HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Tuesday, November 27, 2012
MANYAN 'YAN SIYASAR HADEJIA
Hadejia A yau. Wadannan mutane sune Ruhin siyasar Hadejia! Gudunmawar da suka bayar a siyasa da ci gaban yankin Hadejia sai dai Allah ya saka musu da Alkairi. Sunyi siyasa a lokacinda ba'a san Daga kai sai 'ya'yanka ba! Domin sun kafa mutane da dama a Hadejia da kewaye. Duk unguwa zakaga akwai mutanenda suka kafa a siyasa. Lalle sun cancanci yabo. Idan muka fara da Marigayi Alh. Bello Auyo zamuga cewa Ayyukanda yayi a Hadejia har yanzu babu wani ko wata gwamnati da tayi makamancin nasa. Kama da Secretaria, Maternity, da sauran abubuwanda har yau ana amfana dasu a Hadejia. Allah ya kyauta kwanciya. Mallam Ibrahim Kwatalo shima ya gina mutane daban daban a Tarihin siyasar Kasar Hadejia. Duk Wanda yanzu yake Cikin Gwamnati, in ba yaronsa ba sai wanda shine ya kafashi. Allah ya kyauta kwanciya. Alh. Shehu Mujaddadi (Alkali) shehu Illa shehu, shima kamar M. Ibrahim Kwatalo, ya gina mutanenda suka gina Mutane a Tarihin siyasar Hadejia. Kuma Har yau Taswirar siyasarsa ce take Tasiri a Hadejia. Allah ya kyauta Kwanciya. Alh. Muhammadu Danjani Hadejia tarihin siyasar Hadejia bazai manta da kai ba! Shi ya fara Dan majalissar Wakilai a Jamhuriya ta biyu. Kuma jigo ne a jam'iyyar NEPU. Wadanda sukayi yaki da mulkin Danniya da kama karya. Shaho birkita kaji na Garba, Bauna wanda ya dosheta babu maduhu sai wani ba tasa ba. Allah ya kyauta kwanciya. Ahmed Garba (M.K.) ko an kika irinka akeso. Har yau Taswirar siyasar Hadejia tana Hannunsa. Duk unguwarda kaje a Hadejia to akwai mutanen da a kafa kuma suka kafu. Ya samawa matasa aikin yi bansan Adadi ba! Amma nasan babu wanda yayi kamarsa kawo yanzu. Zabgai yabin Bauchi da kare dangi Maza sai kui Hankali, Mai tulu kaji tsoron fad da mai sanda ko yana a kwance! Kainuwa dashen Allah yaya zakuyi? Ruwa sai ya kare Kainuwa ta kare ba dai kaga bayanta ba. An karawa kogi Ruwa mai jinga kayi jingarka zai karya Inda yakeso yabi. Masu fura da zuma sun kula da gwangi, idan gwangin zakusha to, Allah ya bamu zuma ku ya baku Gwangin baya tana son gaba. Hadejia A yau.
Subscribe to:
Posts (Atom)