HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Friday, March 15, 2013
KUDUBAR JUMA'A DAGA BUBBAN MASALLACIN HADEJIA.
HADEJIA A YAU. A yau malam Na'ibi yi mana kudubace mai taken :-
JIN TSORO DAGA AZABAR ALLAH S.W.T.
Fassara:- Ibrahim Umar.
Yan uwana musulmai Malam ya ja hankalinmune game da jin tsoro
daga azabar Allah Mai Girma da Daukaka domin kamun ubangiji ya kasance mai tsananine. Yan uwana kullun mu cigaba da kasancewa daga cikin bayin Allah Madaukaki masu da'a tare da jin tsoron azabarsa.
Kada mu kasance daga bayi azzalumai masu zalintar
kansu wajen keta Abubuwan da musulunci ya hana.
Manzon Allah S.A.W yana cewa "kuji tsoran wuta ko da da tsagin dabino ne"
Ma'ana koda abin da zakayi sadaka dashi kamar tsagin dabinone don ka bayar dashi ka
kare kanka daga wuta to kayi kokari ka bayar.
ALLAHUMMA INNA NARJU RAHMATIKA WA NAKHAFU AZABAK. ya Allah SWT ka karemu
daga azabar wuta amin.
Subscribe to:
Posts (Atom)