SARKIN YAKIN SARKIN MUSULMI!
Kamar yadda kuka gani A sama Zamu kawo muku Tarihin Zuwan Sarkin Marma Muhammadu Madarumfa. Iyakar sokoto da Niger da kuma yakin da akayi tsakanin Muhammadu da Gobirawan Madarumfa, akan kogin da ya raba Niger da Nigeria, kusa da Jibya. A zamanin Sarkin Musulmi Abubakar Atiku Na Biyu Sarkin Hadejia Muhammadu yaje Sokoto dashi da mutanensa lokacin yana Sarkkn Marma, koda yaje sai ya iske ana yaki tsakanin rundunar Sarkin Musulmi da kuma Gobirawan Madarumfa. Yaki yayi tsanani gashi Dawakai da mutanen Sarkin Musulmi suna jin Kishi su kuwa Gobirawa sun tsare Ruwa, Koda Sarkin Hadejia Muhammadu yaga haka sai ya nemi izni ga Sarkin Musulmi don a bashi dama dashi da mutanensa su shiga wannan yakin. Bayan an bashi izni sai yacewa Sakkwatawa yanzu zaku sha Ruwa koda jini ya gurbatashi, haka kuwa akayi Sarkin Hadejia da jama'a tasa suka shiga sukayi ta dauki ba dadi da Gobirawan Madarumfa har saida sukaci galaba a kansu, suka kore na korewa suka kashe na kashewa suka kama wasu a mazaunin Bayi. Bayan an gama yaki Sarkin Hadejia Muhammadu yazo yayi gaisuwa ga Sarkin Musulmi yace masa Ruwa ya samu aje asha a baiwa Dawakai. Bayan an koma Sokoto sai Sarkin Musulmi ya nada Sarkin Hadejia Muhammadu a matsayin Sarkin yakin Sarkin Musulmi saboda irin gudunmawa da ya bada.
Bayan nadinsa a matsayin Sarkin yakin Sarkin Musulmi sai yayi Sallama da Sakkwatawa suka rakoshi har kan iyaka tare da jama'arsa suka kamo hanya suka dawo Hadejia. Kafin Sarkin Hadejia ya iso gida har labari ya samu Hadejiawa cewa an nada Muhammadu Sarkin yakin Daular Usmaniyya, dan haka sai jarumai da mahaya sukayi shjri sukazo suka taryeshi.
A gaba zamu baku labarin shigowarsa Hadejia da yadda aka kaiwa Sarkin Hadejia Haru Bubba Labarin Muhammadu. Harda Asalin Jafi da ake Ran sallah A kusa da Masallacin Juma'a. Muhammadu na Allah Ruwan kogi Tafi sannu sannu Wanda yayi wargi Ya Halaka. Giwa ta gama da Masu Karfi Ta wuce.