content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, November 24, 2013

TARIHIN HARUNA UJI DA WAKOKINSA. KASHI NA BIYU (2).

Hadejia A yau!



Littafin Muhd. Aji Hadejia.

A kashi na farko kunji cewa Alh. Haruna Uji ya ci gaba da kidan Gurmi gadan gadan.

A lokacin Gwamnan Kano Abdu Bako, sai yaji labarin Haruna Uji, sai yasa aka nemoshi domin yayi masa waka akan wayar da kan Al'umma akan Noma. Saboda haka Gwamna Abdu Bako sai ya hadawa Haruna Uji kayan wasa, kamar Amsa Kuwwa (Loud speaker) da Abin Magana wato (Microphone) da Injin wuta, wato Generator.
Wannan shine lokaci na farko da Haruna Uji ya fara waka da kayan wasa na zamani, kuma ya kama yin waka gadan gadan a matsayin sana'a.

Wakar da yayi a lokacin Itace wakar Noma. Anyi wakar ne da nufin wayar da kan Talakawa su koma Aikin gona.

3.0. WAKOKIN HARUNA UJI NA FARKO.

Alh. Haruna Uji yayi wakoki masu tarin yawa, kuma a cikin Jerin wakokinsa ga wasu daga cikin wakokin da ya fara yi.

*Wakar Naira da kwabo sabon kudi.

*Wakar Gudaliya.

*Wakar Shamuwa.

*Wakar Noma.

*Wakar Bakar Rama.
Wadannan sune kusan Shahararrun wakokin da ya fara yi.

3.1. Ajin Haruna Uji a tsakanin Mawakan baka.

A cikin wani Littafi da Ibrahim Yaro Yahya da Abba Rufa'i suka tsara, Mamuda Aminu ya kawo rabe-raben Mawakan baka zuwa rukunai kamar haka:
*Mawakan Sarakuna
*Mawakan 'yan mata
*Mawakan Jama'a
*Mawakan Mafarauta. Da sauransu.

Ya kawo misalin Mawakan Jama'a shine wanda zai yiwa Sarakuna da 'yan kasuwa da 'yan mata da Masu kudi da talakawa waka. Misali Mamman shata da Haruna Uji da sauransu.

Hakan ta nuna cewa Haruna Uji ya kasance a cikin Mawakan Jama'a, domin ya tabo duk abinda aka zayyana a sama. Wato yakan yiwa kowa waka.

3.1.1 Dangantakar Haruna Uji da Mawakan Baka.

Alh. Haruna Uji yana da kyakkyawar dangantaka da sauran 'yan uwansa mawakan baka, yana girmamasu shima suna girmama shi, sannan ya hori wasu suma sun zama shahararrun mawaka a kasar Hausa. Yayiwa wasu waka kuma shima wasu sunyi masa. A cikin mawakan da suka masa waka har da Alh. Mamman shata, kuma shima Haruna Uji yayi wa Alh. Garba sufa wakar Ta'aziyya bayan ya mutu.

3.1.2 Jerin wasu daga wakokin Haruna Uji.

Bayan rukunin wakokinsa na farko, ga wasu daga cikin wakokin da yayi.

*Wakar Dankabo
*Wakar Alh. Sani Likori
*Wakar Direban Chiyaman
*Wakar (Air vice marshal) Ibrahim Alpha
*Wakar (kwamishinan 'yan sanda) Daudu Gwalalo
*Wakar Haruna karamba
*Wakar Adamu Hassan Abunabo
*Wakar Ahmed Aruwa
*Wakar Asabe Madara
*Wakar Amadu koloji makwallah
*Wakar Bako Inusa kano
*Wakar Balaraba
*Wakar Jimmai Aljummah
*Wakar Birgediya Abdullahi shalin.
*Wakar Dankamasho
*Wakar Fulanin Jebbi fulato
*Wakar Idiyo Mai kayan Babur
*Wakar Kainuwa.

SAURAN WAKOKIN KU DUBA LITTAFIN.

Ka duba kashi na uku (3)

Thursday, November 21, 2013

TARIHIN HARUNA UJI. DA WAKOKINSA. KASHI NA DAYA (1).

Alh. Haruna Uji Hadejia.

Hadejia A yau! An haifi Alh. Haruna Uji A Unguwar Gandun sarki dake cikin garin Hadejia, a shekarar (1946). Sunan Mahaifinsa Mallam Ibrahim, Malami ne kuma shine Limamin Gandun sarki. Sunan Mahaifiyarsa Zainabu itama mutumiyar Unguwar ce. Anan ya tashi yayi wayo. Yana kimanin shekara shida mahaifinsa ya sakashi a makarantar Allo dake kofar gidansu, a gun wani Malami da ake kira Mallam Alhaji.

Haruna Uji ya shafe wajen shekaru uku yana wannan Makaranta a Gandun sarki, daga nan suka tashi da malaminsa zuwa garin Birniwa wanda take gabas da Hadejia, mai nisan kilo mita 45. Sun kwashe shekaru kamar biyu suna karatu da sauran Almajirai, anan Uji ya samu karatu mai dama.

Bayan nan suka bar Birniwa suka dawo Hadejia suka ci gaba da karatu a Gandun sarki. Wannan yasa ya samu karatu mai dama fiye da sauran yara musamman wadanda suka zauna a gida basu fita wani guri neman Ilmi ba. A wannan lokaci Mallam Alhaji yakan sa Uji ya kula da yara tare da koya musu karatu. Haruna Uji ya bar makarantar Allo yana dan shekara goma sha biyu, bayan ya samu karatu mai dama.
Hadejia A yau!

