HADEJIA A YAU! Wannan Dandali Na kirkireshi don bada Tarihin Kasar Hadejia, da Tarihin Sarakunan ta, da wadanda suka bada Gudunmawa wajen Inganta Al'adun Gargajiya. Hadejia A yau. Ismailasabo@gmail.com
Monday, April 30, 2012
KUKAN KURCIYA
Dandalin Muazu Hadejia
KUKAN KURCIYA.....
Da kun ban gari da nayi tsokaci akan wannan
hare haren boma bomai da ake kaiwa
Arewacin Nigeria. Wata rana ina dan primary,
malamin social studies yake bamu tarihin
Hitler Adolph na Jamus sai naji yana cewa
hitler in zaici gari da yaki da farko yana kai
hari ga jami'an tsaro sannan sai ya kai hari
cibiyar kasuwanci da gun ajiyar kudi. Bayan
nan sai ya kai hari ga matasa 'yan makaranta!
In yayi haka to ya karya tattalin Arzikin ku sai
kuma yayi muku duk abinda yaga dama. Abin
tambaya anan shine... Anya tarihi bai
maimaita kansa ba? Musamman a kasata
Nigeria? Yayinda shugaba yakeso ya tabbata a
mulki zai iya amfani da salon Hitler yaci gaba
da mulkinsa a tsunake. Yasan ba ta mulki
kuke ba ku dai ku samu zaman Lafiya. Jama'a
yakin ruwa fa ya tadda sakaina! Ya kamata
muyi karatun ta nutsu game da Hare haren
nan da ake kai mana da sunan wata kungiyar
da babu ita. Ka dauka cewa duk abinda ya
samu dan Borno ya sameka kai dan sokoto.
http://Isabohadejia.blogspot.com/ Muyi
kokari mu gyara kasarmu, muyi ta Addu'ah
Allah ya kauda mana Miyagun Shugabanni.
Kamar yanda Allah ya kawar da Hitler Adolph
na Jamus. http://
jindolada.xtgem.com/
Subscribe to:
Posts (Atom)