HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Wednesday, June 27, 2012
KANO GARIN ALHERI.
HADEJIA A YAU! Kano ba gari ba Dajin Allah Inji masu iya magana! Tarihin kano abu ne wanda sai dai ace an baka kadan daga cikinsa, domin tarihinta bazai kammalu ba ga duk mai rubuta shi. An kafa kano tun a farkon karni na biyar bayan haihuwar Annabi Isah (AS) wato 500AD. Idan akayi la'akari da zuwan Bagauda da mutanensa. Tun daga wannan lokacin ake mulkin kano kawo yanzu mulkin fulani.
Kano ta shahara ta fannoni daban daban kama daga Ilmin Addini da na boko da kuma Uwa uba kasuwanci wanda ta zama babu kamarta a duk jihar Arewa. Al'adunsu da dabi'unsu abin koyi ne ga duk wanda yayi mu'amala dasu. Allah ya albarkaci kano da Ni'imomi daban daban wadanda basu misaltuwa. Kasuwa kuwa duk abinda ka sani ana sayarwa a duniya zaka samu a Kano, kuma duk abinda kake sayarwa zaka samu masu saye.
Kano ta zama wata cibiya ce wanda duk abinda ya sameta lalle ya samu duk jihar Arewa baki daya. A watannin baya ne kano ta samu kanta a wani hali wanda bata taba zatonsa ba. Wato na hare haren bom da kashe kashen jama'a wanda hakan ya kawo cikas a al'amuran yau da kullum. Amma duk da haka ba'a fasa saye ana sayarwa ba kamar yanda aka saba. Lalle duk abinda ya taba hanci to idanu zaiyi ruwa! Wato duk abinda ya taba kano to hakika ya taba Arewacin Nigeria.
Jama'ar kano da ma Arewacin Nigeria... Na rigingine fa ba-a fada masa ganin farin wata. Ina nufin mun san gurin wanda zamu kai kukan mu, shine sarkin da ya kafa kano ya albarkaceta da mutane Irin su WAZIRIN KANO, Da sauransu. Muna rokon Allah ya karemu daga duk abinda zai kawo barazana ga Kano da ma Arewacin Nigeria. Allah ka mana maganin abinda yafi karfinmu da abinda bamu zaton sa. Domin da ikonsa ne komai ya kasance da kuma abinda zai kasance. KANO KWARYAR KIRA MATATTARAR ALKAIRI. Daukar Nauyi freedom Radio kano.
TARIHIN SARAUTAR SARKIN HADEJIA NA (16)
Ranar Asabat 3-january-1999, Mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Abubakar Maje Haruna ya Nada Alh. Adamu Abubakar A matsayin IYAN HADEJIA, NA FARKO. Kuma Ranar Laraba 11- september-2002, Allah ya yiwa Mai martaba Sarkin Hadejia Rasuwa. Alh. Abubakar maje Haruna.
TO A SAKAMAKON AMINCEWA DA GWAMNATI TAYI DA ZABEN 'YAN MAJALISSAR SARKI WATO (KING MAKER'S) Suka zabi Iyan Hadejia Alh. Adamu Abubakar maje a matsayin sarkin Hadejia, Na Goma sha shida (16). kuma an nada shi Ranar Asabat 14-september-2002. Bisa Al'ada ba'a kwana uku ba tare da an nada Sarki ba.
KUMA HAWANSA NA FARKO A MATSAYINSA NA SARKIN HADEJIA SHINE Hawan sallar Azumi wato A watan Disamba 2002. Sannan sallar Layya February 2002 Bai Hau ba saboda yaje Saudiyya.
29-March-2003.
A YAU ASABAT 29-March-2003 ANYI BIKIN BADA SANDA! An baiwa sarkin Hadejia Sanda a Karkashin shugabancin Gwamnan Jigawa ALH. IBRAHIM SAMINU TURAKI! A STADIUM TA HADEJIA.
Kuma bayan an Bashi Sandar jagorancin Kasar Hadejia A karkashin Tutar Shehu Usman Dan fodio, Mai martaba sarki yayi Hawa Guda Uku Wadanda suka Kayatar da
jama'ar Hadejia.
1, BIKIN GASAR ALQUR'ANI A SECONDARY FANTAI
2,TARON DA AKAYI A MAKARANTAR KOFAR AREWA
3,SAI HAWAN GANDU WANDA SHIMA YANA DA TARIHI A MASARAUTAR HADEJIA.
Hakiman da ya fara Nadawa sune:
1, DAN GALADIMA Alh.babbaji Adamu Hakimin waje
2, SARKIN DAWAKI Alh. Umar IbrahimHakimin kiri kasamma.
3, KATUKAN HADEJIA NA (2) BIYU Hakimin Turabu.
A gaba zan kawo muku Labarin Fitar sarkin Hadejia Rangadi da yayi da kuma Hakiman da a Nada.
Subscribe to:
Posts (Atom)