda su ka fara zuwa sune Aborawa. A wancan lokacin sukan zo a lokacin da ruwa ya gama cin dajin ciyawa ta fito sannan su yi kiwo. A wannan lokacin ya kasance a kwai wani ruwa da ake kiransa da suna Ruwan Dukuku; shi wannan ruwa idan ya zo ya kan mamaye dajin gaba daya, ya zamanto babu makiyaya. Hakan yake sa dole makiyayan su yi hijira zuwa kasar Yobe (Bade) don yin kiwo kafin ruwan ya janye su dawo.

Haka aka yi ta tafiya har Udawa su ka fara zuwa don yin kiwonsu a wannan daji kamar yadda Aborawa su ke yi. Su ko mazauna yankin su kanyi nomansu iri-iri, tare da sana'a ta kamun kifi.
Daga cikin Aborawa da Udawa aka samu Fulani mazauna wanda ake kira da Fullo-Hadejia. Sun kafa garuruwa irinsu; Safami, Maidashi, Matarar kano, Dolewa,Askandu da sauransu. Su kan zauna tare da dabbobinsu a rigagensu kuma su kan yi noma a guraren. A yayin da ruwan dukuku ya daina cin Dajin.

Daga nan sai zuwan zamfarawa.
Zamfarawa sun shigo kudancin Guri ne sakamakon fitintinu da ke yawan afkuwa a yankunansu na Zamfara.
Sakamakon haka ne ya sa su ka yi Hijira daga can suka zo kudancin Guri. Sun kasance ba mazauna guri kawai ba, sukan yawata zuwa sauran yankuna na Guri har sukan zuwa makwabta irinsu madaci, marma da sauran guraren da ake noman shinkafa don yin kiwo.

Haka zamantakewa ta ci gaba da kasancewa tsakanin wadannan al'ummah har zuwan Wuddurawa wadanda sukazo daga kasar Katagum da sauran yankunan jihar Bauchi. Domin kudancin Guri ya yi iyaka da Bauchi.

Zumunci tsakanin mazauna yankin da makiyaya (Fulani) ya ci gaba da kulluwa, sakamakon cudanya ta cinikayya da sauran al'amura na yau da kullum ya sa har auratayya ta fara kulluwa a tsakaninsu. Wannan ya sa duk auran da za a yi a Rigar fulani sai ka ga daya daga cikin mazauna yankin ya halarta haka suma fulanin.

Ku biyomu a kashi na biyu (2).
Hadejia A yau.