"" /> HADEJIA A YAU!: Oct 30, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, October 30, 2012

TAKAICACCEN TARIHIN LIMAMIN HADEJIA M. YUSUF IMAM.

Hadejia A yau.
Hadejia A yau. HADEJIA A YAU!Hadejia A yau. A ci gaba da kawo muku Tarihin wadanda suka bada Gudunmawa a Hadejia, yau Zamu baku takaitaccen Tarihin Bubban Limamin Hadejia MALLAM YUSUF ABDURRAHMAN. Muna farawa da sunan Allah wanda da ikonsane komai ya kasance da kuma Abinda zaya kasance! Tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Allah (s.a.w.) wanda ka aiko dashi bil’haqqi da Gaskiya.

An haifi Limamin Hadejia M. Yusuf Imam a unguwar Rumfa da ke cikin Garin Hadejia, a shekarar 10/1/1980, kuma ya fara karatun Addini a Gurin Mahaifinsa M.Abdurrahman Ya’u, bayan ya kai shekaru bakwai (7) shi da ‘yan uwansa an kaisu Makarantar Allo a unguwar Yayari, wato makarantar Mallam Muhammadu Dan birni. Bayan yakai shekaru Ashirin (20) ya koma Makarantar Malam Garba Dake ‘Yankoli, kuma anan ne ya sauke Alqur’ani mai tsarki.

A shekarar 1998 Malam Yusuf ya samu nasarar shiga Makarantar koyon karatun Addini ta Hadejia (S.A.I.S.) inda kuma anan ne ya sake sauke Alqur’ani a Ruwayar Hafsi. Tare da Na’ibinsa M. Habibu Aminu.

A shekarar 2002 Malam Yusuf ya samu nasarar shiga Makarantar Horar da Malamai dake Gumel (ATC.GUMEL) Inda ya samu saidar N.C.E. A bangaren Arabic. Kuma ya samu aikin koyarwa a ma’aikatar Ilmi dake Auyo, bayan shekaru ya dawo yaci gaba da koyarwa a Makarantar S.A.I.S. Dake garin Hadejia.

Malam Yusuf yayi karatun Ilmin Addini a gurin Malamai da dama kamar M. Usman danyaro, Malam Tela Majema, M. Akilu, M. Aminu Ibrahim Daurawa da sauran Malamai.

A ranar Asabat 5/1/2002 Malam Yusuf Imam ya fara bada Ilmi a soron Gidansu, Inda ya fara da Dalibai kamar haka:-

Mohd. Abubakar Malam namu, Ismaila A sabo, Baffale Muhd. Furdi (Baffaliya), Idris Baffa (Liyan), Yusuf abdulkadir wakili, da Adamu A Amar.

Ranar 12/feb./2006 an gayyaceshi da ya gabatar da Maudhu’i a masallacin Juma’a, Inda kuma yayi fadakarwa akan Alamomin tashin Alqiyamah. Wanda kuma wannan fadakarwa ta jawo hankalin mutane akan ranar tsayuwa,wato Alqiyamah.

A ranar Talata 29/Aug./2006 Malam Yusuf ya fara jan Sallah a masallacin juma’a. Sakamakon Rashin lafiyar Limamin wancan lokacin Malam Shehu Qassim.

Haka kuma ranar juma’a, 8/ september/2006 Malam Yusuf ya fara fassara Huduba a Masallacin Juma’a Kuma a wannan lokacine aka tabbatar dashi Na’ibi na biyu.

Ranar Litinin 2/june/2008 Allah yayiwa Limamin Hadejia rasuwa Malam shehu Qassim, kuma bayan mutuwarsa ne Ranar Litinin 23/june/2006 aka tabbatarwa Malam Yusuf Imam ya zama Bubban Limamin Hadejia. Da misalin karfe tara (9:m) na dare.

A Ranar Juma’a 27/June/2008 Mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Adamu A. Maje ya nada Malam yusuf a Matsayin Bubban Limamin Hadejia. Da misalin karfe (10:am) na safe. Sannan a ranar ya fara sallar Juma’a Inda kuma yayi Huduba mai daidaita hankali da kuma tabbatar da Ikon Allah shine abinda za’abi a zauna lafiya.

A Gudunmawar da Mallam Yusuf Imam ya bayar a cikin Garin Hadejia ta bangaren Ilmi, Harda karatuka da littatafai da ya karantar A masallacin Juma’a. Kamar:- 1,UMDATUL-AHKAM 2, MUWADDA MALIK 3, LU’U-LU’U WAL MARJAN, IHYA-USSUNNAH Da sauran Littatafai. Da kuma Lecture da yayi a Gurare da dama a cikin garin Hadejia da kewaye.

A watan August na wannan shekara Malam Yusuf ya tafi kasar Sudan Domin Karo Ilmi. Muna Addu’a ga Malam Allah ya haskaka zuciyarsa ya kyautata jinsa da Ganinsa ya kara masa Ilmi da Basira. Ameen.

Allahumma badi’ussamawati wal’ardhi, zaljalali wal’Ikrami, wal-izzatullati la tarami, As’aluka ya Allahu, ya rahman bi jalalika, wa nuru wajhika, antalzim qalbi hifzu kitabuka, kama allamtani, warzuqni antilawahu alannahwullazi yardhika anni. Ameen. Hadejia A yau. HADEJIA A YAU!