1, Bismillahi rabbana Allah sarkin taimako ka kaini gumel gun sarkin gumel muhammadu sani.
2, Sake shiri muhammadu linzamin duniya uban na makwallah.
3, Na bar Hadejia ran asabat mutane suna ina mallam zaije sai nace Gumel zan jeni.
4, Kuma naje Gumel cikin sa'a sarki na ishe cikin barga tai.
5, Akwa wani doki yana Gumel mai kyau a cikin fada yai daban da dawaki.
6, Doki guda a bakin ran doki goma bidi dan yalawa.
7, Nagarta da kyan gani akwaita a gun bidi takamarsa abar kallo ce wajen rawa mazari ma yasan da bidi dan yalawa.
8, Dokin sarakunan iko ne jirgin saman dawakan lautai.
9, Dokin da ko yana barga tasa indai ka ganshi ka gama kallo.
10, sarkin Gumel uban malam sule kune kuke da mulkin lautai.
Zan kawo muku sauran baiti 5oma a gaba.
HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com