"" /> HADEJIA A YAU!: Jun 14, 2022

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, June 14, 2022

GIDAUNIYAR MALLAM INUWA FOUNDATION TARE DA HADIN GWIWAR QATAR CHARITY FOUNDATION SUN TALLAFAWA MABUKATA DA KAYAN SANA'A DOMIN DOGARO DA KAI.

HADEJIA A YAU!

A jiya Litinin 13/6/2022, wannan gidauniya ta gabatar da taro a garin Hadejia domin tallafawa mabukata da masu karamin karfi abubuwan dogaro da kai. Abubuwan da aka raba sun hada da Kekunan Dinki da Baburan hawa da dai sauran su. Taron ya samu Halartar Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh Adamu Abubakar Maje CON tare da Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi da Shugabannin Kananan Hukumomi na masarautar Hadejia. Da yake bayani mai Martaba Sarkin Hadejia ya yabawa Mallam Kashif Inuwa bisa amfani da Ilmin sa da yake wajen ciyar da Al'umma gaba da sanya farin ciki a zuciyar su. Mai Martaba Sarki ya kara da cewa Irin wannan ci gaban Al'umma suke bukata a wannan lokaci, domin wasu suna da zuciyar yin sana'ar amma rashin abin sana'ar ya hana su. Daga karshe mai Martaba Sarkin ya yi Addu'ah ga wannan Gidauniya Allah ya daukaka ta ya basu ikon ci gaba da ayyukan Alkairi.

Bayan wannan Gidauniyar ta bude rukunin gidaje da aka ginawa masu karamin karfi, da gina famfuna da kuma kafa harsashin gina Ajujuwa a masallacin Yorubawa dake Unguwar Gawuna a Hadejia. Da yake maida jawabi Shugaban wannan Gidauniya Mallam Yusuf Baban ya yabawa Wadda ya kafa Gidauniyar sakamakon namijin kokari da yake wajen samo abubuwan da za su taimakawa Al'umma. Ko a kwanakin baya Wannan Gidauniya ta bada kyautar mota ga wata kungiyar kare hakkin mata da kananan yara da ke garin Hadejia.

 

A bangare daya kuma wannan Gidauniya ta gabatar da Aikin gyaran Ido kyauta da bada Glass din karin gani ga mutane 600, a Masarautar Gumel. In dai ba'a manta ba kwanaki an gudanar da aikin gyaran Ido a Hadejia, wadda mutane da dama suka amfana. Da suke bayyana ra'ayoyin su Al'ummar da suka amfana da wannan tallafi sun yi godiya ga wannan Gidauniya tare da fatan Alkairi, domin wannan gidauniya ta basu abubuwan da za su dogara da kan su har ma su taimakawa wasu. Daga karshe sun yi Addu'ah ga Mallam Kashif Inuwa da Gidauniyar Qatar foundation da kuma Gidauniyar Mallam Inuwa foundation domin kawo wannan abin Alkairi ga Talakawa masu bukata.