"" /> HADEJIA A YAU!: Sep 28, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, September 28, 2012

MUTUWAR SARKIN HADEJIA BUHARI

HADEJIA A YAU!
Bayan Sarkin Hadejia Buhari ya Gama
yake yake kamar yakin Takoko, gamon
kafur da sauransu! Sai ya yanke
shawarar ya fadada Kasar Hadejia daga
Gabas. Kuma a lokacin babu wani Dansa
da ya taso wanda zai bashi wata
sarauta bubba. Dan haka ya Nada
kaninsa Sarkiyo a matsayin Chiroman
Hadejia a shekarar 1863. Da nufin ya
zama Magajinsa, saboda Dansa Umaru
shekarunsa Goma sha Takwas (18).
Buhari yayi Tunanin ya Masa sarauta mai
Girma a Kasar Hadejia, dan haka yayi
kokarin ya masa sarautar Sarkin Auyo,
bayanda ya Kashe Nalara sarkin Auyo
ba'a nada kowa ba! Dan haka yaso ya
nada Umaru a matsayin Sarkin Auyo.
Wato ya kasance ya gajeshi bayan ya
Mutu.
Da wannan kudiri da yake ransa, Buhari
yayi kokarin ya cinye Gogaram (Bedde)
da Yaki don ya Nada kaninsa Chiroma
Sarkiyo a matsayin Sarkin garin. Kuma
dukda yayi haka zuciyarsa daya, wasu
daga cikin 'yan-uwansa sai suka yi
kokarin su baza masa abinda ya tsara!
Dan haka wani daga ciki 'yan-uwan
Buhari sai ya fara yada jita-jita a
tsakanin fadawan Buhari cewa yana so
ne ya kaisu a kashe su don ya cimma
wata manufarsa, su kuma fadawa sai
suka ga Dangantakarsa da Buhari bazai
fadi karya ba sai suka yarda da
maganarsa.
Dan haka fadawa sai suka fara shawara
a junansu ba tare da Sarki Buhari ko
wani ya sani ba, don su yiwa Buhari
tawaye a gun yakin, kuma duk suka
amince da hakan. Bayan kwanaki sai
Buhari ya sanar da fadawa cewa zasuje
suci Gogaram da yaki, amma bai san an
warware masa shirinsa ba. Aka saka
rana Buhari ya jagoranci mayakan
Hadejia don su ci Gogaram da yaki,
sarkin Hadejia Buhari ya shiga Gogaram
ta kofar Garin yamma amma mayakan
Buhari kamar su Sarkin Arewa Tatagana
da Sarkin yaki Jaji da sauran fadawa sai
suka tsaya suka ki su bi Buhari, ko da
ganin Haka sai Buhari ya shiga garin
suka fara dauki ba dadi da Mayakan
Sarkin Gogaram DAN BABUJE. Har suka
sokeshi da Mashi, kuma sai suka fice
daga Garin suka koma Bedde ta yanzu.
Koda mayakan Hadejia suka ga an
raunata Buhari sai suka bisu da yaki,
bayan sun dawo sai suka taho da
Buhari zuwa Hadejia, inda suka yi Gadon
Kara suka Dora shi. Akan hanyarsu ta
dawowa Hadejia Buhari ya musu jawabi
kuma suka fahimci cewa Munafurci ne
akayi tsakaninsu da Buhari. Kuma yace
musu lalle In ya mutu su kaishi Hadejia
su binne shi, kuma Allah ya dauki ransa
a Madaci kusa da Hadejia. Bayan fadawa
sun fahimci 'yan-uwan Buhari ne suka
munafurceshi, sai suka yanke shawarar
cewa dukda Kankantar Dansa Umaru shi
zasu Nada A matsayin Sarkin Hadejia.
Kuma hakan akayi karkashin jagorancin
Tatagana da Jaji. In kazo kayi Gaisuwar
Mutuwar Buhari sai ka Juya kayi
Mubaya'a a gun Sabon Sarki wato
Umaru Dan Buhari. Hadejia A yau.