"" /> HADEJIA A YAU!: Mar 22, 2012

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, March 22, 2012

HADEJIA A YAU!: TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!

HADEJIA A YAU!: TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!: HADEJIA- TARIHIN KAFUWAR Hadejia Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, a yawon farauta da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sa...

TARIHIN HADEJIA A TAKAICE!

 HADEJIA A YAU - TARIHIN KAFUWAR HADEJIA Ya farune daga wani maharbi mai suna Hade, shi dai wannan Mutumi Maharbi ne kuma yana yawon farautarsa ne ya taho yankin Hadejia. Kuma a yawon farautar da yakeyi ne wata rana yana tafe da karyar sa sai tayi nisan kiwo har tazo bakin Kogin hadejia, bayan ta sha Ruwa kuma ta shiga ta jika jikinta. ko da tazo sai yaga duk jikinta da ruwa, sai yayi mamakin hakan har ma sai yabi sawunta. Koda yaje sai yaga kogi kuma ga tsuntsaye suna shawagi a gurin. Sannan kuma ya rinka jin kukan Namin Daji, Sai ya yanke shawarar zama a wannan gurin, kuma hakan yayi. Anan ya zauna yayi bukkarsa yake harbe harben Namun daji kuma yayi su wato kamun kifi. In ya kashe namun daji sai yaje ya sayar da fatun. Da kuma Naman. Harma ya dauko Matarsa wato Jia ya dawo da ita wannan gurin. Koda maharba 'yan-Uwansa suka ga Gurinda yake akwai Namun daji da abubuwanda suke bukata sai sukayi shawarar suzo su zauna dashi, sai gurin ya zama Gari Kuma mutane suna zuwa sayen fatu da naman dabbobi a garin. Duk wanda yazo garin sai yayi sha'awar zama a gun, haka nan gari ya fara bunkasa wasu maharba, wasu masinta, wasu kuma mafarauta. Sai gari ya kafu kowa yazo wucewa sai ya yada zango a garin. 

 To kasancewar gari sai da shugabanci ne yasa shi Hade ya zama shugaban garin, duk wanda zaije sayen fatu ko nama sai yace na tafi garin HADEN-JIA. Wato ana masa lakabi da sunan matarsa. To sakamakon takaita kalma irin ta Bahaushe sai aka dunkule sunan ake cewa Hadejia. Kuma bayan zamanin wannan mutumin Hadejia taci gaba da zama gari a Karkashin Daular Biram (Garun Gabas) kuma Sarkin Gabas shine ya Nada Dan-uwan Sarkin Machina Algalfhati ya zama shine Sarkin Hadejia, Shekaru da Dama bayan Hade ya Mutu. Wadannan sune Sarakunan Habawa. Kuma a lokacin akwai kananan Garuruwa masu cin gashin kansu kamar Rinde, yayari, wunti, Anku da dai sauransu. Wadanda suma suna da nasu sarakunan a wannan Lokacin. Amma yanzu duk unguwanni ne a cikin garin Hadejia. 

Hadejia sunyi sarakunan Habe guda talatin da biyu(32) amma sunan mutum uku ake dasu wadanda sukayi mulki kafin zuwan Fulani. 1, BAUDE 2, MUSA 3, ABUBAKAR. Kuma a lokacin Abubakar fulani sukazo kasar Hadejia, kuma shine ya basu masauki a Hadejia Lokacin Hadejia tana karkashin Daular Borno, kuma ya nada Umaru a matsayin Sarkin fulanin Hadejia. Wato kafin Jihadin Shehu usman dan fodiyo. Kuma har yanzu fulanin sune suke sarautar Kasar Hadejia.

MASARAUTAR HADEJIA...... 
Masarautar Hadejia daddiyar masarauta ce wadda ta kafu shekaru da dama da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da kuma yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. sannan tana daga cikin masarautun da sarakunan HABE suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, masarautar  tana daya daga cikin masarautun da suke Karkashin Daular Usmaniyya. Daga Gabas tayi
iyaka da Tsohuwar Daular Borno da Gorgaram, daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu tayi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa tayi iyaka da Masarautar Gumel.

Birnin masarautar yana cikin garin Hadejiya dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asalinsa daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin, wannan maharbi ana kiransa da suna HADE,  yana da matarsa da ake Kiranta da suna JIYA, Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama HADEJIYA. 
A wancan lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabida sunan Matarsa. Saboda takaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejiya.

A wani littafi da Marigayi Tafidan Hadejiya Abdu Maigari ya rubuta ya bayyana cewa
‘‘Shi wannan mutumin da ya kafa Hadejiya wato Hade ya taho ne daga yankin Machina a yawon farauta da yake har ya iso wannan yanki, kuma da ya shigo sai yaga Daji mai Ni’ima da tsuntsaye da namun daji ta ko ina, kuma ga kogi ya fito daga yamma ya gangara zuwa gabas Sannan ga ‘ya’yan
itatuwa kala kala. Da ganin haka sai ya kewaye dajin sosai don ya samu inda ya dace ya zauna, sai ya samu wuri ya kafa Gadonsa irin na maharba yaci gaba da farautar Namun daji da tarkon tsuntsaye’’.

