HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Monday, March 11, 2013
FACEBOOK A KARKARA!
HADEJIA A YAU!Hadejia A yau! Assalamualaikum! 'Yan uwa barkanmu da yau, da fatan Alkairi.
muna gaf da fara wani shiri a wannan
shafi na facebook. shirin kuwa zai leka ne loko na kauyukan Arewacin Nigeria, domin jin halin da talakawa suke ciki a kauyuka
da karkara. domin wasu kauyukanma
ba'a kulasu sai an buga gan-gar siyasa.
Sanin kowane Talakawa akar-kara suna
cikin mawuyacin hali fiye da na biranen
Arewacin Nigeriya. Ada sashin hausa na
gidan redion b.b.c. yana gudanar da
wannan shiri wanda kuma yin hakan na
sanya gwamnati ta gyara kura-kuranta.
To amma yanzu shiru muke ji ba labari.
Hakan yasanya mu yin azama wajen
gabatar da wannan shiri ta hanyar fcbk.
kasancewar shugabanni na amfani da
shafin na fcbk. Duk da ma dai sunsan
halinda ake ciki to amma fadawa duniya
zai kara sanyasu su gyara. Kaima kema
zaku iya shiga wannan shiri ayi da ku
domin yin hakan jihadi ne bubba wanda
Allah ne kadai yasan ladan da zaka samu.
Domin ka yi sanadiyyar fitar miliyoyin
alumma daga cikin Kangin talauci. Duk
mai bukatar ayi wannan aiki da shi ya
Tuntubi Garba Tela Hadejia ta inbox. Ko
ya kira lambarsa ko ya masa sakon
Wasika (text). 07065540705. Allah ya
bada Iko.
Subscribe to:
Posts (Atom)