"" /> HADEJIA A YAU!: Apr 2, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Monday, April 2, 2012

TARIHIN SARAUTAR FULANI A HADEJIA! A TAKAICE.

Image Hosted by ImageTitan.com HADEJIA A YAU!

JIYA NA KAWO MUKU TAKAICACCEN TARIHIN HADEJIA DA DALILIN KAFUWARTA.

TARIHIN FULANI- BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM.
Kamar yanda na fada a baya Sarkin Hadejia Na sarakunan Habe shi ya nada Umaru a matsayin sarkin fulanin Hadejia, To su fulani sun taso ne daga Gabas da Machina akan Hanyarsu ta yin kiwo, ko da sukazo Hadejia sai suka tadda Garin akwai albarkar kiwo da noma. Hakan ce tasa suka nemi izni a basu gurinda zasu zauna A zamanin sarki Abubakar Sarki na karshe a sarautar HABE.

Kuma suna tafe ne a karkashin jagorancin HARDO ABDURE DAN JAMDOJI MACHINA. A lokacin da Umaru yake a matsayin sarkin fulanin Hadejia sai ya samu labarin jihadin da SHEHU USMANU DAN FODIYO yakeyi hakan tasa ya tashi 'yan-uwansa biyu(2) suje suyi mubaya'a a gun SHEHU.

Wato SAMBO DA LARAIMA kuma hakan sukayi Inda shehu ya basu Tutar jaddada Addinin Musulunci. Kuma ya umarci SAMBO ya tsaya a HADEJIA Shi kuma LARAIMA a MARMA. Saboda can akwai dauloli suma masu zaman kansu yayi kokarin Hadesu karkashin Daula guda daya. kamar DAWA FAGI GATURWA DA MARMA.

Shi kuma SAMBO yaci gaba da jaddada Addinin Musulunci a HADEJIA DA AUYO DA SAURAN DAULOLIN SARAKUNAN HABE A karkashin jagorancin Dan-uwansa Umaru.

Bayan rasuwar sarkin fulani Umaru SAMBO yaci gaba da jaddada Addinin Musulunci har saida suka kawar da SARAKUNAN HABE. Amma ba yaki akayi ba Sai suka Koma Fantai anan sukaci gaba da rayuwa. (wato akwai wata tsangaya a kusa da gidan Labaran fantai nan ne suka zauna) wadansu kuma suka zauna a Dalla (akwai wata duriya a dallah har zuwa Library anan suka zauna).
Sarakunan fulani sun karbi mulkin Kasar Hadejia a karkashinDaular Usmaniyya.

ZAN KAWO MUKU TSARE TSAREN SARAUTA DA KUMA HAKIMAN WAJEN KASAR HADEJIA A LOKACIN SARKIN FULANIN HADEJIA MALAM SAMBO. HADEJIA A YAU!

HADEJIA PART ONE! RANGADIN KASAR HADEJIA.

HADEJIA A YAU!

RANAR TALATA 21/DECEMBER/2004 MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALH. ADAMU ABUBAKAR YA FARA RANGADI DOMIN WAYAR WA DA AL'UMMAR MASARAUTAR HADEJIA KAI A KAN KIDAYA (POPULATION).
Kuma ya fara da Gundumar Kafin Hausa! Kasar Dan-amar.

Ranar Laraba 22/12/2004 Yaje Bulangu Kasar Wambai.

Ranar Alhamis 23/12/2004 Yaje Jabo Kasar Dan kadai.

Ranar Juma'a 24/12/2004 Mai martaba ya huta ba'aje ko ina ba.

Ranar Asabat 25/12/2004 Ma baije ko ina ba. A RANAR YA NADA DAN-BURAN ALH. ALIYU BAFFALE. Kuma Ranar Lahdi ma Hutu akayi.

Ranar Litinin 27/12/2004 Ya nufi Sarawa Kasar Barden Kerarriya.

Ranar Laraba 29/12/2004 Ya tafi Kwatalo Kasar Sarkin Kudu Alh. Adamu Haruna. Allah ya kyauta kwanciya.

Ranar Lahdi 2/january/2005 Yaje Ruba Kasar Sarkin Sudan.

Ranar Talata 4/01/2005 Yaje Duma-dumin kyaure Kasar Dan maje.

Ranar Alhamis 6/01/2005 Yaje Duma-dumin Toka Kasar Dan makwayo.

AN GAMA DA KASAR KAFIN HAUSA.

KASAR GURI

Ranar Talata 11/01/2005 Mai martaba Sarki ya nufi Guri Kasar Sarkin Shanu.

Ranar Alhamis 13/01/2005 Yaje Kadira Kasar Dan'Isah.

DAGA NAN MAI MARTABA SARKIN HADEJIA ALH. ADAMU ABUBAKAR SAI YA DAKATA SAI BAYAN SALLAR LAYYA.

ZAN KAWO MUKU KARASHEN RANGADIN. KU DUBA HADEJIA PART TWO.

HADEJIA A YAU!