Hadejia A yau! Allahu Akbar!
ALH. ABDUL'AZIZ DANMASAGA :-
Hakika Tarihin Hadejia bazai manta da wannan bawan Allah ba, yayi iya kokarinsa wajen taimakon rayuwar mutanen kasar Hadejia, musamman Talakawa Masu karamin karfi da Miskinai.
Yayi Amfani da Arzikin da Allah ya bashi ya kyautatawa Jama-ar kasar Hadejia. Allah ya gafarta masa.
Alh. Abdu Danmasaga Mutum ne mai fara'a da son ci gaban Al'umma, baya so yaga mutane suna zaman banza. Hakan tasa yake daukan mutane ya sanyasu Inda zasu koyi sana'a domin su dogara da kansu. Shine mutuminda duk ranar Juma'a ko Lahdi yake raba kudi ga 'yan makarantar Boarding, saboda yasan basa kusa da Iyayensu.
Ga kadan daga Ayyukansa da yayi na Alheri.
(1) yana sayen itace mota mota ana faskarawa a tarashi kuma a saidashi lokacin da yayi wahala akan kudi kadan.
(2) Ba'a fara sayan Itace ba a Makabarta sai bayan mutuwarsa, saboda ya bada fisabilillah. Allah yasa yana Aljannah.
(3) yana saida kalanzir a kankanin farashi musamman lokacinda watan Azumi ya karato ko kuma lokacin Damina.
(4) yana saida fetur a farashi mai sauki yayinda ake wahalar sa. Ko ya zama babu a gari.
(5) shi yake sakawa ayiwa Mahaukata Aski, ya basu Abinci kuma ya dinka musu sabbin Riguna.
Dama ace masu kudi ko 'yan siyasa zasu koyi hali Irin nasa, da kasa ta kwana lafiya!
Allah ya Gafarta masa, Allah yasa mu koyi Hali Irin nasa.
Alh. Abdul'aziz Danmasaga.
Hadejia A yau.