1, Daren jiya ba na yau bane gun kwanan yaro daban da bubba.
2, Bismillah zana shirya waka sarki Allah kaban basira inyi wakar saude 'yar nikatau.
3, Ina dada godiya ga rabbi Allah da yasa na sanki saude.
4, Ga saude sarauniyar kano mai saukin kayi da son mutane.
5, A wajen kyauta fa ba kamar saude 'yar sarkin kano na korau.
Taurari ko suna da haske basu kai hasken farin wata ba.
6, Inda mata suna sarauta a kano mukan muna da saude.
7, A zaria sunyi Quen Amina to mu a kano muna da saude.
8, A gabas na dangana da Borno ba kyakkyawa kamarki saude.
9, A yamma kwa har naje Ilorin ni banga ba wadda tayi saude.
10, ta nan kudu har zuwa Adamawa banga ba wadda tayi saude.
11, A arewa saida na wuce Nijar banga ba wadda tayi saude.
12, Kai duk matan dake cikin facebook babu wadda tayi saude.
14, Hotonki ana comment akanshi na kirga comment dubu a yanzu.
15, Ga allurar cikin duhu sai mai zurfin hankali ka tsinta.
16, Ga saude bakin zare a matoya sai mai hankali ka tsinta.
17, Ni burina a duniya inga kina mulkin kano sa'ade.
18, Allah ba yanda bai iya ba a zazzau shi ya bai Amina.
19, Ansa giwa cikin zubo taci guda bakin rabonta kelau.
20, Allah in yai nufi ga iko nai babu abinda zai hana shi.