Bayan kwanaki wannan maharbi yana zaune a wannan wuri sai yayi shawarar ya koma ya dauko matarsa don su cigaba da zama a wannan wuri. A lokacin da yayi niyyar komawa sai ya debi abinda zai iya diba na Naman da yayi farautarsa ya dawo garinsu ya dauki matarsa ya koma wannan dajin da yanzu ake kira da suna Hadejiya, sai ya kafa bukkarsa a kan jigawa kuma yaci gaba da farautarsa a wannan wuri har
mazauna karkara dake kusa da wurin suka san da zamansa suke zuwa sayen nama da sauran dabbobin daji. Ana haka ne jama’a suka rinka  zuwa suna kafa bukkokinsu wasu masunta wasu kuma mafarauta da masu kamun tsuntsaye har gari ya zama gari ake kiransa Garun Haden Jiya, sannan akayi shugabanci, zuwa wani dogon lokaci aka takaita Kalmar ta zama Hadejiya. 

Ance a lokacinda ya zauna a Bangaren
Arewa akwai wani gari da ake kira Hadegwaigwai inda yanzu Rubban Dakata take, sannan a bangaren gabas akwai gari da ake kira Kulunfarda inda ada can yake kan hanyar Tandanu. A yamma kuma akwai garin Kadime sannan a Arewa akwai garin da ake kira Majeri, a bangaren kudu kuma akwai garin Tunawa wadda yanzu ake kira Auyakayi. Sannan akwai Kudigin da Hadebako wadda a lokacin take kusa da Kafur, sannan akwai Urki wadda yanzu ake kira Unik sannan akwai Majawa, da kuma manyan garuruwa irinsu Auyo, Garungabas, Kazura, Dawa da Fagi.

A wancan lokacin ance Hadejiya tana Karkashin Daular Auyo ne amma wasu sunce a’a tana karkashin Ikon Garungabas ne tunda daga can ne ake nada Sarki ake kawoshi Hadejia, masu wannan da’awa sun
bada labari kamar haka…

        ‘A zamanin Sarkin Kano Yakubu dan              Abdullahi Barja wadda yayi sarautar
        kano a cikin shekarar (1452-1463),                   Algalfati dan sarkin Machina yaje kano         tare da ‘yan-uwansa guda uku inda                  Sarkin kanon ya bashi sarautar Gaya,            dan-uwansa na farko kuma yaje Rano              Sarkin Rano ya bashi sarautar Dal, na           biyun kuma yaje Zazzau Sarkin                      Zazzau ya bashi sarautar Gayan, na               ukun yazo Biram (Garungabas)  inda              Sarkin Gabas ya bashi sarautar                         Hadejiya.
        Zuriyarsa ne sukayi mulkin Hadejia               har tsawon lokacinda Sarkin Borno Mai        Ali Ghaji ya tura Dansa Mai Idris Aloma        ya yaki kano, sai ya biyo ta Hadejia ya            yaketa ya cinyeta da yaki da sauran                kasashen dake yammacin Borno, sai ya          danka ikon Hadejia da Garungabas da            Dawa da Fagi a hannun Galadiman                Borno, kuma shi Galadiman Borno sai            ya barsu a rarrabe kamar yadda suke            tun farko. Sashen Auyo ya barshi a                  hannun sarkin Auyo, Hadejia ya barta a
        hannun sarkin Hadejiya, Garungabas             ya barta a hannun sarkin Gabas,                     sannan Dawa da Gatare da sauran duk         sai ya barsu a hannun fadawansa,                  amma duk a wurinsa suke karbar                  umarni kuma shi ake kaiwa
       Albarkar kasa har zuwa tsawon lokaci’.

Koda yake ba’a samu rubutaccen tarihi game da sarakunan Habe da suka mulki kasar Hadejiya ba, ance anyi sarakuna guda Talatin da biyu (32), kafin mulkin Fulani. Amma wadanda aka samu sahihin sunansu sune BAUDE, MUSA, DA ABUBAKAR.  Shi wannan Abubakar din shine wadda fulani suka karbi mulki a hannun sa. 

MADOGARA......
1. TARIHIN HADEJIA A TAKAICE. (ABDU MAIGARI. 
2. TURAWA A KASAR HADEJIA. (PROF. H. WAKILI). 
3. THREE NIGERIAN EMIRATE. (VICTOR N. LOW) 
4. MUHAMMADAN EMIRATE. (S. J. HOGBEN) 

HADEJIA A YAU....