content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!: 11/01/2018 - 12/01/2018

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, November 11, 2018

MATASA A FAGEN SIYASA.....

HADEJIA A YAU!



1. MATASA A FAGEN SIYASA.  
Da farko zamu dubi kalmar matasa ko matashi, me ake nufi da matasa?
Matasa ko matashi wata kalma ce ta Hausa wadda ake kiran wasu mutane da ita, (Mai Tashe) ana nufin wadanda shekarunsu ya fara daga goma sha takwas  18, zuwa shekara Arba’in 40. Domin ko a musulunci matasa su aka fi bukatar su bada gudunmawarsu don ci gaban al’umma, sannan matasa sune suke shirya duk wani tsari mai inganci na zaman rayuwa wadda idan sun gyaru hakika al’umma ta gyaru.

Matasa a fagen siyasa suna da muhimmiyar gudunmawa da zasu taka domin dorewar Demokradiyya, duk wata gwamnati  bata zama ingancacciyar gwamnati saida matasa. tarihin siyasar duniya  ya nuna matasa sune kan gaba wajen juya akalar rayuwar al’umma, domin sune masu zabe kuma daga cikinsu ake zaba. Babu wata siyasa da zata ci gaba ba tare da matasa ba, kuma matasa zasu iya tsare mutuncinsu a siyasa ba tare da anyi amfani dasu an gurbata siyasa ba. Tun lokacin NPC ta Sardauna da NEPU ta Aminu Kano aka baiwa matasa dama wajen tsayawa takara a kujeru daban daban don inganta rayuwar Al’umma, misali duk dan takarar da ya tsaya takara a lokacin Npc da Nepu babu wadda shekarunsa suka wuce 40, duk daga 35 ne zuwa 37. Haka akayi har zuwa zamanin NPN da PRP Idan ka debe shekarun Shehu Shagari daga lokacin da yayi mulki zuwa yau zaka gane lalle yayi Shugabancin Nigeria ne yana Matashi, Haka Gwamnonin zamaninsa irin su Rimi da sauransu har zuwa Senatoci da ‘yan majalissun Tarayya da na jihohi. Tun daga wancan lokacin zuwa yau matasa ne suke jan akalar Siyasar Nigeria, dukda cewa ana samun tsarmi da yawa da mutanen da muke kira Dattijai. Idan muka dubi lokacin Gwamnatin Saminu zamu ga yayi gwamna ne shekarun sa basu kai Arba’in ba, haka Mataimakin sa Barrister Ibrahim Hadejia ya zama Deputy Governor yana da Shekara 37 zuwa 38. Wannan yana nuna mana cewa Matasa sune dai a fagen Siyasar Nigeria, amma yanzu abin haka yake kuwa? Wadannan mutane da na saka hoton su wato Mustapha Sule Lamido, Ahmed Bello, Hussaini Rally, Barr. Mallam Abubakar Jallo, sune suka fanshi Matasa a fagen Siyasar wannan lokaci, kuma sune zasu zama fitila ga sauran matasan mu zuwa nan gaba, domin sun kasance sun karfafawa matasa Gwuiwa wajen damawa dasu a fagen Siyasa.

MECECE SIYASA?
Ma’anar siyasa itace tsara rayuwa ko samar da shugabanci da duk abinda yake ta’allake dashi, kamar tsarin zabubbuka, yin doka, umarni da hani. Tsarin horo ga wanda ya karya doka, kira ga hukuma da tayi ko ta bar wani abu.

Haka kuma kalmar siyasa kalma ce ta larabci aka arota zuwa harshen Hausa, ita kalmar siyasa ta samo asali ne daga ‘SASA’ ko ‘SULASI’. Kaga kenan wannan kalma ta “SIYASA” tana nufin Jagoranci, hikima, kiwo, horarwa da gudanarwa. Haka kuma ana amfani da siyasa yayinda wani abu na son zuciya ya shiga, amma wannan ba shine ainihin  kalmar ba. Ilmi yana da matsayi mai girma a tsarin siyasar kowace Al’umma. Daga kaarshe ina Addu’ar samun Nasara ga Matasa da suka tsaya Takara a kujeru daban daban, Allah ya tabbatar mana da Alkairi a Nigeria baki daya.

Matsayin Ilmi a siyasar Turai... masu ilmin falsafar Turai sunyi  ijma’i  game da muhimmancin Ilmi a siyasa. Plato yana ganin masu ilmi ne kadai suka cancanci su shugabanci jama’a, yayinda shi kuma  Aristotle yace A’a idan ana son siyasa ta inganta sai a baiwa jama’a  Ilmi. Shi kuma Spinoza cewa yayi amfanin siyasa shine ‘yanta Dan-adam da samar masa da Adalci, wannan kuwa bazai samu ba sai an bashi Ilmi. Shi kuwa Emanuel kant yana ganin rayuwa ce gaba daya sai da ilmi, yadda zaka kare lafiyarka, yadda zaka nemi Aure ka rikeshi, yanda zaka zabi shugaba.

Wasu mutanen su dauki ma’anar siyasa kamar wata kasuwa ce ta baje hajoji, inma a samu riba ko a samu faduwa. Irin masu wannan tunanin ne ake kira ‘yan siyasa marasa akida, domin su babu ruwansu da abinda ya dace illa abinda Aljihunsu ya dace dashi. Wasu kuma sun danganta siyasa kamar  dabi’a ce ta halittu masu rai aga uwa tana gaba ‘ya’yanta suna biye da ita, wato mai hankali shike shiga gaba domin na baya yayi koyi dashi.

Ismaila A Sabo
Ismailasabo@gmail.com