1.1, ASALIN INKIYAR HARUNA UJI..
Sunansa na yanka Haruna, yaci sunan wan Mahaifinsa, wato Mallam Haruna. Mallam Haruna mai sunan Uji yana da mata mai suna IYA KURA, Lokacin Uji yana karami matan kanin Babansa suna masa wasa suna ce masa Mijin Iya Kura, Mijin Iya Kura' A wannan Lokacin yara kannensa basu da baki, sai suke ce masa, Ujin Iya Kura. Maimakon Mijin Iya Kura. Wannan shine Asalin inda Haruna Uji ya samo Inkiyar Uji. Tun ana danganta sunan da Iya Kura har aka daina ake cewa Uji.

1.11, SIFFAR HARUNA UJI.
Haruna Uji baki ne, mai matsakaicin tsawo, yana da jiki matsakaici, ga farin hakora da bakin gashi, yana yawan barin gashin baki, ga magana (Idanu) haka kuma, ma'abocin barin suma ne, yana da Murya mai zaki da kauri kadan, kuma Gwanin Ado ne, da manyan kaya na sarauta. Kuma yakan saka 'yar shara, musamman lokacin zafi.

Alh. Haruna Uji mutum nd mai fara'a da kyauta, domin abin hannunsa bai rufe masa ido ba. Yana da raha sannan kuma bashi da wata nakasa a fili.

2.0, SANA'OIN HARUNA UJI..

2.1, Farauta da Noma.
Bayan Haruna Uji ya bar makarantar Allo, ya fara zuwa Daji da nufin farauta. Wadda itace sana'arsa ta farko, wanda ya fara, kuma ta sanyashi jarunta inda ya zama bashi da tsoro. Kuma a nan ne ya samu tambaya wato lakani na tsare kai.

Bayan farauta Haruna Uji Manomi ne, ya fara aikin gona ne da taya mahaifinsa, domin neman tabariki, wannan tasa yasan harkar noma wanda har yake noma gonar kansa.

2.2, Sana'ar Tukin Mota (Direba)
Alh. Haruna Uji yayi Sana'ar Tukin mota, wanda ya fara da Yaron mota a gun Mai gidansa wanda ake kira da suna Jibrin Dan Amingo. Jibrin Dan Amingo dan Asalin Danbatta ne ta Jihar Kano. Haruna Uji ya shafe shekaru da dama yana sana'ar yaron mota. Tukin mota ne sana'arsa ta farko da ta fara fitar dashi wani gari da nufin zama. Suna aiki ne tsakanin Kano da Hadejia.

Kuma a wannan lokacin suna zaune ne a garin kano a Tudun wada. Amma duk abinda ya taso a gida dashi akeyi, musamman aikin gona da bukukuwa da sauransu.

2.3, Sana'ar Waka.
Haruna Uji bai gaji waka ba, domin Mahaifinsa Malami ne, kuma ko a wakarsa ta Gurmi ba Haramun ba yana cewa:-
"Ni Haruna dan Mallam nake, Waka ta ba ta gado bace"

Saboda haka tun farko Haruna Uji ya riki waka ne a matsayin nishadi, domin ba wanda ya koya masa waka a matsayin Sana'a.

Haruna Uji ya fara ganin Gurmi ne a gun wani ma'aikacin titi wanda sukayi aiki a hanyar Mallam madori zuwa Gumel, wanda ake kira Dan-mato, a gun Dan-mato Uji ya fara ganin Gurmi da kidansa, shi Dan-mato yana kada Gurmi ne a yayinda suka samu hutun aiki. Yana kadawa yana waka, lokacin Uji yana Matashi, duk lokacinda sukaje kallon aiki sai su tsaya suna ganin kidan Gurmin Dan-mato, wannan tasa kidan Gurmi ya shiga ran Haruna Uji, idan ya dawo gida sai yakan nemi gwangwani da tsirkiya ya hada Gurmi yana kadawa. Har Dan-mato suka hada aikin hanya bai koyawa Uji Gurmi ba, sai dai Uji yana zuwa yana ganin yanda yake kadawa. Wannan tasa Uji ya dinga kwaikoyon Dan-mato tun bai iya ba har ya koya.

Wannan yasa idan yana gurmi yara sukan tsaya suna ji da kallonsa, Wannan shine Asalin koyon Gurmin Haruna Uji. Daga nan sai ya fara tunanin ya samu sanda, da lilo da butar Duma da fatar Damo da Zobe domin ya hada bubban Gurmi.

Farkon lokacinda ya fara Gurmi idan an bashi abu baya karba, don yanayi ne saboda Nishadi. Kuma sau da yawa idan ya fito hira ko ana wani biki na samari da 'yan mata, yakan kada Gurminsa yana waka, samari da 'yan mata suna kallo.

A wancan lokacin yana Gurmi yana aikin Mota, wannan yasa ya fara Gurmi a garuruwa daban daban na Arewacin Nigeria.

Daga nan Uji ya bar tukin mota ya koma kidan Gurmi Kuma ya nemi mataimaka don sunayi su biyu.

Karashe a kashi na 2.
Littafin Muhd. Aji Hadejia