HADEJIA A YAU!
SARKIN HADEJIA UMARU: A SHEKARAR 1863 allah ya yiwa Sarkin Hadejia Buhari rasuwa a Yakinsu da sukayi da Gogaram (bade). Ko da aka dawo Hadejia aka binne shi sai Manyan fadawan Hadejia wadanda akwai Amana tsakaninsu dashi Buhari. Kamar SARKIN AREWA TATA GANA (GINSAU MAI KINA BAWO) DA KUMA SARKIN YAKI JAJI suka jajirce Sai an Nada UMARU DAN BUHARI SARKIN HADEJIA. kuma hakan Akayi!
SARKIN HADEJIA UMARU NA BIYU an nadashi yana da shekara Goma sha Hudu. Kuma manyan fadawan Mahaifinsa sune suke gudanar da Sarautar tunda shi yaro ne. Kuma a zamaninsa Sarkin Damagaram Tanimu ya kawo yaki Hadejia. Kuma yayi sansani a Arewa da Hadejia daga nan har Jigawar Kasim mutanensa ne. saida yayi kwana Arba'in ana yaki amma Hadejiawa basu fasa wasanninsu na dandali ba. Wata rana ana yaki Sai aka harbi dokin Sarkin Arewa! Koda ya mutu sai akaje gida aka dauko wani Dokin aka cire kayan wancan Dokin aka sakawa wanda aka kawo. Tata gana ya koma kan doki, kashe gari ana cikin yaki sai Tata gana ya sauko daga Dokinsa yayi alwala ya koma kan Dokin, to ashe Sarkin Damagaram yana kallon su sai yace Lalle Sarkin Hadejia ya Isa ana yaki ka sauko kayi alwala? Jiya ma an kashe masa Doki amma saida akaje aka dauko wani a gari? Sai Zagin Sarkin Damagaram yace ai ba Sarkin Hadejia bane Yaronsa ne! Sai Sarkin Damagaram Tanimu yace to Ina Sarkin Hadejian? Sai zaginsa yace ai ance yana gida tunda aka fara yakin nan bai taba zuwa ba. Sai sarkin Damagarm yace wa fadawansa Gobe zamu bar Hadejia kar mu tsaya ayi ta kashemu. Saboda Sarkin Hadejia ya raina mu kwananmu Arba'in amma bai taba zuwa anyi yaki dashi ba? Wa yasan me zai mana in ya zo? Amma basu san Sarkin Yaro bane. Washe gari suka juya suka koma Damagaram. Kuma lokacinda sukazo Hadejia Da kaka ne! Anyi girbi Manoma basu gama Tare Amfaninsu ba. Shi yasa suka dade a Hadejia saboda akwai abinci da ruwa a kusa dasu. SARKIN HADEJIA UMARU Mutum ne mai son Nishadi kowane Lokaci yakan fita Bakin kogi ko Gona Domin Debe kewa. Kuma anyi amfani da wannan Damar inda wata rana ya fita sai aka Rufe Masa Kofa. Koda yazo yaga kofa A rufe sai ya juya ya tafi Chamo ya zauna. Aka nada Kanin Mahaifinsa Sarkin Hadejia Wato HARU BUBBA. 1865-1885. Shi kuwa UMARU DAN BUHARI yayi zamansa a Chamo kuma Ya rasu a shekarar 1920. Allah yaji Kansu Ameen.
HADEJIA A YAU.