HADEJIA A YAU!
Wannan dandali zai kawo muku tarihin unguwannin da suke cikin Garin Hadejia. Kuma zamu fara da...
UNGUWAR FANTAI- fantai tana daya daga cikin unguwanni masu tarihi a Hadejia, wato lokacin da aka jaddada Addinin musulunci akwai Sarkin Hadejia na wancan lokacin wato sarkin Habe Abubakar, basu yarda sunbi Daular Usman Dan fodiyo ba. Sai suka tare unguwar fantai wato gabas da Hadejia sukaci gaba da zama anan. A lokacin tana da nisa da cikin garin Hadejia. Kuma ba'ayi yaki dasu ba.