"" /> HADEJIA A YAU!: DAGA NA GABA! HADEJIAWA...(part one 1)

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Wednesday, February 19, 2014

DAGA NA GABA! HADEJIAWA...(part one 1)


;
*****Ciroman Hadejia Sambo da ne ga Sarkin Hadejia Abdulkadir.Yana daga cikin 'yan boko na farko a Arewa kuma mutum na farko da ya fara zuwa England a Masarautar Hadejia.Ya rike mukamin Dan Majalissar tarayya a zamaninsa kuma shi ne Babban Dan Majalissar Sarki (senior councillor) a wannan masarauta.Idan aka yi Tarihin ci gaban kasar Hadejia ba a sanya Ciroma Sambo ba tamkar an yi tuya ba a sa albasa ba ne.


Ciroma Sambo dan ajinsu Sardauna ne Sir Ahmadu Bello kuma amininsa ne don haka Sardauna ya yi masa tayin mukamin minista amma ya ki saboda ya ce "idan na bar Hadejia to ba za ta ci gaba ba"A takaice dai ciroman Sambo shi ne kashin bayan ci gaban Hadejia, a zamaninsa ne aka yi gagarumin fashin layi wanda ya zama sanadin titunan da muke gani a cikin gari a yau kuma zamaninsa ne aka fara ginin rumfunan kasuwa na bulo.



Zamaninsa aka fara gina asibiti aka ofisosin gudanarwa da muke da su,a dai lokacin aka kawo wayar tangaraho a Hadejia da Malam Madori kuma Saboda hangen nesa da sanin muhinancin ilmi ciroma ya tursasawa jama'a su sa 'ya'yansu makaranta wanda wannan ce ta sa wannan gari ya yi fice a fagen ilmi har a yau.Wato ba za mu iya kididdigewa aiyukan marigayi ciroma sambo ba saboda aiyukansa ya hade masarautar baki daya.



Ciroma sambo shi ne ya koyawa Sarkin Kano Sunusi Turanci saboda zamani. Allah ya albarkanci bayansa domin har yau Hadejia tana cin gajiyar 'ya'yansa da jikokinsa.Marigayi ciroma sambo masanin ilmin addini ne da na zamani, rumfa sha shirgi,mai hannun kyauta,mai dimancaccen tunani, mai kishin Hadejia na farko.An haifi marigayi a 1909 Ya rasu a 1958 wato yana da shekaru arba'in da tara a duniya kenan. Allah ya sa jannatil firdausi ce makomarsa. Amin.

FARFESA MUHAMMAD IBRAHIM YAKASAI 
*************** Farfesa Muhammad Ibrahim Yakasai haifaffan kasar Garin Gabas ne ta karamar Hukumar Malam Madorin Hadejia.Ya samu lakabin Yakasai saboda ya yi karatunsa a gaban yayarsa da ke aure a 
unguwar Yakasai ta kano. Muhammad Ibrahim yana daya daga cikin manyan 'yan boko na wannan Masarauta kuma shi ne Bafulatani na farko da ya samu darajar farfesa a wannan masarauta.Yakasai ya fara malamin makaranta a sakandiren wunti da ke Hadejia na gajeren lokaci sannan ya samu koyarwa a Jami'ar Bayero da ke kano.



Allah ya yi masa nasibi a harkar karatu domin ya kammala karatuttukansa a cikin lokaci takaitacce. Yakasai yana cikin malamai dake taimakawa 'yan wannan masarauta da ma jihar jigawa baki daya wajen samun shiga jami'a.Baya da daukansu kuma yakan dauki al'alar taimakawa wajen warware matsalar da duk wani dalibi ya shiga cikin jami'a.

Yakasai mutum ne mai fara'a,mai saukin kai,mai sanin yakamata,Karatunsa bai sa ya dauki duniya da zafi ba.Muna masa addu'ar zama vice chancellor nan gaba. Hadejia A yau...

No comments:

Post a Comment

RUBUTA RA'AYINKA!