Hadejia A yau! Assalamu Alaikum! Godiya ta tabbata Ga Allah
wanda ya Halicci Mutum da Aljannu dan mu bauta masa.
Tsira da Aminci su tabbata ga
shugabanmu Annabi Muhammadu, wanda Allah ya Aikoshi da Alqur'ani da Salloli guda Biyar (5).
Bayan haka Al-ummar Musulmi Musulunci
yana da tsare tsare wanda Idan ka bisu zaka
rabauta! Hakika Tsayuwa a bayan Liman a
yayinda ake sallah ba na kowa bane na
Masana ne! Domin Idan Liman yayi kuskure a
sallah sune suka san Irin abinda zasu fada
masa dan ya gyara.
Idan wanda baida Ilmi ya tsaya bayan Liman
kuma aka samu akasi Liman yayi Kuskure
kana tunanin zai iya gyara masa? Bazai iya ba,
saidai ya sake batawa.
Manzo (s.a.w.) yana cewa :- An sanya muku
Liman dan kuyi koyi dashi, Idan yayi Ruku'i
kuyi Ruku'i, Idan yayi Sujudi kuyi sujudi.
Danme zakayi abinda Liman baiyi ba?
ZAN BAKU LABARIN MUJRIMI...
Mujrimi wani Balaraben Kauye ne! Yazo Birni
kuma Sallah ta Magriba ta kamashi sai yazo
yayi Alwala ya tsaya a bayan Liman. Sai akayi
Sa'a Liman ya karanto Ayar nan da take
cewa:-
Alam Nukhliqil Awwalyn? (Fassara) shin
bakuga yadda muka Halakarda Mutanen farko
ba?
Sai Balaraben kauye ya fice daga sahun farko
ya koma sahu na biyu.
Sai Liman ya sake karanta Summa
Nutbi'uhumul-Akhiriyn.
(fassara) sannan haka muka aikata ga
mutanen baya.
Sai Balaraben kauye ya koma sahun Karshe.
Sai Liman ya kara karanta Kazalika Naf'alu bil-
Mujrimiyn.
(fassara) sannan haka Muka aikata ga
Mujrimai.
Sai Balaraben kauye ya fita a guje yace Ni ake
Nema. Domin yaji an ambaci kamar sunansa.
To dan Allah me ya janyo haka? Allah yasa mu
Gane.