NAZARI AKAN TARIHI DA RAYUWAR GALADIMAN HADEJIA ALH. USMAN ABDUL'AZIZ. (USMAN II)
(TARE DA SULEIMAN GINSAU)
"SALSALAR HAIHUWA DA KARATUN GALADIMA"
Kamar yadda yake a bayyane an haifi Mai Girma Galadiman Hadejia Alh. Usman Abdul'aziz a cikin garin Hadejia da ke Jihar Jigawa a ranar 23 ga watan Oktoba a shekara ta 1959, wadda yayi dai-dai da 20 ga watan Rabi'ul Sani na shakarar ta 1379. Idan muka dubi rayuwar Galadima a bangaran karatunsa ya halarci Makarantar Hudu Islamiyya dake garin Hadejia a shekarar 1963, ya halarci Makarantar Firamare ta Hadejia Central a cikin shekarar 1965-1971, inda daga nan kuma ya wuce zuwa Kwalejin Geamnati dake Kano wadda a yanzu ta koma Rumfa Kwalej a shekarun 1972-1976, a matakin sakandare daga nan kuma ya wuce Makarantar koyan sana'a dake Kaduna (Kaduna Polytechnic) anan ne ya yi karatunsa na Karamar Diploma ckin shekarun 1976-1979. Yayi Babbar Diploma akan kasuwanci a (Kaduna Polytechnic) cikin shekarun 1979-1981. Yaci gaba da karatunsa a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi a Shekarun 1997-1998 ya sami shaidar Babbar Diploma ta gaba da Digiri a kan kasuwanci, daga nan ya wuce kasar waje domin karo Ilmi inda ya shiga Jami'ar St. Clements da ke kasar Australia a shekarun 1998-1999 a inda ya samu shaidar Digiri na biyu a bangaren Kasuwanci, daga nan ya sake komawa Jami'ar Tafawa Balewa dake Bauchi domin cigaba da karatunsa a inda ya sake samun shaidar wani Digirinsa na biyu a kan kasuwanci na komai da ruwanka wato ( General) a shekara ta 2000-2001. Mai Girma Galadima Usman Abdul'aziz ya yiwa kasa hidima a Jihar Binuwai. daga shekara ta 1981zuwa1982 (Taskar Suleiman Ginsau)
"RAYUWARSA TA AIKI"
Bangaran Rayuwarsa ta aiki kuwa abin abin sha'awa da ban mamaki Mai Girma Galadiman Hadejia Alh. Usman Abdu'aziz ya fara aiki ne a ma'aikatar Ciniki da masana'antu ta tsohuwar Jihar Kano a shekara ta 1982, a matsayin jami'i mai kula da bangaren ciniki.
"AIKIN GALADIMA A KAMFANIN TOTAL"
Daga nan ya kama aiki da Kamfanin Mai na Total a matsayin wakili mai kula da harkokin kasuwanci a watan Augusta na shekarar 1983, bayan samun horo da yayi a Hedikwatar Kamfanin da ke birnin Lagos, daga nan an yi masa canjin aiki zuwa Jihar Kano a matsayin jami'i mai kula da harkokin kasuwanci.
Bayan dawowarsa Kano ansake yi masa canjin aiki zuwa Jihar Barno a shekarata 1988 a matsayin wakilin harkokin kasuwanci mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas na Kamfanin Mai na Total. Kasancewarsa a wannan shiyya ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban wannan Kamfani, hakan ne ya sanya aka sake yi masa canjin aiki zuwa sabon ofishin da aka bude na Kamfanin a Jos, hedkwatar Jihar Filato a matsayin Manaja mai kula sha'anin kasuwanci, zamansa a Jos ya gudanar da ayyukan da suka kai Kamfanin ga samun nasara, a inda aka daga darajarsa a wannan shiyya, hakan ta sa aka kara ciyad dashi gaba aka bashi Manajan kula da kasuwanci a shiyyar Arewa maso Gabas, a shekara ta 1996. A lokacin da yake gudanar da ayyukansa a wannan shiyya a Jos bayan ci gaban da na bayyana mai dorewa ya samar ta fuskar habaka kasuwancin Kamfanin. Lallai Galadima ya tabbatar wa Duniya cewa shi tsayayye ne wanda yasan harkokin kasuwanci bisa gaskiya da rikon amana.
