;
*****Ciroman Hadejia Sambo da ne ga
Sarkin Hadejia Abdulkadir.Yana daga cikin
'yan boko na farko a Arewa kuma mutum na
farko da ya fara zuwa England a Masarautar Hadejia.Ya rike mukamin Dan Majalissar
tarayya a zamaninsa kuma shi ne Babban
Dan Majalissar Sarki (senior councillor) a wannan masarauta.Idan aka yi Tarihin ci
gaban kasar Hadejia ba a sanya Ciroma
Sambo ba tamkar an yi tuya ba a sa albasa
ba ne.
Ciroma Sambo dan ajinsu Sardauna
ne Sir Ahmadu Bello kuma amininsa ne don
haka Sardauna ya yi masa tayin mukamin minista amma ya ki saboda ya ce "idan na
bar Hadejia to ba za ta ci gaba ba"A takaice
dai ciroman Sambo shi ne kashin bayan ci gaban Hadejia, a zamaninsa ne aka yi
gagarumin fashin layi wanda ya zama
sanadin titunan da muke gani a cikin gari a
yau kuma zamaninsa ne aka fara ginin
rumfunan kasuwa na bulo.
Zamaninsa aka
fara gina asibiti aka ofisosin gudanarwa da
muke da su,a dai lokacin aka kawo wayar
tangaraho a Hadejia da Malam Madori kuma
Saboda hangen nesa da sanin muhinancin
ilmi ciroma ya tursasawa jama'a su sa
'ya'yansu makaranta wanda wannan ce ta sa wannan gari ya yi fice a fagen ilmi har a
yau.Wato ba za mu iya kididdigewa aiyukan
marigayi ciroma sambo ba saboda aiyukansa ya hade masarautar baki daya.
Ciroma
sambo shi ne ya koyawa Sarkin Kano Sunusi
Turanci saboda zamani. Allah ya albarkanci bayansa domin har yau Hadejia tana cin
gajiyar 'ya'yansa da jikokinsa.Marigayi
ciroma sambo masanin ilmin addini ne da na zamani, rumfa sha shirgi,mai hannun
kyauta,mai dimancaccen tunani, mai kishin
Hadejia na farko.An haifi marigayi a 1909 Ya rasu a 1958 wato yana da shekaru arba'in
da tara a duniya kenan. Allah ya sa jannatil
firdausi ce makomarsa.
Amin.
FARFESA MUHAMMAD IBRAHIM YAKASAI
*************** Farfesa Muhammad
Ibrahim Yakasai haifaffan kasar Garin Gabas ne ta karamar Hukumar Malam Madorin
Hadejia.Ya samu lakabin Yakasai saboda ya
yi karatunsa a gaban yayarsa da ke aure a
unguwar Yakasai ta kano. Muhammad
Ibrahim yana daya daga cikin manyan 'yan
boko na wannan Masarauta kuma shi ne Bafulatani na farko da ya samu darajar
farfesa a wannan masarauta.Yakasai ya fara
malamin makaranta a sakandiren wunti da
ke Hadejia na gajeren lokaci sannan ya samu koyarwa a Jami'ar Bayero da ke kano.
Allah
ya yi masa nasibi a harkar karatu domin ya
kammala karatuttukansa a cikin lokaci takaitacce. Yakasai yana cikin malamai dake
taimakawa 'yan wannan masarauta da ma jihar jigawa baki daya wajen samun shiga
jami'a.Baya da daukansu kuma yakan dauki
al'alar taimakawa wajen warware matsalar da duk wani dalibi ya shiga cikin jami'a.
Yakasai mutum ne mai fara'a,mai
saukin kai,mai sanin yakamata,Karatunsa
bai sa ya dauki duniya da zafi ba.Muna
masa addu'ar zama vice chancellor nan
gaba. Hadejia A yau...