Tarishi dai yanuna cewa babu wane dalili da
ke jawo yawan 'kaurace-'kaurace kamar
ya'ke-ya'ke, Mutanin Gumel (Mangawa) sunyi
fama da ya'ke-ya'ken tsaron gida, tundaga
inda suka fara kaura daga Ngazargamu,
yazuwa inda aka kafa garin Gumel na yanzu.
Ya'ke-ya'ke ke sawa idan jama'ar wata
gundumar suka ga alamar cewa za'a
mamayesu, sai su kauracewa guri. Jama'ar
Gumel sun tabka ire-iren waddannan
fa'dace-fa'dacen, da dama kafin su kafa
garin Gumel, da kuma bayan sun kafa zango
a Gumel. Gumel tana daya daga cikin
garuruwan da basu nuna amincewarsu da
mulkin Hausa-Borno, ko na Sokoto ba, ko da
shike Barno ta mallaki Gumel da farko,
mulkin Borno bai taka kara ya karya ba,
domin masarautar Gumel ta balle daga
'kar'kashin Borno ta yi tsayuwarta ta kanta a
1837.
Tarihin yake-yaken Gumel ya faro ne tun
daga karni na goma sha takwas, zamanin
sarki Kalgo (1804-1811) wanda ya dinga
kare garin Gumel, daga hannun mayakan
Kano da kuma Machina har sai lokacinda
wani bawan sarkin Machina ya sami fili ya
soke shi da makami ya masa raunin da ya
karasa shi har lahira.
Saboda kwadayin samun fa'Da'Da 'Kasa, da
'Yancin kai, wanda jama'ar Gumel suka fara
nunawa tun fil azal, yasa sun kutsa kai
wanjen ya'Ke wanda ake kira da "karo daya
tsakanin kyai da dutse", suka fara yakar
garuruwa wanda har ya sa ratar mil
tamanin ne kawai ya raba su da shiga cikin
garin Kano.
A wani fage da Gumel ta taimakawa Kano za
a iya samun karin haske irin kwazon
jaruman Gumel a ya'ke-ya'ken da suka goyi
bayan kungiyar Yusuf a tsakaninsu da
askarawan Tukur na yakin (1893-1895).
Wata yar gajeruwar jawabi da Gwadabe ya
zayyana, ta ambaci irin kwarewa, jarunta, da
kuma tsarin askarawan Mangawa, tun
lokacin da suka soma fa'Dace-fa'Dacen su a
mazaunin su na farko a Dogoma. A cikin
wannan jawabin Gwadabe ya kwatanta irin
shirin Mangawa da na askarawan Shehun
Borno, inda shi shugaban askarawan ke
bada umurni, kuma yake tafiyadda fasalin
hare-haren askarawan sa baki 'Daya. Da
farko Shiga cikin mayakan Mangawa an
takaita shi tsakanin yan sarauta kawai, ko
da shike irin wannan daukar na saukaka
samun maya'ka, yana kuma toshe armashin
samun kwararrun askarawa. Bisa wata yar
tarzoma a shekara ta 1852 Mai Muhammadu
Cheri ya fa'da'da daukar askarawa, ya bu'Da
kofar dauka ga duk mai niyyar shiga, ya
kuma sau'ka'ka wa wasu kwararrun
maya'ka ko da basu da jinin sarauta zasu iya
shiga kwamban askarawan.