Har ila yau kwarewarsa ce ta sa aka sake karama masa mukami zuwa Manajan yanki wanda ya kunshi Jahohi kamar su:-
1. Bauchi
2. Gombe
3. Barno
4. Yobe
5. Adamawa
6. Taraba
7. Filato
8. Nasarawa
9. Binuwai
10. Kogi
shedikwatar tana nan a matsayinta a Jos.
A shekara ta 2001 lokacin da Kamfanin Mai na Total da na ELF suka hade an sami canje-canje inda aka kirkiro sabon Ofis mai kula da Arewa mai nisa dake da shedikwata a Kano, tare da nada Galadima a matsayin Manajan shiyya mai kula da Jihohin da suka yi iyaka da kasashen Republic of Benin, Niger, Chad da Cameroon kamar haka:-
1. Kebbi
2. Sakkwato
3. Zamfara
4. Katsina
5. Kano
6. Jigawa
7. Yobe
8. Barno
9. Adamawa
A shekarar 2006 an kuma yi masa canjin aiki zuwa birnin Benin a matsayin Manaja mai kula da shiyyar yamma ta tsskiya. Kamfanin Total ya kirkiro Ofishin kasuwancin Najeriya a Abuja wanda aka bawa Galadima Manajan wannan Ofis mai kula da shi a shekara ta 2008. (Taskar Suleiman Ginsau)
"AIKIN GALADIMA A KAMFANIN MAI NA NNPC"
Dangane da irin gagarumar gudun mawa da jajircewar sane tasa, daga bisani aka yi masa canjin aiki zuwa Kamfanin NNPC a shekara ta 2012 lokacin da Kamfanin na NNPC ya nemi Kamfanin Total da ya basu shi don ya taimaka wajen canja akalar tafiyadda kamfanin NNPC Retail yadda zai yi daidai da sauran manyan kamfanonin mai na kasuwanci irin su TOTAL.
A yayin zamansa a Kamfanin NNPC na kasa ya samar da ci gaba ta fuskar samar da kudaden shiga masu tarin yawa, ya samu nasarar bude kananan gidajen Mai shiryawa tare tabbatar da tsaftace kasafin kudaden Kamfanin, Galadima ya samar da ci gaban Kamfanin NNPC Retail tare da inganta harkokin kasuwanci a matsayin Janar Manaja mai kula da saye da kasuwanci a karkashin NNPC Retail Ltd, a Abuja cikin watan Maris na 2012.
Haka kuma Kamfanin NNPC ya sake ba shi mukami Janar Manaja mai kula da tsare-tsare da dabarun aiki cikin watan Maris na 2013 a dai karkashin NNPC Retail Ltd.
"A JIYE AIKIN GALADIMA"
Alhamdulillah mai Girma Galadima ya yi aikinsa cikin koshin lafiya tare rikon amana da gaskiya wanda hakan ya bashi damar ajiye aikinsa cikin walwala da jindadin, Galadima ya ajiye aiki don kashin kansa a shekara ta 2014, inda ya kafa Kamfaninsa mai suna ENCEE BUSINESS SERVICES, wanda yake gudanar da shawarwari da horo kan yadda za'a bunkasa harkokin kasuwanci Mai da Iskar Gas...
Galadima yana da matan Aure guda biyu da 'ya'ya Goma... Ina mai addu'a agareshi Allah ya tayashi riko, Allah ya daukaka wannan Masarauta ta Hadejia.
Tsarawa
ISMAILA A SABO
Tsarawa
ISMAILA A SABO
Mai Nazari
SULEIMAN GINSAU
Association Of Nigerian Authors (ANA)