"" /> HADEJIA A YAU!: Feb 12, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, February 12, 2012

WAKAR MAIJIDDA DAGA M. AMADU DANMATAWALLE

AMSHI - Haka nan ne malam Ahmadu masu fasaha kanda gwamna kai aka yiwa firimiya.


1, Bismillah waka nai nufi tarihin malam amadu na hadejia wanda ake fadi.


2, A watan august ran litinin kwana daya nai wakar nana tarihin mai girkin dina.


3, Zamanin nan a Hadejia shi ba sarkin samari bane Allah ne yai masa martaba.


4, 'ya'yan sarki da na hakimai talakawa 'ya'yan tajirai a gidansa ake girkin dina.


5, zamanin nan a Hadejia abinda ya shirya babu mai rushewa malam amadu.


6, sai malam yai musu shawara aduba budurwa mai mukami Hadejia ayi mata gwamnati.


7, samari sai sukace masa a dallah asa mai jidda domin tafi budurwar zamani.


8, gurinda take ban al'ajab bata fushi mai jidda bata da girman kai kuma ga ladab.


9, in tana zance fa murmushi ga karamar murya a gunta kamar 'yan matan india.


10, sunan mai jidda hawa'u gwamnan 'yan mata a hadejia.

Allah sarki duniya!