"" /> HADEJIA A YAU!: Mar 31, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, March 31, 2012

SARKIN HADEJIA BUHARI DA WAZIRIN SOKOTO A KATAGUM (1)

Image Hosted by ImageTitan.com
HADEJIA A YAU! A lokacinda Sarkin Musulmi Aliyu Bubba ya turo Wazirin Sokoto Abdulkadir Gidado Gurin Sarkin Hadejia Buhari, Wazirin Sokoto shine wakilin sarkin Musulmi a yankin Gabas sai ya taho Hadejia daga Kano Amma sai ya wuce Katagum, Ya turo Jakada zuwa Hadejia yana So su Gana da Sarki Buhari.

Buhari yayi tunanin ya tafi shi kadai daga baya sai ya canza shawara kawai ya Tafi Katagum Da Mutanensa. zasu gamu da Wazirin Sokoto a can. Lokacinda suka isa Katagum Sarkin Hadejia Buhari ya tsaya a Kofar Garin Katagum sai ya tura a fadawa Waziri Ya Iso Wazirin Sokoto da Sarkin Katagum suka zo sai sukace Buhari ya Biyosu amma shi kadai tunda Shawara zasuyi.

Sarki Buhari ya bisu Har ya shiga Kofar Garin Katagum. Sai Mawakinsa wato DAN FATIMA ya fara masa waka yana cewa:-

1, Abubakar Garba Mijin Maza,

2, Buhari kai ke da Nutso Kai ke da Hankali.

3, Don Allah yayi ka Uban Jama'a

4, Kuma kai Allah ya baiwa shugabancin Gidan Sambo

5, Ba dan na isa ba, In ka yarda ga Aike ka shiga dashi

6, Fasa Maza Gagara gasa Aiken shine

7, In ka sauka lafiya ka gaida Na Lara Sarkin Auyo

8, Ka gaida Bello Sarkin Dutse

9, Na Sambo sai ka dawo.

Abinda Dan fatima yake Nufi Sarkin Auyo da Sarkin Dutse duk Buhari ya kashe su. Dan haka shima In ya shiga Katagum Lalle Bazai fito ba.

KodaSarki Buhari yaji Wannan Waka ta Dan fatima sai ya juyo da baya, Wazirin sokoto da Sarkin Katagum da suka fahimci Buhari ya juya sai suka Biyoshi da Ihu Su da mutanen Katagum Suna ce masa Kafiri yaki bin Umarnin Sarkin Musulmi. sai da suka biyoshi har Unik Iyakar Hadejia Da Katagum. kuma sun kashe wasu daga mutanen Buhari. koda yazo Unik sai ya yanke Shawarar ya yi sansani a nan ya koma ya yaki Katagum. kuma mutanensa suka koma suka Karkashe Mutanen Katagum karkashin jagorancin Barde Risku. Daga nan Rashin Jituwa Tsakanin Hadejia da Katagum ya Fara har bayan shekara Goma sha biyu bayan Mutuwar Buhari.

(1863). daga nan Aka samu wasa tsakanin Hadejia da Katagum. koda Katagumawa suka juya sai Wazirin Sokoto ya sake Gyyato Mutanen kano suka Hadu da Na Katagum zasuzo su yaki Buhari. da sarki Buhari yaji wannan Labarin sai shi da mutanensa suka bar Hadejia suka tafi Shabawa Iyakar Hadejia da Gumel Sukayi sansani a can.

da Buhari ya bar Hadejia sai Wazirin sokoto ya nada Wansa Ahmadu Sarkin Hadejia. A shekarar (1850). Wanda dama saboda shi suka Takurawa Sarki buhari.