HADEJIA A YAU!
TARIHIN SARKIN ZAZZAU JA'AFARU....1936-1959.
Na rubuta wannan labari nawa don in bayyana godiya ta ga Ubangiji, kuma mutane kuga tsaunukan da na taka har na kawo ga wannan matsayi.
A cikin shekarar 1911, watau ina da shekara Ashirin da hudu (24) da haihuwa kenan, aka aika dani makarantar Dan-Hausa dake Kano. Na shekara guda acan na dawo gida. rannan ina zaune sai ga Shehu Baloha masinjan Joji, yace wai Joji yana kira na a Bariki. bayan naje sai naga Razdan ya dauki lambar Masinja ya lika mini a riga ta, yace "Yau ka zama Masinja" sai na durkusa nayi godiya. aka yanka mini albashin sule Talatin (30).
Bayan nayi shekara uku ina wannan aikin sai rannan na roki Razdan ya maida ni makarantar Turawa ta Zariya, in rika koyawa 'yan makaranta Larabci.
Razdan yace "A'a wannan aiki bazai yi maka ba" saboda haka ya kai Magatakardar sa M. Kwasau can, Malami guda kuma Malam Umaru ya maida shi aikin Shanu, nikuwa aka game mini aikin su duka nake karbar Sule saba'in (70).
Ina cikin wannan aiki a cikin shekarar 1918 sai wani Hakimi na Zangon Katab ya taba kudin Jangali, aka fishe shi, ashe Allah ya nufa Sarautar a kaina zata fada, aka nada ni Hakimcin Zangon Kataf na koma can.
Sa'ad da nake Hakimi a wannan Kasa, naga abubuwan Tashin hankali guda biyu. wata shekara ina karbar Haraji sai Arnan Unguwar Gayya suka yi mini Tawaye. ina zuwa kauyen sai naji sun dauki kuwwa, nan da nan baka suka taru makil, kowa daga kwari sai baka a hannun sa, sai kayi tsammani wani abu ne yasa wannan bore. Dalili kuwa wai sun gaji da biyan Haraji ne kawai! Abu kamar wasa sai wani Arne wai shi Gankwan ya dana kibiya, yako duban ya sako mini ita. Sai ya kuskure mini ya samu Sarkin fada na a kafada. Yara na daga ganin haka sai suka yi kazam akan Arna! da Arnan nan suka ga bamu da Alamar tsoro sai suka bada baya, suka shige Kurmi gidan Tsafi.
Muka shiga garin muka tarar ba kowa, duk sun gudu mazan su da matan su. Na kira Sarakunan su da basu cikin tawayen, na gaya musu su lallashi mutanen su su dawo, babu komai. Washegari ni kuwa na yi zuwa Mabushi. A can na samu labari sun dawo sai shi Gankwan da ya harbi Sarkin fada na shine ba'a gani ba. Na aika ga Sarkin Zazzau Dalhatu da abinda ya faru duka, yace in kara matsawa kan neman Gankwan. Amma Ina? Ai har yau ba'a same shi ba, kamar an biya bashi dashi. Sarkin fada na kwanan sa wajen Arba'in a Mabushi yana jinyar daffin kibiyar nan.
Kai Arnan Zangon Katab a lokacin suna da wuyar sha'ani wajen al'amarin Haraji! Dubi wata shekara kuma da ni da wani Joji muna kama Awakin wadanda basu biya Haraji ba a Zankuwa, ba sai muka kama na wani wadda ya biya ba? sai gashi faram faram da matar sa suka zo suka durkusa suka ce mana "Wadannan Awaki namu ne, mu kuwa mun biya Haraji" Joji yace "To mu dai mun kama Awaki. Watau Makwafcin ka ya biya kenan, in ya samu kudi sai ya biya ka."
Da suka koma gida sai matar sa ta shiga zuga mijin ta na cewa "Allah wadan ka! Ashe dai kai ba Namiji bane? yaya don tsoron Sarauta zamu yarda a kwace mana Awaki? Ina ruwan mu da Makwafcin mu da zamu biya masa Haraji? Kai in baka dauki Kwari da baka ka tarad da Baturen nan ba, ina sa Wuta in kone su in kuma rabu da kai." Daga nan sai maigida ya dauki Kwari da baka ya tanka, 'ya'yan sa kuwa kowa ya dauko tasa, suka nufo wajen mu zasu tada Jihadi. Da na hango shi sai na daka masa tsawa sai ya yada Baka sai yazo ya fadi gabanmu yana haki. Na lallashe shi, na bashi magana sa'an nan ya koma. Ka ji tashin hankali da na hadu dasu lokacin ina Hakimcin Zangon Katab.
Na samu wannan Sarauta zamanin Sarkin Zazzau Aliyu ne, bayan shi aka nada Dalhatu. Daga nan sai Sarkin Zazzau Ibrahim ya kama Sarauta, shi kuma ranar 31/1/1937 ya rasu. Allah yaji kan su Amin. Bayan rasuwar Sarkin Zazzau Ibrahim, ina Hakimci a Zangon Katab sai ga waya ana nema na a Zariya, don Gwamna da manyan mashawartan Zazzau sun yarda in zama Sarki a shekarar 1936.
Madogara... Gaskiya Ta fi Kwabo ta 17. 1939.
Daga nan sai na koma Zazzau da zama, muna rokon Allah da ya taimake mu rikawa Amin.
Sarkin Zazzau Ja'afaru shine dan M. Isyaku Sarkin Zazzau, dan Sarkin Zazzau Abdu dan Hammada. Allah ya masa rahma.