HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Sunday, December 16, 2012
SABON GWAMNAN KADUNA DA TARIHIN RAYUWAR SA.
Free Music A yau Lahdi Za'a rantsar da Alh. Mukhtar Ramadan yero a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna! An haifi Muktar Ramalan Yero a ranar 1 ga Mayun shekarar 1968 a birnin Zazzau. Ya halarci makarantar Firamare ta karamar hukumar wadda ke Unguwar Kaura daga shekarun 1974 zuwa 1980. Ya shiga ta Sakandire dake Ikara daga shekarun 1980 zuwa 1985, sannan ya wuce Cibiyar Koyon Mulki wadda ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, inda ya samu takardar shaidar digiri na farko da na biyu, wato Masters, a fannin Akanta daga 1986 zuwa 1991. Ya wuce Kwalejin Koyon Aikin Akanta ta Jos. Muktar ya yi aikin NYSC a jihar Ogun, a hukumar saye-sayen Kayayyaki masu muhimmanci a shekarar 1991. Da ya karasa, sai ya fara aiki sashen Kudi na Jami’ar Ahmadu Bello, a matsayin mai kula da hada-hadar sashen da bankuna. Bayan shekaru biyu, sai ya koma bankin Universal a matsayin mai kula da asusun masu hudda da bankin daga shekarun 1993 zuwa 1997. A wannan bankin saida ya kai matsayin Babban Akantan bankin. A shekarar 1997 ne ya mayar da aikinsa zuwa Kamfanin Nalado Nigeria Limited, kamfanin Namadi Sambo a matsayin Babban Akanta, daga baya ya zama Shugaban Ma’aikata, Shugaban Sashen Kudade da Shugabancin Ma’aikata. Cikin hukuncin Ubangiji, da Namadi Sambo ya zama gwamnan jihar Kaduna a 2007, sai ya nada shi kwamishinan ma’aikatar kudi, mukamin da ya rika shekaru uku. Shi memba ne na kungiyoyi da dama, daga cikinsu akwai Kungiyar Akantoci ta Kasa da Cibiyar Shugabannin Kamfanoni da ta Akantocin Kididdiga da Riritawa Kudade da ta Masu ilmin fasaha da Injiniyoyi da sauransu. Yana da aure da ‘ya‘ya, kuma mutum ne mai sha’awar karance-karance da hawan dawaki da sauraren kade-kade da kuma yin mu’amala da mutane, shi ya sanya yake da tausayi. Wani abin lura shi ne, Muktar Yero ya baiwa marada kunya, inda ya gudanar da ayyukan Ma’aikatar Kudin jihar Kaduna cikin rikon amanar da aka san shi da shi, a duk wuraren da ya yi ayyuka a baya. Saboda haka ne, aka ba shi mukamin mataimakin gwamna a lokacin da Shugaba Namadi Sambo ya zama Mataimakin Shugaban Kasa a 2010. Bayan Mutuwar Gwamna patrick Yakowa Ranar Asabat 15/12/2012. sakamakon Hatsarin Jirgin sama a yau. Alh. Muktar Yero ya zama Gwamnan Jihar Kaduna. An rantsar dashi ranar Lahdi 16/12/2012. ALLAH YA TAYAKA RIKO.
Subscribe to:
Posts (Atom)