HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Thursday, March 7, 2013
HUKUNCIN GADO DA MASU CIN GADO. KASHI NA DAYA (1)
HADEJIA A YAU!
Assalamu Alaikum! Wannan babi zai yi bayani
a kan masu
gado a cikin maza, da masu gado a cikin
mata. Sannan babin zai yi bayani akan irin
bambancin darajojin magada.
(1) MASU GADO A CIKIN MAZA
Masu gado daga cikin maza, su goma (10) ne!
Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su,
su goma sha biyar ne, (15) kamar haka:-
1. Da (Na tsatso)
2. Dan da, (Jika har zuwa tattaba kunnansa)
3. Uba (Na ciki)
4. Kaka namiji (Na wajan uba, har zuwa
Sama)
5. Dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba daya)
6. Dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa daban)
7. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya, uba
daban)
8. Dan dan'uwa shakiki (Na uwa daya, uba
daya)
9. Dan dan'uwa li'abi (Na uba daya, uwa
Daban)
10. Kanin uba, shakiki (Na uwa daya, uba
daya)
11. Kanin uba li'abi (Na uba daya, uwa
daban)
12. Dan dan kanin uba, shakiki (Na uwa
daya uba daya)
13. Dan dan kanen uba, li'abi (Na uba daya
uwa daban)
14. Miji.
15. Ubangijin bawa. Hadejia A yau!
MASU GADO A CIKIN MATA
Masu gado a cikin mata su bakwai ne (7)
Ga jimlarsu, amma idan aka rarraba su, su
goma ne, (10) kamar haka:-
1. 'Ya ko Diya (Ta tsatso)
2. 'Yar da, (Na tsatso duk yadda ya yi nisa)
3. Uwa
4. Kaka mace (Ta wajan uba)
5. Kaka mace (Ta wajan uwa)
6. 'Yar'uwa shakikiya (Ta uwa daya, uba
daya)
7. 'Yar'uwa, li'abiya (Ta uba daya, uwa
daban)
8. 'Yar'uwa, li'ummiya (Ta uwa daya, uba
daban)
9. Matar Aure
10. Uwargijiyar bawa ko baiwa.
Hadejia A yau!
MASU GADO DARAJARSU TANA DA BAMBANCI
DA JUNA
Masu gado suna da bambanci da
junansu. Ma'ana gado ba abu ba ne wanda
za a ce a raba shi daidai, a tsakanin magada.
Dole ne a raba shi yadda Allah Madaukakin
Sarki Ya raba shi cikin hikimarSa.
A rabon gado wani ya fi wani rabo. Wani
kuma ba ya da rabo in ga wani. Wani kuwa
zai tashi daga wani rabo ya koma ga wani
rabo, saboda samun wani tare da shi. Wani
kuma zai kada wani; wani sauran dukiya
yake kwashewa. Saboda haka za mu bi su
dalla-dalla, domin mu yi bayaninsu, in sha
Allahu.
MASU FARALI
Za mu fa ra da bayanin abin da ake nufi
da masu farali. Masu farali su ne wadanda
Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci rabonsu a
cikin Alkur'ani Mai girma. wadannan su ne
kamar haka:
1. 'Ya (Ta tsatso)
2. 'Yar da (Na tsatso)
3. Uwa
4. Uwar uwa
5. Uwar uba
6. Dan'uwa li'ummi (Na uwa daya)
7. 'Yar'uwa li'ummiya, (Ta uwa daya)
8. Miji.
9. Mata.
MASU ASIBCI
Za mu fara bayani a kan abin da ake
nufi da asibi. Asibi shi ne wanda idan a ka
zo wajan rabon gado, zai tsaya har a fitar
wa masu farali, farilinsu, sannan abin da ya
yi saura ya kwashe, za mu jera su kamar
haka:
1. Da (Na tsatso)
2. Dan da (Na tsatso)
3. Dan'uwa shakiki, (Uwa daya uba daya)
4. Dan'uwa li'abi, (Na uba daya)
5. Dan dan dan'uwa shakiki (Uwa daya uba
daya)
6. Dan dan dan'uwa li'abi, (Na wajan uba)
7. Kanin uba shakiki (Uwa daya uba daya)
8. Kanin uba li'abi, (Uba daya uwa daban)
9. Dan kanin uba shakiki, (Uwa daya uba
daya)
10. Dan kanin uba li'abi, (Uba daya uwa
daban)
11. Wanda ya 'yanta bawansa.
12. Wadda ta 'yanta bawanta.
MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU
KARBI FARALI
Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani
lokaci kuma su amshi farali, su ne kamar
haka:
1. 'Yar'uwa shakikiya (Uwa daya
uba daya)
2. 'Yar'uwa li'abiya (Uba daya uwa
daban-daban)
MASU ASIBCI WANI LOKACI WANI LOKACI SU
KARBI FARALI WANI LOKACI SU HADA DUK
Wadanda ke yin asibci wani lokaci, wani
lokaci kuma su amshi farali, wani lokacin
kuma duka gaba daya, da asibci da farali.
Sune:-
1. Uba.
2. Kaka namiji.
MASU GADON NISFI
Kafin mu yi bayanin masu gadon nisfi, ya
kamata mu san mene ne nisfi?
Nisfi kalmace ta Larabci. Ma'anarta rabi
(1/2). Idan an raba wani abu biyu, kowane
daya daga cikinsu ya zama nisifi ke nan.
Masu gadon nisfi (Rabi), su biyar ne
kamar haka:
1. Miji.
2. 'Ya (Ta tsatso)
3. 'Yar da (Na tsatso)
4. 'Yar'uwa (Ta uwa daya, uba daya)
5. 'Yar'uwa (Ta uba daya, uwa daban)
Wadannan su ne masu nisifi. Za mu bisu
daya bayan daya; mu yi bayanin su dalla-
dalla, ta hanyar da za a fahimta, in sha
Allahu, domin ko wanensu yana da sharuda.
Alhamdulillahi.
Subscribe to:
Posts (Atom)